Joda Page 3 Complete by Sadi-Sakhna

 

👑 JODA👑

Na  Sadi-sakhna 

Ƴar mutan Jama'are 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

*Harƙa ta (3)*👑 

"To amma idan mukayi nasara fa,zamu tseratar da rayuwar ƴar mu,idan da kwananta a gaba zata tashi fah,sai muka bari aka binneta a gobe,baka tunanin zamu rayune tamkar ranmu ya zare daga jikinmu. " 

Shuru yayi yana nazarin maganarta,idan har mace mai tsoro kamarta zata iya yanke irin wanann hukuncin to inaga shikuma.... Kuma gaskiyar ta tunda sun gagara samun mafita wannan ce kaɗai mafitar duk da tanada matuƙar haɗari. Kuma yasan babu kyau,to amma yazayyi kare iyalansa shine nauyi na farko daya ɗoru akansa. 

Ɗaga mata kai yayi alamar ya gamsu da maganar tata,duk da ƙwaƙwalwarsa  alamun bata gama yarda da hukuncin da zuciyarsa takeson yankewa ba. 

"Yanzu to ta wacce hanya zamu bi kenan,abinda akwai kasada sosai,banason saka rayuwarku a haɗari" 

Da mamaki ta kalleshi,ya yarda kenan. 

"Muje aban Joda ko inane,indai har ƴata zata rayu a wajen batareda an farmaketa ba a shirye nake danaje wajen ,kuma na shirya jure duk wani kalubale na hanyar tafiya zuwa wajen. Ban kawo haka a rainaba amma banajin zuciyata zata iya ganin binneta a gobe,idan naji tsoron tafiya dan kada akamani ma to banida tabbacin rayuwa a goben bayan an zartar da wannan zalincin a gareta" 

Yanda take maganar kaman tazare sai hakan yaƙarawa kamaluddeen jin tsananin tausayinta, ji yake inama yanada iko,inama shi ɗane da zai iya tsayawa iyalansa,ba matsoraci ba kuma rago wanda guduwace mafita a gareshi.  

****     **** 

Ƙafarta ta ɗora akan cinyar matar tana gyara mata,can kaman wani lokaci yarinyar da bazata wuce shekaru goma ba ta zare hannunta ta zabgawa matar mari wacce zatayi shekara hamsin koma fi a duniya. 

Rike wajen marin tayi,duk da ba yaune ita ko wani daga cikin bayin yake samun wulakanci daga wajen ƙaramar gimbiyar ba amma wannan ne karo na farko dataji mari ya sauƙa kan kumatunta daga wajenta. 

"Ke wacce irin marar hankalice Jahila,cewa nace fah ki sakamin jan fenti shine zaki sakamin baƙi,mayya kika maidani komai,to kisaka harshenki ki lashe yanzunnan" 

Kallon farcen yarinyar takeyi wanda tashafa mata baƙin fenti da aka haɗashi daga wani sashe na jikin bishiya bayan an ƙona shi. Abune mai tsada daba kowo ke iya siyansa ba sai ƴan wane da wane,domin daga Masar ake kawoshi.  

Karkarwa jikinta yafara ganin tozarcin da jikar cikinnata takeyimata a kawai domin tana baiwarta. Bakinta tasaka tana lashe abin ɗaya bayan ɗaya saida tayi farce huɗu ta fixge ƙafarta cikin tsiwa. 

"Tsaya tsaya haka ni karki shafamin cuta da wari,jeki ɗauko ruwa ki zuba miski ki wankemin" 

Tashi matar tayi da rawar jiki ta wuce wasu bayi guda biyar da suke tsaye kowa da abinda yake hannunta na biyan buƙatun Gimbiya Meerah wacce itace ƴa mace tak a wajen Sunkia Maryama matar Sarki Abdujalal Sunni Ali na Daular Songhay ta biyu. 

