Joda Page 5 Complete by Sadi-Sakhna

 ____👑 *JODA* 👑_____

Na 

*Sadi-sakhna*

Ƴar mutan Jama'are

THE TRIO OF TALES 

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 

@sadisakhna on Arewapen

@SAKHNA03 On Wattpad

09035784150 on Whatsapp

LITTAFI NA 1

*Harƙa ta (5)*👑

Ɗaga mata kai tashiga yi kamar kaɗangare tana ƙara sautin kukanta mai haɗe da dariya.

"Nice Joda nice Ummah ce,sannu kinji sannu.....nayi zaton na rasaki Joda......"

Sambatun da takene yajawo hankalin baba yakub yayi magana daga waje domin yaji mai yake faruwa,a zatonsa ko ciwon kamaluddeen ne yayi tsamari.

"Baba Yakub joda ce ta tashi,Joda ta tashi shigo ka gani harta ƙira sunana"

Ƙarisawa yayi ciki jin tayi masa ido,a kwance yaga yarinyar akan cinyarta ta rirriƙeta tamkar zata maidata ciki,ita kuma kallo kawai take bin Aminatoun dashi.

"Yarinya sannu kin farfaɗo ya jikin?"

Tsayawa Aminatou tayi da jijjiga ta domin bata damar amsawa baba yakub ɗin. Itama Joda a nata bangaren jin muryar mutum yasa ta juya inda yake tana ƙare masa kallo cikin nutsuwa kamar ba yarinya,batace komai ba ta ɗauke kanta tareda Nuna gogar Duma na ruwa dayake gefen Aminatou.

Ta gane mai take nufi dan haka da sauri ta miƙo mata ruwan tareda ɗan tayar da ita kaɗan ta fara sha.

Ƙwat ƙwat kwat saida ta shanyeshi tass kafin tasaki gorar,ajiyar zuciya tasake tareda sakin jikinta ta koma ta kwanta,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya fizgeta normal bawai na suma ba.

Ita dai ta baba Yakub ido kawai suka zuba mata har zuwa lokacin data sulale ta kwanta,Aminatou cema ta miƙa hannu da sauri zata ɗagata amma yayi saurin dakatar da ita.

"Ahah ki barta kada ki tasheta,ba doguwar suma ta koma ba wannan bacci ne. Har yanzu jikinta bai gama Farkawa ba,dan haka dole saita samu hutu sosai kafin komai ya daidaita. Na samo wani maganin bari zan saka masa kafin daga bisani da Asuba mu ɗau hanyar Daular Songhay in Allah ya yarda"

"To bakomai,nagode fah yanda kake ɗawainiya damu Allah yabaka kaima mai maka nagode sosai gashi mu ba ƴaya face bayi"

"Karki damu musulmi ai ɗan uwan musulmi ne,duniyar tamuce ta sauya,har ana ganin bawa kaman ba mutum ɗaya bane da masu ƴan ci." 

Koda ya isa inda kamaluddeen yake kwance,ɗaurin da yayi masa a wajen ciwon yafara kwancewa,ƙofar da kibiyar ta huda yayi baƙiƙƙirin ya kumbura,jijjiga kai yayi cikin halin tausayawa domin da ganin ciwoan kasan duk wanda yake a jikinsa to yanashan wuya.

Saida ya goge ruwan daya fito kafin ya ɗauko wani Dakyakykyen maganin dayazo dashi ya manna masa a wajen,wata ƙara ya saki yana numfarfashi,amma bai daina danna maganin ba har saida ya tabbatar ya ratsa ciwon kana ya maida wani sabon tsumman ya ɗaure. 

Duk abinda suke Aminatou tana kallonsu amma ta gagara ƙarisawa wajen,domin bazata iya gani ba,hawaye kawai take gogewa daga nesa.

Har baba yakub yazo zai fita sai kuma yace mata.

"Kishirya muku kayanku dare yana rabawa biyu zamu fara tafiya,yakamata mu hanzarta,jinkirin mu zai iya sakawa dafin ya ratsa zuciyarsa,wannan makari ne nasaka masa ba lallai yaɗau dogon lokaci yana bashi kariya ba."

Amsa masa tayi da to,da sauri kafin ta miƙe tafara haɗamusu kayansu. 

Har suka fito zuwa cikin jirgin ruwan Joda bata tashi ba,sai Aminatou ce ta ɗauketa,shikuma yusha'u suka riƙo kamaluddeen shida baba yakub.




