Abu A Duhu Page 4 by Fadeela Lamiɗo - Abokiyar Hira Novels


 ABU A DUHU

       NA

Fadila Lamido 


ADABI WRITER’S ASSOCIATION


Page 4

Dakewa ta yi ta hanyar boye firgicin ta tare dayin kasa da murya tace, "Unaisa lafiyar ki?" Cikin sauri ta dago ta kalli Dada adan firgice dan batai tsammanin ganin ta ba, dago hannunta ta yi daga kan sakatar da take kokarin cirewa sannan tace, "Lafiya lau Dada"

"Unaisa me yake damun ki? Kuma ina zaki da wannan Dattijon daren?"

"Gida  zani Dada dakin Innawuro, na kasa bacci kuma na tabbatar matsawar ba dakin Innawuro na kwanta haka zan wayi gari ban runtsa ba." Wani irin kallo Dada taiwa Unaisa sannan tace, "Ko za ki kwana baki yi bacci ba babu inda zaki da wannan tsohon daren, ki koma ki kwanta kar Malam ya fahimci wani abu, kin sani sarai idan Malam ya ganki anan duk zuciyoyin mu ba za su yi dadi ba, idan gari ya waye saiki tafi inda kika fi sakewa, banda abinki Unaisa garadan maza ke kawo miki hari"

"Ai Dada da na kasa bacci na tuna kalmomi biyu da mutumin ya fada, na tuna mara lafiyan kafar ya ce, "Gudu da waiwaye shi ke kawo mugun zato, sannan ya sake cewa kowa ya ki tsotse hannu beji dadin miya bane." Lumshe ido Dada ta yi zuwa can ta bude sannan ta ce, "Sai dai ya je  ya tsotsi hannun uwar sa, danni ban gane inda zancen shi ya nufa ba, wallahi Unaisa ke macece ba namiji ba, kuma kin kai minzilin da maza zasu yi tunanin kasancewa da ke musamman idan su ka fahimci cewa ke kadaice a gidan"

"Dada gobe zan dawo, ni yanzun idan ba jina na yi dakin Innawuro ba hankalina bazai kwanta ba."

"Wato kina nufin kin kafe kenan sai kinbi hanya awannan lokacin?" Shiru ta yi dan haka Dada ta ce, shikena, Allah ya tsareki aduk inda kike" Juyawa ta yi ta nufi dakin da ta fito saidai bata iya runtsawa ba tunda taji alamun Unaisa bata dawo ba, idon ta bushewa yayi tunani da zullumi sun hanata bacci.

                                   ****

Unaisa kuwa cikin tsanin firgici tare rawan jiki ta isa gida bayan ta bude gidan ta shiga bakinta dauke da addu'a, sannan ta bude kofar dakin ta shiga tare da kunna wutan lantarkin dake dakin, take haske ya gauraye dakin, hannunta tasa ta cire nikaf din dake fuskarta ta ninke ta aje a inda ta saba ajewa, sannan ta cire hijjabin, shima ninkewa ta yi ta adana sannan ta dauki rigar da ta saba sawa idan zata kwanta ta cire kayan jikinta ta saka su, wani mayafi ta dauko babba ta yafa tare da daurewa a wuyan ta, dan tunda ta fara nono ko ita kadai adaki bata iya barin kirjinta abude, zaune ta yi abakin gadon ta hada kai da guiwa, kanta abude gashin kantane ya baje agadon bayanta baki sidik.


Tsayon lokaci ta dauka ahaka, hawaye na zuba afuskarta yayin da nutsuwa take kara shigarta, sai misalin 3 ta kwanta ba jimawa bacci ya dauke ta.


Washegari da sassafe Dada ta iso bugu biyu ta yi Unaisa ta gane Dada ce dan haka ta je da saurinta ta bude kofar tare da fadawa jikin ta.


Lumshe ido Dada ta yi jin Unaisa jikinta, a jiyan zuciya ta sauke me karfe sannan suka nufi cikin gidan Unaisa na kwance ajikinta, cikin daki suka nufa, yayin da Dada tabi Unaisa da kallo tsawon lokaci sannan tasa hannunta ta cire nikabin, fuskarta ta zuba mata Ido tsawon lokaci sannan tai maza ta rike kunnen Unaisa ta murde, cikin sauri Unaisa ta yamutsa fuska tare da kanne idonta daya tame nuna alamar tana jin zafi, "Dada ki yi hakuri Allah akwai zafi."

