🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 4
A kaf nahiyar aljanu shine mai ƙarfin faɗa a ji, saboda tarin dukiya,da tarin mayaƙan aljanu da yake da su
Shine Sarkin musulman aljanu,kuma limaminsu,a duk duniya babu wata masarauta ko daular kafirai da bai yaƙa ya ga bayanta ba,banda ɗaya,wato Daular Baruda
A kowanne lokaci tsawon shekaru ashirin sarki Laimus ya kasa sukuni saboda baƙin ciki da ɗacin zuciyar da yake ciki na rashin nasara,ko cika alƙawarin da ya ɗauka sama da shekaru ɗari da goma baya, shiyasa ya yi duk iya yinshi,amma tasirin sarki Akaal a wancan lokacin ya shafe nashi,duk da kasancewar sarki Akaal mutum,amma manyan matsafan aljanun da yake tare da su daga wasu nahiyoyin na duniya sun shafe jarumtarshi
Wannan kenan!
💫
Shiru fadar ta ɗauka,ana sauraren saƙon da ɗan aiken sarki Laimus,wato Shabbir ya kawo, lokaci guda kuma fadar ta ruɗe da sowar murna da farin ciki,sarki Laimus da annuri ya cika fuskarshi ya dubi Shabbir da fara'a ya ce"Shabbir!
Yanzu kana nufin daular Baruda ta ruguje kenan?babu sarki Akaal a raye?"
Shabbir cikin girmamawa ya ce"haka ne ya shugaba na!"
Sarki Laimus ya ce"Allahu Akbar!to ya batun sarkin yaƙi Anudu da mafarauci Murad?"
Shabbir ya sake rissinawa ya ce"dukkansu sadaukin sarki Iyaad ya shafe labarin su ya shugaba na!"
Kabbara mai ƙarfi ta ratsa fadar,kowa fuskarshi ɗauke da murmushi,sarki ya ce"kuma da gaske ajiyarmu tana cikin garin aminci Daular Tayaar?"
Shabbir ya jinjina kai cike da girmamawa ya ce"haka ne ya shugaba na!
Sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba"
Shiru fadar ta yi ana sauraren Shabbir,sarki Laimus ya ce"ina saurarenka amintacce na"
Shabbir ya gyara zama ya ce"a halin yanzu ajiyarmu baya addinin mu kamar yadda muka sani,kuma babu yiyuwar zai koma ɗin, saboda tsanar musulunci da musulmai sune abubuwa mafi girma da ake rainon duk wani ɗa a daular Baruda
Sannan Kamar yadda muka san jinin SUHAIF BIN YASSAR suna da kafiya da tsatstsauran ra'ayi,to shima ajiyarmu yana da wannan gadon"
Murmushi sarki Laimus ya yi,ya dubi Shabbir ya ce"duk wannan mai sauƙi ne,kuma mai wucewa ne
Na san sarki Iyaad sosai,sarki ne mai adalci,kuma a ko'ina aka samu adalci ana samun nasara,don haka mu zuba ido kawai,mu taya shi da addu'a,amma tabbas sarki Iyaad zai ƙarasa abin da ya fara, kamar yadda ya yi abin da ya gagare mu a baya"
"Ina fatan haka ya shugaba na"a cewar Shabbir yana murmushi
*DAULAR TAYAAR*
washe gari ta kama juma'a, Kamar yadda ya zama al'ada a daular Tayaar sarki Iyaad ne yake jagorantar sallar juma'a ta ƙarshen kowanne watan Musulunci idan ya kama,to yau ma haka ne, kasancewar yau ta kama ashirin da bakwai ga watan Safar ya zama shine zai jagoranci sallar juma'ar
Gashi kuma a yau ne za'a laƙanawa ribatattun yaƙin da aka kamo daga daular Baruda kalmar shahada,ga waɗanda suka yi turjiya kuma a ƙarar da rayuwarsu, kamar yadda yake doka a ƙasar ta Tayaar
Kuma a yau ne za'a yi liyafar murna ta wannan gagarumar nasarar da aka samu,irin wadda ba'a taɓa samu ba,asalima babu wata daula da ta taɓa karawa da Baruda ta samu nasara,sai dai ko Baruda ta yi nasara ko a yi kunnen doki
Daidai farkon mukhtarin sallar azahar Sarki Iyaad ya fito don ya jagoranci sallar juma'a,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya hau mumbari don fara huɗubar sallar juma'a
Dakaru ne suka gabato da ribatattun yaƙi zuwa gaban masallatan, waɗanda suka yi ƙasa da kai cikin jin ƙasƙanci
Ba'a ɗauki dogon lokaci ba aka idar da sallar juma'a,daga nan limamin Masallacin ya gudanar da jawabai masu ratsa zuciya,a ƙarshe ya tambayi ribatattun yaƙin shin sun amince da Allah shi ne abin bauta?
Kuma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama bawanshi ne?