Kasancewar anyi maza uku aka sameta sai hakan yabata damar cin karenta babu babbaka,kuma an raineta da raina kowa ta taka kowa,domin itadin takai tama wuce tsaranta sai na gaban gaba. 

Ko daƙiƙa uku bata cikaba sai gata ta dawo da kwarya mai dauke da ruwa a cikin yana zuba ƙamshi. Kama kafar Gimbiya Meerah tayi kaman ta riƙe kwai karta sake yafaɗi haka tafara wanke mata kafar tana gogewa da wani farin ƙyalle. Ita kuwa sai kallonta take tana yatsina karamar fuska. 

"Nuratu....ko batanan" 

"Gani ranki ya daɗe" 

Da sauri wata yarinya da kaɗan zatafi Gimbiya Meerah don bata wuce shekara shabiyu ba. 

"Haɗamin ruwan wanka,sauran kuma kiyimin shirme irin na wancan lokacin,na kula ku ƴaƴan bayinnan kunnenku a toshe yake,kuna daɗewa baku iya abuba,wanann karon idan bakiyi daidai ba sai na saka anyi miki bulala ashirin ba goma ba. 

Girgiza jikin Nuratun yayi jin hukuncin da Gimbiya Meerah ta ambata zata saka ayi mata. Kallon kakarta Inna Mairo wacce take wankewa Gimbiya Meerah ƙafa,ita tun tashinta bata san kowa ba sai Kakartata, Ubangidan mahaifiyarta ne yayi mata fyaɗe wanda ƙarshe ta mutu a haihuwarta,ganin babu abinda zayyi da jinjirar yasa ya mikata ga Inna mairo ta raineta, sannan yakarbi kuɗinta a wajen Sunkia Haleema tunda itace uwargijiyar Inna mairon. Sai hakan yasa ta zama baiwa mafi ƙanƙanta a sashen. Tanada shekara biyu aka haifi Gimbiya Meerah tare suke wasa ta ɗauketa kamar yayarta,amma tunda tafara girma tagane matsayinsu ba ɗaya ba,kuma komai ita idan tayi ba'a yimata faɗa saidai a sauƙe akan Nuratu ce tayi,sai hakan yasa halayyar ta suka fara sauyawa. Kuma bugu da ƙari yayunta ma suna riritata,komai take buƙata shi suke mata. Sannan Sunkia Haleema itama tafito ne daga masarautar Mali,daular kuɗi da iko. itace Ta biyu bayan Sunkia Madina Yaƴanta Biyu ne a Duniya,Gimbiya Hareesah wacce itace gimbiyar da ake ji da ita a kaf faɗin daular,saboda tanada kyau izza dakuma ɗumbin baiwa ta ilimi,yanzu haka tana Birnin Jodan acan take karatu na Madarar mulki da tafiyar da sha'anin sa,makami ce ita mai zaman kanta da ake kaifata domin nemowa dukkan masarautar suna ,duk wani buri akanta uwarta ta ɗora,kasancewar ita aminiyar Musso Aimaanah ce,kuma tayi mata alƙawrin itace zata zama Sarauniyar gobe ta mali,Gimbiya meerah kuma so ake a haɗata da Kaita Hamad ɗan Musso maleekan. sai kuma Gimbiya Meerah. tanason ƴaƴanta,kullum burinta su zamo sune a sama su taka kowa yanda suke so. Wannan yataka muhimmiyar rawa wajen sauya halayyar Meerah gabaɗaya. 

Duk lokacin da su Nuratu suka baro sashensu na bayi suka zo aiki zuciyar ta take cunkeshewa,babu wani da take gani mai muhimmanci a rayuwarta kaman Inna mairo. Abin yanayi mata ciwo idan taga Meerah tana cimata mutunci amma babu wanda zai nuna bacin ransa ma akai ballantana ya hana. Mutum goma ne a sashen Meerah,Inna mairo ce Babba kuma kusan ita tayi rainonta. Sai masu matsakaicin shekaru guda Takwas sai kuma Nuratu itace ƙarama kuma Jikar Inna mairo. 