"Aina dauka bakisan inda ke miki ciwo ba Unaisa" kara matse kunnen Unaisa  Dada ta yi tana bin kyakyawan fuskarta da kallo.

"Dada nasani fah"

"Meyesa kika biyo hanya da daddare?" Hannun Dada dake rike da kunnenta ta rike sannan ta ce "Bazan kuma ba Dada ki yi hakuri." Sakin kunnen Dada ta yi har yanzun tana binta da Ido, ta cigaba da fadin, "Unaisa na yanke wata shawara zan sake zuwa gida da maganar ki akaro na biyu" Girgiza kai Unaisa ke yi yasa Dada dakatar da zancen ta, "Meyasa Unaisa?" 

"Dada dan Allah ki bar su,  yanzun shekara biyar da rasuwar Innawuro tun inna wuro na raye basu taba min kallon arziki ba, ranar da Innawuro zatabar duniya ta tara gaba daya danginta ta yi yinkurin ba basu amanata basu duba halin da take ciki ba su ka ce baza su amsa ba, haka dangin Baffah da suka zo gaisuwar Innawuro" Hawaye Unaisa ta share sannan ta cigaba da cewa,  "Suma cewa suka yi tabbas Baffa  nasu ne amman ni kar a kara danganta su da ni, Dada dan Allah na roke ki karki kara danganta ni da kowa, ni ma bana tunawa da kowa, kawai dai bana mancewa Innawuro ta ce tabarwa Allah amanata sannan tabarwa miki, bana son alaka da kowa Dada,  nafison na ganni ni kadai Kamar yadda Innawuro tabarni ni daya, ni kaidai ta haifa hakama Baffa na."

Itama Dada hawayen dake makale a idonta ta share sannan tace, "Amman Unaisa yanzun fa kin kai minzilin aure matukar ba aure kika yi ba hankalina bazai taba kwanciya ba, bacci na zai zama rabi da rabi ne, koda a ce tare dake nake kwana nake tashi zuwa wannan lokacin aure ne ya dace dake, bare kuma ace ke kadai kike rayuwa acikin gidan nan, kuma cikin Unguwar nan babu wadda be sani ba." Aguje Unaisa ta fita adakin, binta da kallo Dada ta yi sannan ta mike da sauri tabi bayan ta, gefen famfo ta same ta tana sheka amai, cikin tsananin mamaki ta shiga taimaka mata, bayan aman ya tsaya ta wanke mata fuska sannan ta rukota suka dawo daki, saman gadon Unaisa ta kwanta tare da jawo katon mayafi ta rufe jikinta, karkarwa jikinta ke yi alamar tanajin sanyi, ganin haka Dada ta mike ta tattara ragowan kayan abincin dake dakin ta daura girki.


Misalin sha biyu ta sake shigowa har yanzun Unaisa karkarwa take dan haka ta janye mayafin a hankali ta sake taba jikinta har yanzun da zafi rau, ajiyan zuciya ta yi sannan tace, "Unaisa, yau kuma dan na yi maganar aure shine harda zazzabi?"

"Dada gaba nane ya ke faduwa."

 "A kan wanne dalili me? Hawaye Unaisa ta share da tafin hannun ta sannan ta ce,  "Na ji ne kince wai nakai munzalin aure." Kallo Dada ta bita da shi gefen idonta yayi ja sabo da share hawaye, duk da babu kwalliya afuskarta Unaisa kyakyawa ce sosai, kawar da fuaka Dada ta yi daga kallon Unaisa sannan tace, "Ai da na ce kinkai minzilin aure ina nufin daga yanzu zuwa kowanne lokaci kinkai a miki aure bawai ina nufin yanzu yanzu bane" Ajiyan zuciya Unaisa ta sauke me karfi sannan tace, "Allah ya sa kafin nakai karshen matakin Allah ya yanke numfashina kamar yadda ya yanke na Innawuro." Kallonta kawai Dada ta yi sannan tace "To ki saki ranki ki bude jikin ki ko zazzabin ya sauka."


Saida Dada ta tabbatar zazzabin Unaisa ya sauka sanan ta wuce gida, tun daga wannan ranar kullum sai taga motar bakin nasu ko in zata makaranta ko idan ta dawo, saidai bata kula su duk kiran da zasu  mata bata kula su.


                               *****

"Muftahu Moddibbo ya na damuwa da lamari yariyar, hakan na bakanta mini rai, wata biyu kenan  muna zarya a hanyar nan da bata da kyau amman ko kadan be taba nuna ya gaji da bibiyar ta ba, saidai ma ka ji yana cewa wai kurma ce, tun bana yadda har na fara yadda, saboda duk kiran da  zanwa yariyar bata taba koda dago kaine ta dube ni har bakaken magana na gaya mata amman bata ko nuna alamar tasan me nake cewa ba, har takai yanzun ni kaina inason nasanta acikin idona, ina son inga fuskarta sosai."