Saida suka tabbatar sun gama ɗaukar kayansu tass kafin suka since igiyar data riƙe jirgin a bakin ga'ba,kana suka nausa Arewa izuwa ga masarautar Songhay




Sannu a hankali jirgin yafara tafiya a saman ruwan,saida suka ɗanyi tafiya mai nisa sun daina ganin tsibirin da suka biyo kafin yafara ƙara gudu.




Matsakaicin jirgi ne mai ɗaki ɗaya a tsakiya wanda zai ɗauki mutum huɗu,sai kuma gefe da gefe inda mutane zasu zauna suyi fito idan igiyar ruwa tayi ƙarfi.




Joda da kamaluddeen ne a cikin ɗakin,Aminatou tana tsaye a waje,yayinda su baba yakub ke ƙoƙarin wajen ganin sun saka hancin jirgin a hanya.




**Joda**




Bude idona nayi,wannan karon banga rufin zana ba saidai na katako,kenan ba a inda nake ɗazu ba nake a yanzu? Nayiwa kaina wannan tambayar. Tashi nayi zaune ina rarraba ido,jikina yamin nauyi dakyar yake bani haɗin kai wajen motsashi.waigawa gefena nayi na hango mutum a kwance a irin gadon katakon danake kai,kunnuwana suna jiyomin ƙarar iska tana ƙugi irin wacce ake samu a kogi. Tashi nayi a hankali na nufi mutumin dayake kwancen Abah nane nagani,gefen kafaɗarsa a ɗaure,mai ya sameshi haka? Bana tuno komai na rayuwata ta baya,fuska biyunnan kawai na tuna,Ummah da Abah. Wata ƙofa nagani hakan yasa naje nabuɗe,da tunanin kozai kaini waje inda wasu suke,domin idan kunne na ba ƙarya yakemin ba ina jiyo alamar motsin mutane a wajen.




Da farin sararin samaniya nayi arba,fararen tsuntsaye manya suna shawagi a cikinsa,gabana na kalla wanda bana ganin komai face zallan samaniyar wanda tayi kaman ta saƙƙo ƙasa ta haɗu da ruwa.




Toh mai muke a cikin kogi kuma,ban tuna inda muka fito ba,amma dai inaji a jikina cewar nayi wata rayuwar dole wacce ban tuna ba,tunda gani a tsaye kam ai dole saida nayi rayuwa kafin na iso yanda nake.




Lissafi ƙwaƙwalwata naji tana yi na yanayin sararin samaniyar,son gano wacce kusurwa iska take bi,sannan su kansu tsuntsayen dake shawagi wacce irin rayuwa suke gudanarwa,dannan wacce alƙibla jirgin da muke ciki yakebi. Shin wannan wanne irin kwaɗayine na neman ilimi danaji zuciyata da ƙwaƙwalwata sun haɗu suna yi?




"Joda Mashaallah Joda kin tashi"




Inda naji sautin sunana yana tashi na kallah,Ummah ce garinya ban kulada ita ba tunda na fito daga cikin ɗakin. Hankalina gabaɗaya ya tafi ga son sanin abinda yake zagaye dani.




Kallon hannayen ta nayi wanda tarike nawa gamm a cikinsu kaman wanda idan tabuɗe ido bazata sake gani na ba na bace.




Daga yanayin kallonta alamar akwai abinda yafaru kenan,inaso na tambayeta ko kuma nayi magana,amma sam nagagara cewa komai,badan ban iya maganar ba sai domin yadda fatar bakina tayimin nauyi,kenan na ɗau wani lokaci a kwance.




"Baba yakub zoka dubata dan Allah kaddai bayan tabin ƙwaƙwalwa kwanciyar da tayi yasakata daina magana....."




Cikin murya mai rauni tayi maganar....tabin ƙwaƙwalwa ohh dama banida hankali,ko shiyasa waɗannan lissafen suke shigowa cikin kaina kai. Wani dattijo ne ya nufo mu,wanda buɗe idona na farko na ganshi,ban taba ganinsa ba sai yanzu mai ya haɗasu dasu ummah,ko ban tuna ba amma wani yanki na cikin kaina yana gwadamin ba'a nan muke rayuwa ba da,domin wannan ne karo na farko danaga wajennan.




Ƙarisowa yayi inda muke ya zubamin ido,ganin kallon har hanji yakeyimin yasa na ɗauke kaina ina kallon wani waje daban,bayan kaman wani lokaci ya sauƙe ajiyar zuciya kafin yace.