Yau tayi nasara ta haɗa ruwan yanda Meerah takeso,Mata hudu ne suka tattaro kayan wankanta suka shiga banɗaki,ita kuma Nuratu tabi inna Mairo zasuje suci abincin rana kafin su dawo,yamma har tayi da kyar take tafiya saboda yanda cikinta ya fafe. 

Babbar masarauta ce mai matuƙar girma kamar gari guda,ita kanta Nuratu tunda suke bata taba fita waje ba,rayuwarta gabaɗaya ta ƙare a cikin masarautar, Domin a bayi sai matsayinka yakai kafin za'a baka damar fita,wanda yawanci ma maza ne suke fitan. 

Kamo hanya sukayi zasuje inda ake raba abinci,jikinsu a sanyaye suke tafiyar,sun san zuwa yanzu kam an gama rabawa bazasu samu ba. Meerah ta hanasu tafiya firr,kuma ta sani sarai samun abincinsu na lokaci ne. 

"Inna shin wacce irin rayuwa ce taketake wakana a waje,shin irin tamu ce ko kuma ita dabance da wannan?" 

"Ehh to bazan ce miki ga wacce tafi ba,ko a wajen ma idan ke baiwa ce to duk ɗayane,saboda ɗabi'a ce ta ɗan adam idan yanada dama ya dama. Wani lokacin har gwara nan zaki samu wani mai kyau kici daga inda kike aiki idan ya rage,amma a waje sabanin hakane saboda shi kansa mai gidanki ba lallai ya ƙosheshi sosai ba ballantana ya baki" 

"Inna shin iya abincine abinda idan bawa yasamu shikenan an gama masa komai,ina kimarsa da darajar sa a matsayin sa na shima ɗan adam ne?, ni kaɗai nasan yanda nakeji a raina idan Gimbiya meerah tanayi miki walaƙanci,koba komai ai kin fita" 

Tsayawa da tafiya inna mairo tayi cakk kafin tajuyo ta kalli Nuratu da fuska mai ɗauke da rashin alamar wasa. 

"Nakula ke har yanzu yarinya ce baki gama sanin a wacce duniya kike rayuwa ba ballantana kisan a wanne matsayi kike. To ki shiga hankalin ki in kinaso mu rayuwa cikin kwanciyar hankali zamaninmu ya shuɗe a haka. Kada ki taba damuwa da halinda zanshiga bama a wajen Denti meerah ba koda a jaririn da aka haifa yau ne. Domin na daɗe da Haɗiye zuciyata,bana ma jinta bare ta kaini ga shiga matsalar da bazan iya fitar da kaina ba" 

Suna tafe inna Mairo tana nusar da Nuratu rayuwar da suke ciki har suka iso wajen rabon abinci,kaman yanda suka tsammata kuwa an gama raba busashshiyar gurasar da mutum zai gabjeta ko babu ruwa. To su basu samu ba. Kallon banza mai rabon abincin tayi musu,ƙatuwar matace hannun ta riƙeda wani ƙaton ludayi na itace wanda take juya miya a cikin wata tukunyar kasa dake kan murhu. 

"Tsabar Walaƙanci bakai zaka ciyarda kanka ba,amma kazo ka karbi abunma sai kaga dama tukunna. To ya ƙare saiku jira na gobe." 

Kallon miyar dake kan wuta Nuratu tayi da kuma uwar gurasar da take cikin wata babbar ƙwarya,amma kuma matar tace musu wai babu abinci saidai su dawo gobe. Meyasa kowa bashida tausayine wai. 

Haɗiyar yawu tayi saboda yunwar da take mintsininta. 

"Dan Allah baaba Sahura ki ɗan bamu wlh yunwa mukeji tun safe bamuci komai ba,kuma aikine mukayi uwargijiyar mu ta hanamu tafiya shiyasa,gashi can dayawa kin ajiye mai zakiyi dashi" 

Cikeda ƙukewa hawaye yana taruwa a idanunta tayi maganar. 