Wani irin kallo Muftahu yaima Magaji, "Moddibbo ya gaya maka dalilin son yin magana da yariyar ne?"

"Kaima kasan bazai gaya min ba."

"Toh karka fara son ganin fuskar ta, bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane, sannan kuma barin ƙara tunatar da kai dan wata kila ka manta, in za'ayi tubka a yi mata hanci dan gudun kata da warware."

"Ban gane ba Muftahu, ni nasan halin Modibo ciki dabai, sai dai yace zai mata abin da ya saba ba abin da nasaba ba."

"Idan ko har ya mata abun da ya saba hnmm rayuwarta zata canza"

"Ni kuma fa? Idan namata wadda na saba?" Gyara zama Muftaho yayi a cikin kujerar motar sannan ya ce, "Ni fa yanzu tsoron ka nake ji, amma ina son zama da Moddibo duk da cewa wani lokacin bashi da kirki"


Kwashewa da dariya Magaji ya yi sannan ya ce, "Ka dai fadi gaskiya ni nasan nafishi dadin zama"

"A'a fa, kai kanka kasan cewa zama dame turare ya fi zama da maƙeri, domin zama dame turare ko be baka turaren ka fesa ba ka ji kamshi ajikin ka, zama da makeri kuwa ko be konaka ba taratsatsin wuta ya ya same ka." Lumshe ido Magaji yayi tare da fadin, "Na ji, sauka min amota akwai in da zani." Cikin sauri Muftahu ya fice a motar Yana murmushi yayin da Magaji ya zagaya ya shiga motar tare da figanta aguje.

  

                                 ***

Ya dade a tsaye a kofar gidan ganin babu alamar zata fito kamar kullum, jiran fitowarta ya ke ganin ya jima ya waiga yace, "Moddibbo Ina tunanin bata cikin gidan."

"Tana ciki Magaji kacigaba da bugawa" Wani mutumi ne da ya zo wucewa yai karaf yace, "Tana ciki amma fa bazata taba bude kofar ba barema har ta yi magana" Muftahu dake jingine jikin motar ne yayi saurin cewa "Toh me yasa hakan?"

"Babu wadda zai gaya maka dalilin." Modibo dake cikin motar ne yai saurin kiran mutumin da yaga yana kokarin wucewa, bayan ya karaso gaban motar daker Modibo ya iya bude baki yace, "Baba bani labairn abin da ka sani game da ita." Kallon Modibo yayi sannan ya ce "An ce kyakyawa ce ita, kyanta ya shahara, ni makocinta ne amman bantaba ganin fuskanta ba, kafarta kawai zaka gani ya tabbatar maka da cewa fara ce sosai, kuma ita kadai take rayuwa agidan."

"Toh ina iyayenta?"

"Iyayen ta sun kasance tsofaffi ne tukuf domin ance lokacin da suka haifeta shekarun su arba'in da biyar da aure basu haihu ba."

Yamutsa fuska Moddibo ya yi sannan ya ce, "Ina zuwa malam, ni inason nai magana ne da ita amman abin ya gagara, na bita nabita amman ko kalma daya bata taba furta min ba, hakan yasa nafara tunanin ko kurma ce?"


"Ba kurma bace, amman ba zata kulaka ba, ka yi hakuri kawai yarona duk nacin ka bazata yi maka magana  ba, domin tun da nake ban taba jin muryan ta ba, kullum zata zo ta wuce bata magana da kowa, an taɓa yin wani saurayi da yayi nacin sonta, da ta zo zata bude gidan yake shigewa, shekaran sa daya da wata biyu yana shiga gidan bata taba tankashi ba, dan haka ya gaji ya daina zuwa." Lumshe ido yayi sannan ya bude su suka yi ido hudu da mutumin cike da kasaita yace, "Me yasa take rufe fuskar ta?, Bama wannan ba, kana da tabbacin ba kurma bace ko?"

"Ba kurma bace an tabbatar min da hakan" Idon sa ya daga ya kalli Magaji dake kofar gidan ya ce "Magaji ku cire min kofar gidan" Bayan bada Umarnin nasa bude murfin motar yayi yayin daya zuro kafarsa me lafiya...



Fadila Lamido...✍️

07014197556

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post