"Abin akwai ɗaure kai,kada kiyi mamakin jawabina amma da alamun komai yasameta a jejinnan ya kwantar da ita doguwar suma to kuwa yayi mata maganin gefen ƙwaƙwalwarta daya shanye,domin idanuwanta basa ɗauke da wani abu waishi wauta,da alama hasashena ya zama gaskiya,doguwar suman data shiga ƙwaƙwalwarta ce take jinyar warkewa daga shanyewar da tayi. Amma kada mu yanke hukunci da wuri mu bari lokaci ya nuna mana dakansa."




Duk wannan bayanin dayakeyi babu wanda bangane ba,amma kuma daga kallon fuskar umma alamun bata ganeba ko kuma mamakin hakan yahana ta gasgata bayaninnasa.




Wani ƙugi cikina yakeyi,jiri yafara ɗibata kaman zan faɗi,saurin kama hannun umma nayi ina riƙe kaina. Ganin haka yasa wani matashi a gefe shiga cikin ɗakin dana fito ya ɗauko irin gorar ruwan da suka bani a tashina na farko,sannan da wani abu a nannaɗe cikin ganye. Buɗewa nayi ina kallon abun,nakiyace da akayi ta da soyayyan gari da ruwan rake,sai kamshi take tun kafin nakai bakina.




Gutsira nafarayi da sauri sauri kaman wani zai ƙwace har na cinye dukka,sannan na bita da ruwan da umma ta miƙomin.




Sai a lokacin nafara ganinsu garau,ashe tun da yunwa ce tahanani gani da kyau,ko kuma ba komai nake gani ba sai yanzu,domin ji nayi kaman an yayemin wani baƙin mayafi daga idona. Kuma bakina yayi fayau zan iya buɗeshi ba kaman ɗazu ba.




"Umma ina ne nan,mai yasamu Abah na naganshi a kwance kaman baya motsi,ɗazu naji kuna maganar nayi doguwar suma,shin mai ya sameni nafaɗa doguwar suma. Wacece ni dana kasa tuna komai a rayuwata ta baya,iya fuskarku kaɗai nake tunawa banda haka bana tuna komai sai tashina ɗazu da kuma tashina a yanzu"




Sakin baki ummah tayi saƙale tana kallona,saikuma taja da baya kaɗan da alamar razani a fuskarta. Kaman taga wata sabuwar halitta. Ganin hakan bazai kaita ba bubbuga fuskarta tayi sanann ta murza idonta.




"Wai ba mafarki nake bane,Joda meyasami maganarki da yanayinki,badan da kamanninki akan fuskarki ba,da kuma mu mukayi ta dakonki a gadon bayanmu da zance na ajiyeki a wani wajen na ɗauko wata daban. Ikon Allah tsarki ya tabbata ga ubangiji. Baba yakub tabbas maganarka gaskiya ce, yanayinta da kuma maganar ta gabaɗaya ya sauya daga yanda take baya, wannan Jodar tawa mai lafiyace,wacce baza'a zagemin ita ba,wacce baza'a cutarmin da ita ba,kullum addu'ata tazamo ƴa kamar kowacce,mai hankali,tunani dakuma basira,ba wawiya mai tabin hankali ba,wacce takasance abar cutarwa ga kowa ba. Allah ya karbamin addu'a ta,wacce tafidda tsammani da zan sameta saidai idan Allah ya ajiyemin ita sai gobe kiyama,sai gashi ashe ya amsa yah Allah,yah Allah yah Allah...."




Rushewa tayi da kuka tareda zubewa a wajen tayi sujjada tana cigaba da kukan fuskarta na kan goshinta.




Jikina ne dukka yayi sanyi,shin mai ya farune,wacce irin rayuwa iyayena suka fuskanta haka, meyasa na gagara tuna komai a ciki?  Tsugunnawa nayi tareda dafa ta a bayanta,ɗagowa tayi jin hannuna ta rungumeni tsam a jikinta,har sannan bata daina sheshshekar kuka ba. 




Baba yakub ne yayi gyaran murya tareda cewa.




"Kamata ki kaita ɗaki,idan ta nutsu hankalinta ya kwanta zata baki dukkan wani labari dakikeson ji. Ki shiga da ruwan dayake gefenki wataƙila zata buƙaceshi,sannan kibita a hankali domin taga rayuwa sosai"




Ɗaga masa kai nayi alamar na fahimta kafin na rike hannunta muka shiga ɗakin.