Aikuwa kaman jira baaba Sahurar Take ta juyo kanta kaman zata cinyeta. 

"Lallai yarinyar nan dama ana faɗin kin fiye rashin kunya da shiririta ashe da gaskene,to innaga dama daga yau bazan ƙara baki abinci ba naga yanda zakiyi ko zaki ƙwata kai" 

Kirjinta ne ya buga dummm jin abinda baaba Sahura tace, inkuwa haka ta faru to kashinta ya bushe,kallon fuskar inna mairo tayi wanda itama bataji daɗin furucin Nuratun ba. 

Saurin zubewa tayi akan gwiwoyinta tana roƙon Baaba Sahura tareda haɗa hannayenta waje ɗaya tana murzawa. 

"Dan Allah kiyi haƙuri baaba sahura wlh ba haka bane yunwa nakeji shiyasa" 

Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kukan ban tausayi. Kallonta baaba sahura tayi tana kanne ido ɗaya da kuma ɗaga kai alamar takama,saidai kuma ta alama taji daɗin roƙon da Nuratu tayi mata domin fuskarta ta ɗan sarara. 

"Shikenan tunda kin roƙa na janye magana ta" 

Ajiyar zuciya Nuratu ta sauƙe kafin ta tashi akan gwiwoyinta tana kaɗe kasar dake kan gwiwarta. Har sunyi niyyar juyawa zasu tafi baba Sahura ta cillowa nuratu gurasa guɗa ɗaya,bata iya ta cafke ba sai ta faɗi a ƙasa. Kallon gurasar tayi da take kwance a cikin rairayi ta kuma kalli baba sahura wacce tayi kaman bata aikata komai ba na rashin daidai. Saima juyawa da tayi ta cigaba da aikin gabanta. 

Tsugunnawa Nuratu tayi cikin sanyin ta ɗauki gurasar kana ta fara ƙade ƙasar dake jiki tana kallon inna Mairo. 

Itama kallonta takeyi da alamu masu wuyar fassara,tafiya ta farayi zuwa hanyar sansaninsu,ganin haka yasa Nuratu raba gursar biyu tabi inna mairo a baya da sauri ta miƙa mata. 

Juyowa tayi ta karba suka fara tafiya. 

"Keee keee ku waɗannan masu tafiya ku biyun kuzo nan" 

Juyowa sukayi a tare suna kallon mai maganar, Gimbiya Asma ce matar Yerima Kabeer babban ɗan sarki Abduljalal mai jiran gado, bazata wuce shekara goma sha Bakwai ba don aurene akayi mata da wuri irinna tsarin gidan sarauta. Itama ƴar sarki ce daga yankin Masarautar Ghana,wanda suma suna da madafin iko,shiyasa take jinta da mulki da taƙama,sannan take taka wanda taso saboda jin itace Sarauniyar garin ta gaba. Duk da mijinta hankalinsa ba iya ga kanta ya tsaya ba harma da bayin dake gefensa,kuma duk wacce ta ɗau hankalin mijinta bata barinta haka saita illata ta,shiyasa sunanta yake kaɗa duk wata hantar bayin dake masarautar.  

Juyawa su inna mairo sukayi suna kallonta,tafiya take cikin takama jikinta sanye da wata doguwar riga da jan saƙi mai tsada,wuyanta cikeda zinare, tsohon cikin dake cikinta yaƙarawa suffarta ɗan cika,idonta cikeda baƙin kwalli kasancewar tana ɗan haske sai yataimaka wajen yiwa fuskarta gwarjini. 

Bayan ta bayi ne guda uku,gefe da gefe sai kuma ta tsakiya a bayanta wata tariƙe lema akanta domin kare mata hasken rana. Da alama tafito zagayawa ne. 

