Nour Ayn Page 2 Complete by Zainab Amzah


 NOUR AYN

Hasken idaniyata 

BY ZAINAB AMZAH ✍️ 



Team WOW 5 WRITERS HUB.

No. 03


https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS?mode=gi_t


Comments section 

https://chat.whatsapp.com/CcpoemEqe2N84Ydb6uGPum?mode=gi_t



*To whomever comes across this book, please say a prayer for my mother who now rest in peace. May Allah forgive her shortcomings. Amin 🙏🏻*


*Page 2*



Koda suka isa hospital ɗin, ko neman Faruk Ammi bata tsayi yi ba, saboda yanayin jikin Mimi sai gaba yake yi. Ko kafin su ƙaraso sai da ta kara yin amai a mota. Ba tare da bata lokaci ba aka yi attending ɗinsu. Kasan cewar an sansu, don ko wane wata sai Mimi ta kwanta hospital ɗin. Sannan kuma Ammi mahaifiya ce ga Dr. Faruk, one of the best gynecologist they have at the hospital. Kuma nan ɗin wurin zuwa su ne. “A time ɗin Faruk na London yana masters ɗinsa. Kafin ya gama ya dawo Nigeria, ya fara aiki a ALYSHA Premier Hospital. Tun bayan dawowarsa sai suka rage zuwa hospital ɗin. Shine yake kula da duk wani harka da ya shafi lafiya a gidan da family ma gaba ɗaya. Idan ka gansu a hospital ɗin sai da babban dalili, ko kuma wani emergency kamar yanzu. Ko kuma idan shi yazo da su for some examinations. Yanzu ma don Ammi tayi kiransa bai ɗauka ba, ta san definitely akwai babban reason da yasa bai picking calls ɗin ba. Don Faruk never jokes with anything da ya shafe ta. Sannan kuma ƙari da ganin yanayin halin da Mimi ke ciki, shine dalilin da ya sa ta yi deciding su taho hospital ɗin su sameshi a nan. They admitted her after seeing the doctor. Because her body was too weak already. Drip aka saka mata tare da allurai da suka sa ta barcin wahala. Sai a lokacin Nadiya ta samu tayi sallar Zuhr da ba ta samu damar yi ba a gida, bayan ta dawo daga school. Sai a lokacin Ammi ta samu natsuwa har ta aiki Malam TK, yaje gida wurin maid ɗinsu ya amso masu abinci da duk wani abu da zasu buƙata. Sai gabannin Maghrib Mimi ta farka daga barci. Cikin saukin jiki ta tashi, unlike yadda suka shigo da ita da zun. Bayan tashinta daga barci, Nadiya ta kama ta ta kai ta toilet. Sai da ta wanke bakinta, ta gyara jikinta sannan suka fito. Suna fitowa, Ammi tace, Nadiya haɗa mata tea. Sai ki zuba mata abinci kaɗan ta ci. Idan ta gama sai ta sha magani. Dan marairecewa tayi tare da girgiza kai. A hankali tace “Ba zan iya cin abinci ba yanzu Ammi. Sai dai tea zan sha kaɗan. “Mimi, ki daure ko kaɗan ne ki ci kin ji?

Girgiza kai tayi cikin sanyi jiki, kamar za tayi kuka. Tace "No Ammi, please later. Murmushi tayi, tace wa Nadiya ta bata tea ɗin da ta haɗa mata. Amsa tayi tare da ɗan yamutsa fuska kaɗan. A hankali ta fara sipping tea ɗin. Ba ta wani jima da fara sha ba ta ce ta koshi. Sai da Ammi ta matsa mata, da ƙyar aka samu ta shanye tea ɗin gaba ɗaya. Bayan ta gama shan tea ɗin, magani Ammi ta ba ta sha. Tana gamawa ta sake kwanciya. Tun asali dama Mimi ba ta son cin abinci tun tana ƙarama. Tun abun yana damun Ammi har ya kai ta gane nature ɗinta ne hakan. Barin yanzu da ba ta da lafiya kuma.


Wani kyakkyawan matashin saurayi ne da ba zai wuce 32 years ba. Fari ne sosai amma ba fari irin na Larabawa ba. 