Bayan tagama bani labarin zuyawa nayi na kalli inda mahaifina yake kwance,hawayen dayake ta zurara tun ɗazu da aka fara labarin ban share ba,su na samu damar saka hannu na sharesu yanzun. Muryarta na tsinkayo ta cigaba da magana.




"To kinji abubuwan dasuka faru,karkiji babu daɗi domin baki tuna ba,dama ba abun daɗi bane dazaki tunashi,duk da cewa yana daga cikin wani tsagi na jarrabawar rayuwarki. Bansan wacce irin godiya zanyiwa ubangiji ba danayi arba dake kin warke kina cikin hankalin ki kaman sauran kowanne ɗan adam mai lafiya. Yanzu burina bai wuce Abanki ya tashi ba na sanar dashi wannan daddaɗan labari,nasan zaifi kowa farin ciki da jinsa"




Har taƙare bayanin nata ban kalleta ba idanuwana suna kan Jarumin mahaifinnawa,wanda nakeji a raina babu tamkarsa,lallai nayi sa'ar iyaye wanda suka zabi kare rayuwata ta hanyar saka su tasu rayuwar a haɗari. Ni banida wani buri daya wuce naga ya tashi yana rayuwa cikin farin ciki da ƙoshin lafiya. Sannan kuma nasakashi yin alfahari dani wanda bayyi ba a baya.




Dare na uku yashiga mana a babban kogin muna tafiya,duniyar tayi tsit babu wannan ƙarar tsuntsayen dasuke shawagi akan mu kullum daga gari ya waye. Sai taurari wanda kowacce ke takara wajen ganin ta ƙyalla nata hasken a duhun samaniyar.




Nafi minti goma ina kallonsu,wanda wannan shine nima kwanana na uku ina zuba musu ido. A gefen mu kuma yusha'u ne da Ummah suke fifita Kurfoti zasu dafa mana shayi. Wanda a yanda na kula alamun sun ɗan samu jituwa da ummantawa. A bangare ɗaya yana mata kallon tamkar babbar yayarsa,itama kuma kallon ƙani takeyi masa,wani zubin kuma idan an kalla tamkar ɗa.




Tunda na tashi daga suman danaji ana cewa nayin na samu kaina da sabon halin da banida shi a baya. Hankalina yafi karkata da abubuwan da suke kewaye dani fiyeda shiga shirgin mutune ko yaushe,indai ba abu yazama dole na shiga ba to nakan koma gefene nayi nazarin wani abun daban. Ji nake kaman rayuwar cikin jirgin tayi min kaɗan,ƙwaƙwalwata ji nake kaman tanaso ta fice daga cikin keji ta shiga duniya nemo wani abun da bansanshi ba.  Hakanne yasa naga kaman mutanen jirgin sunayimin kallon miskila,ko kuma a kalam mafi daidaito ace marar magana.




Hankalina ha 'ilau tafiya yayi kan baba yakub wanda yasaka hannunsa guda biyu sama suka bada ƙofa a tsakiya,saita wata tauraruwa yayi dake arewancin duniya ta yanda zata shiga tsakiyar ƙofar daya bayar a . Karkata hannunasa yayi a hankali zuwa Gabas maso arewan,kaman na wasu daƙiƙu sai ya ajiye hannunsa yana wani nazari da hannunsa.




Karisawa nayi gefensa a hankali nayi magana,wanda saida ya ɗan zabura,domin tunda nake bantaba tunkarar sa nayi masa magana ba. Saidai idan ya tambaye ni na bashi amsa,ko kuma in yayi magana na ɗaga kai alamar naji.




"Baba yakub shin menene matsayin wannan tauraron dayake arewancin sararin samaniya,baya motsawa sosai har gari ya waye,ba ya karkata yamma ko gabas saidai ya ɗanyi ƙasa kaɗan, ko yayi sama. Sannan wasu taurari ma wanda suke a sunkushe waje guda,a duk lokacin dazaka karkata jirgi,ko kuma an daɗe ba'a tuƙashi ba sai ka saka hannunka inda suke na wani lokaci daga bisani saika gyara jirgin. Yawwa akwai wani ma wancan mai haske sosai,daga haskensa ya dusashe Ko ya bace saika tashemu nida umma muyi sallahr asuba. Akwai abubuwa da dama dakakeyi harma auna lokaci da tafiyar rana da kakeyi da inuwar tsinke......shin zaka sanar dani wanne ilimine wannan sannan kuma mai kake karanta a tareda su kuma taya kake ganewa?"