"Ke ƙaramar kizo nan zan aikeki tsohuwar masarsuta ki karbomin saqo  

Zaro ido Nuratu tayi ta kalli inna mairo. Dan harga Allah duk wanda ya kalli fuskar nuratu to kuwa yaga alamar gajiya da galabaita sosai. Fasihmman data ambaci tsohuwar masarauta inda iyayen sarkin suke,can ne masarautar kafin a gina wannan a dawo, kuma akwai tafiya mai ɗan tazara tsakanin sabuwar da tsohuwar, iya kafin mutum ya fita daga da'irar masarautar ma ya nufi can tafiyace mai zaman kanta. 

Ganin inna mairo batace da ita komai ba yasa idanuwan data zaro ɗin suka fara zirarar ruwan hawaye,saurin kama gefen zaninta tayi ta goge mata saboda karsu kula. Ita kanta tasan aikan da aka saka ɗiyar tata yayi mata yawa,domin ko ita akace taje ta dawo a yanzu an gamata da aiki ballantana kuma ƙaramar yarinya kamar Nuratu,to amma shin ya zasuyi?. 

Wata dabara ce ta faɗo mata,da sauri taja hannun nuratu ta ƙarisa gefe kaɗan da Gimbiya asma,wacce take wani yatsina fuska tanayi musu kallon kamar takalli kashi. 

"Ran Gimbiya ya daɗe nace idan babu damuwa ni zanje miki aikan,yarinyar batajin daɗin jikinta" 

Ta ƙarisa maganar tana haɗa hannayenta biyu tareda langabar da kanta gefe. 

"Ai na ganki nace tajemin aiken,bake nayi niyyar aikaba ita nayi niyya,idan taje a hanya mala'ikun ajalinta su ɗauketa,ina ruwana da jinyarta. Tukunna ma yaushe bawa a masarautar nan yafara maida yawunsa idan aka bashi umarni. Sa'ar ki ɗaya wannan maganar taki kin furtata ba'a fusace nake ba,da saina sakata zuwa da dawowa sau goma" 

Saurin durƙusawa tayi jikinta yana rawa tana bata haƙuri,ganin hakan bazai kaita ba yasa ta tashi da sauri ta tura Nuratu gaban gimbiya Asmah akan ta aiketa,ita kuma tayi gaba da sauri. 

Aikan magani ne da aka aiko mata daga garinsu,bataso ta aiki babba tana tsoron karya bsta mata shiri,shiyasa tana ganin Nuratu tasaka a ranta itace daidai da aikennata. 

Jiki babu ƙwari haka ta karbi bayanin gun wanda zataje ta nufi hanyar fita daga masarautar,har haɗa hanya take saboda tsabar gajiya da yunwa. 

Har tazo wuce ta wani waje taji an cafko hannunta zuwa bayan katangar. Har ta gigice zata kwaɗa ihu taji muryar ummannata. 

"Ke dan Allah kiyi shuru,hungo ruwa maza sha,ga tsagin gurasata ma maza haɗa dukka ki cinye in kina tafiya a hanya,sannan kiyi sauri karki tsaya a ko ina,daga kin karbo mata kuma maza ki dawo gida kinji?" 

Ɗaga kai tafi dan maganar bazata fito ba tacika bakinta da gurasa tana binsa da ruwa. 

Da kallon tausayi inna mairo take binta harta gama ci tasha ruwan,ajiyar zuciya tayi kafin ta kama hanyar fitan. Ba kaman ɗazu ba yanzun da ɗan kumarinta. 

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

JODA by sadisakhna 

DAAƊIN ZAMA by Seemah 

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by gureenjoh 

*A whatsapp 

One 1k

Two 1800

Three 2400* 

 *Telegram 

One 700

Two 1200

Three 1500*

Account details 

0545475847 

Gt bank 

Fatima Muhammad Gurin 

Sai a tura shaidar biya ta

09035784150

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post