Irin mazan nan ne masu aje suma a kansu. Ga wani irin gyara da sumarsa ta sha. Da ka gani ka san ba kana-nun kuɗi ake kashe mata ba. Yana da jiki mai kyau sosai, irin na maza da suka amsa sunan su maza. Dan madaidaici ne dogo. Yana da yar kibar sa kaɗan da ta yi masa kyau ainun. A tsaye yake, daga samansa a buɗe yake irin na maza da suke daga ƙarfe. Ga wani dimple da ya ƙara ma fuskarsa kyau sosai. Yana da kyawun jikin da duk wanda ya kalleshi sai ya ƙara. Zaune yake a office ɗinsa bayan fitowarsa daga masallaci. Cike da gajiya yake zaune. Ya jingina kansa da kujera da yake zaune a kai, idanunsa a lumshe. Basu daɗe da fitowa daga theatre room ba, dan haka a gajiye yake sosai saboda last surgery ɗinsu da ya ɗauki lokaci sosai kafin suka gama. Sai da yaje masallaci yayi sallah sannan ya dawo office ɗinsa. iPhone 17 Pro Max ɗinsa ya jawo zai duba time. He saw a lot of missed calls from different people. Daga cikin su akwai na Fahad, da wani friend dinsa Mujahid da ya tafi garinsu anyi masa rasuwa. Sai kuma na Ammi da bata daɗe da sake kiran sa ba. Ganin tarin missed calls ɗin Ammi, sai hankalinsa ya ɗan tashi. Ya san definitely akwai problem. If not, Ammi da ya sani da tayi masa kira biyu ba zata sake ba muddin yana hospital, duba da yanayin aikinsa. Dialing number ta ya fara yi. Yana kira ta ɗauka. Bayan sun gaisa yace sorry Ammy yanzu na fito theatre. Na ga missed calls dinki. Hope you're ok? Ok. Which room? Ya tambaye ta bayan ta sanar dashi suna hospital. Tana faɗa masa yace “Just a minute. I'm coming now. Tattara phones ɗinsa ya shiga yi, da duk wani important abubuwan sa da zai buƙata. Ya yi switching komai na office ɗin, sannan ya ɗauki car key dinsa. Kai tsaye ya nufi ward ɗin da suke, cike da mamakin waye kuma ba shi da lafiya? Don shi dai ya san lafiya lau ya bar kowa a gida. Da sallama ya shiga ɗakin. Nadiya da ke zaune kusa da Mimi tana chatting, tayi saurin gyara zamanta. At the same time ta aje wayarta gefe, jin sallamar sa cikin muryarsa mai daɗin sauraro. Dan kallon sa tayi tace Yaya, Ina wuni? Cikin natsuwa ya amsa mata sannan ya ƙara gaida Ammi. Ganin Nadiya da Ammi dake zaune, yasa ya gane wacce ba tada lafiya, da dalilin zuwa su hospital ɗin. Gadon ya zuba ma ido, tare da Jan ƙaramin tsoki da ba lallai ma ka ji ba. After some seconds ya nufi gadon kai tsaye, cikin takunsa mai ban sha'awa. Saurin rufe idon ta tayi da taji alamun yana tahowa, pretending as if she's sleeping. Kallonta yayi, sai kuma ya kalli Nadiya yace Me ke damunta? Duk da ya san dai ba zai wuce dysmenorrhea ba, amma still ya tambaya. Cikinta ke ciwo Ammi ta ba shi amsa. "Ok, Allah ya bata lafiya. Suka ce Amin. Kallonta ya sake yi, ya ga idanuwanta a lumshe, but still sun kumbura, alamun ta sha kuka ba kaɗan ba. Tabe baki yayi, yace "Lazy girl." Duk da kasa-kasa ya faɗa, amma sarai ta ji shi. A ran sa yace shi bai san wace irin ragguwa yarinya ce wannan ba, da ba za ta iya daure wa ciwo komin ƙanantarsa ba. Ga kukan banza da ba ta gajiya da shi. Just period cramps, ba zata iya enduring ba, tayi ta damun mutane da kukan banza. Ashe duk ranar da zata haihu ba karamin wahala za’a sha ba. Don ya san sai kowa sai yaji a jikin sa, daga ita har doctors ɗin. Lallai akwai aiki. Disconnecting drip ɗin yayi, yace Ammi, we can go now. No need to stay here. I'll take care of her at home. “Ku shirya kafin na dawo. Bai jira cewar Ammi ba, ya fice daga ɗakin.




Ina mai farin cikin sanar daku muna siyar da Kaya Kala Kala masu kyau da quality direct from Egypt Abaya, jalbabs,  boubou, scarfs, jersey hijabs, jersey veils, comfy gowns,tie back caps,crinkle turban caps,nightwear’s,and lots more,,


Muna yin adashe na kome kake so  ga wanda bashida halin siya lokaci daya..Masu son fara business su ma muna maraba dasu. For more info +201508856397

WhatsApp only.


+201508856397 

My WhatsApp number 

Tiktok @amzaah

Instagram @zainabuh_Amzah

Snapchat @Zainabuh20

Wattpad @zainabuh Amzah

Arewapen @zainab Amzah


*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*



*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*



1- Ummulkhairi Sani Panisau  (Khairatup)

GABA TAZO BAYA


2-Harira Salihu Isah 

 Uwar Batoorl 

YARIMA BAHJAT


3-Zainab  yahaya Amzah 

NOUR AYN


4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)

KUSKURENA NE


5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) 

WAHEEDA



Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.


Guda ɗaya  1k

Biyu  1500

Uku  2k

Huɗu  2500

Biyar 3k



Account Number  9126022777

Bank: Opay

Suna: Ummulkhair Sani Panisauu


Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇


09023907030


09161720046


+20 150 885 6397


09065856251


07061707238


*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post