Ba iya baba yakub kaɗai ba,harma dasu Aminatou dake gefe dasu kaɗan suka tsaya suna saurarena dasuka ji ina magana saida suka sake baki da ido suna kallona. Shuru nayi na sunkuyar da ido,duk sai naji na tsargu da kallon dasukemin. Ko saboda da bahaka nake bane shiyasa sukemin wannan kallon mamakin.




Amma zancen ba haka bane,hatta yusha'u da tun yana ƙarami baba yakub yake tafiya dashi acikin teku bai taba lura da yanayin taurari ko kuma yanda ake amfani dasu ba. Sai ita wacce gabaɗaya kwananta uku a cikin jirgin,har ta kulada waɗannan tarin ilimummuka haka.




Ganin wajen yayi shuru kowa yana kallona yasa baba Yakub barin wajen zuwa can inda hancin jirgin ruwan yake ya zauna. Juyowa yayi yakalleni tareda nunamin gefensa nazo na zauna. Banyi musu ba naje na zauna inda yace ɗin.




Kallona yayi na wasu sakwanni kafin yamaida kallonsa izuwa sararin samaniyar.




"A gabaɗaya tsawon rayuwata nayita ne akan ruwa fiyeda doron ƙasa,nayi tafiya da mutane da dama acikin ruwa bayan mahaifina ya turani neman ilimin gane hanyoyin garuruwa ta hanyar amfani da taurari. Hakanne yasa na tafi ƙasar Fararen fata wanda sukeda ruwa manya manya na koyo ilimin gane hanya akan ruwa. Wannan ilimi dana samo ya siyamin daraja sosai,ciki kuwa harda nemana da akayi tayi akan nazama matuƙin manyan jirage na ƙasar Songhay. Amma firr sainaƙi amincewa,domin ni babu abinda nake sha'awa kuma nake mafarki kamar rayuwar ƴanci, sunyi ta bibiyar ɗan uwana ganin yakasa shawo kaina yasa suka haƙura. Nasan zakiyimin tambayar meyasa naƙi amincewa da wannan babbar dama?"




Hakan kuwa ne a cikin raina,sai ya tari numfashina yayimin tambayar shi da kansa.




"Mutanen gidan sarauta masu ƙarfin mulki da iko sunada wani hali guda ɗaya. A duk lokacin dasuka kalli wata baiwa a gareka wadda zatayi musu amfani,to zasu bibiyeka suyita ƙwadaita maka dukiya da matsayi domin su jaka zuwa jikinsu,daga lokacin da suka kalli bakada wata damar sai tasu,ko kuma abinda suke nema a wajenka babu shi,to zasu ƙasƙantar dakai su koreka,wanda hakan zaisa zuciyarka ta karye ka kasa amfanar da kanka da komai harka koma ga mahaccinka. Hakan shine yafaru da mahaifinmu a dalilin fikirarsa da ilimin sanin magunguna. Labarin da tsayi bazan iya sanar dake a yanxu ba. Shiyasa nazabi nayi rayuwata ni kaɗai,nayi amfani da fikirata na nemi abinda zan ciyarda iyalina. Banason cutar da kowa saannan nima banason wani ya cutar dani ko ya dunga juyani a ƙarƙashinsa.




Wannan labarin na zabi bakishine saboda jikina yabani rayuwarki bazata tsaya a iya waje ɗaya ba Joda,saboda duk wanda Allah ya bashi kaifin hankali irinnaki to lallai zai jarrabeshi da abubuwa kala kala. Dan haka ki kulada duk abinda zakiyi,karki bawa mutane komai naki batareda kinsan waye su ba. Mutum yanada kaifi sosai dayafi tsinin takobi,kada ki zauna akai batareda kinsan dabarun yanda zakiyi bazai sokeki ba. Sannan idan kinada goma ki boye biyar ki nuna biyar. Wannan biyar ɗin da kika boye zata iya yimiki amfani da lokacin da shi mai goman bashida ko sisi. Nasan kin fahimci maganganuna,koda baki fahimta a yanzu ba ki haddacesu zaki fahimta a gaba "



Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....


JODA by sadisakhna 

DAAƊIN ZAMA by Seemah 

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by gureenjoh 



*A whatsapp 

One 1k

Two 1800

Three 2400* 


 *Telegram 

One 700

Two 1200

Three 1500*


Account details 

0545475847 

Gt bank 

Fatima Muhammad Gurin 


Sai a tura shaidar biya ta

09035784150

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post