Ba tare da ɓata lokaci ba suka ce sun yarda,take liman ya laƙaba musu kalmar shahada,suka maimaita,take wajen ya ɗauki kabbara mai ƙarfi,bayan an nutsa liman ya cigaba da jawabi
"Kamar yadda na faɗa Allah ɗaya ake bautawa,rana da wata,da kogin Baruda da kuke bautawa dukkansu alama ce ta wanzuwar Ubangijin talikai, ayoyi ne daga ayoyinshi,ya yi su ne don mu ƙara iymani,ba don mu rasa shi ba
Muna yi muku Barka da shigowa Musulunci, Allah ya ƙara mana iymani baki ɗaya,ya ba mu rabo mai albarka"daga nan dakaru suka wuce da su don a koya musu al'amuran musulunci
Daga nan sai babban aiki,wato jin ra'ayin sadauki Kazuzi kan batun addinin Musulunci,wanda tunda aka kawo shi garin Tayaar har zuwa yanzu bai saka ko da ruwa a bakinshi ba,babu wanda zai iya cewa ya ga ko da ƙwayar idanunshi da suka kasance a rufe a kowanne lokaci aka ziyarce shi,mutane da yawa sun ayyana hakan a matsayin borin kunya,duba da cewa ba'a taɓa samun ko da kwatankwacin nasara akansa ba,kai tsaye yake ayyana dakarun da suka tunkare shi don yaƙar shi da sunan mata
Sarkin yaƙi da jama'ar shi ne suka fito da shi daga ɗakin hukunci,har lokacin babu wanda ya yiwa magana,babu wani yunƙuri da ya yi banda abin da aka saka shi ya yi
A gaban sarki Iyaad da limamin babban masallacin daular Tayaar aka gurfanar da shi,kamar koda yaushe kanshi a ƙasa,liman ya dube shi ba tare da wata shakka ko tsoro Ba ya ce
"Sadauki Kazuzi!
Muna yi maka Barka da zuwa daular Tayaar,ɗauka mai cike da adalci da girmama ɗan adam,muna yi maka fatan samun rabo mai girma,a don haka muke yi maka tayin shiga mafificin addini, addinin lumana,addinin zaman lafiya,wato addinin musulunci,menene ra'ayinka akan hakan?"
Shiru ya ziyarci wajen,gaba ɗaya jama'ar da ke wajen suka yi shiru suna jiran jin ra'ayin Kazuzi akan batun da liman ya zo masa da shi,sai dai har bayan shuɗewar wasu daƙiƙu babu alamun zai yi magana,wanda hakan ya kaɗa hanjin wasu daga cikin jama'ar, liman ya sake dubanshi cikin sarewa,amma ya dake ya ce"kai muke saurare Kazuzi!"
Nan ma dai shiru babu amsa, Sarkin yaƙi ya dubi Sarki Iyaad don jin ra'ayinshi,sarki Iyaad ya ɗan girgiza kai ya ce"a sake ba shi lokaci,duk da cewa ba mu san abin da ya saka shi yin shirun ba,amma nan gaba muna fatan ya magantu,kuma mu ji alkhairi daga gare shi
Da haka taron ya watse ran jama'a da yawa babu daɗi,don wasu sun so ya musulunta,wasu kuma sun so an ƙarar da rayuwarshi, cikinsu har da Hayat wadda ta koma cikin turakar ta a fusace,ta kori dukan kuyanginta ,ta fizge lulluɓinta ya jefar,sannan ta haye gadonta tana hargitsa dogon gashinta
Miƙewa ta yi a fusace, ba tare da tunanin komai ba ta fito daga ɗakin, kuyanginta suka rufa mata baya,kai tsaye ta nufi inda keken dokinta yake,ta shiga, kuyanginta suka bi ta,kai tsaye ta nufi ɗakin hukunci
A fusace ta ƙarasa inda dakarun suke,ganin yadda ta zo a fusace suka yi azamar buɗe mata ƙofa ba tare da ta yi magana ba,kai tsaye ta afka ɗakin a tsananin fusace
Yana zaune a inda ya saba zama,sai dai yau saɓanin koyaushe yana zaune a jikin bango Ya jinginar da kanshi, hannayenshi da ƙafafunshi ɗaure da manyan sarƙoƙin da har yanzu ba'a raba shi da su ba,tana zuwa ba tare da tunanin komai ba ta cafki gashin kanshi ta shiga jijjiga kan nashi da ƙarfin tsiya,tana haɗa kan nashi da bangon ɗakin da yake jingine,amma ko buɗe idanun nashi bai yi ba ballantana ya nuna ya san abin da take yi
Sai da ta yi mai isar ta sannan ta hankaɗa shi,kanshi ya sake dukan bango ya bayar da wani sauti,su kansu kuyangin nata da dakarun da suka biyo ta sun tsorata da wannan fusatar tata,ta fara magana a kausashe
"Baka jin magana?
Har yanzu kana jin kanka a wata tsiya bayan duk wani alkadari naka ya karye?
Ka yi faɗuwar baƙar tasa!daga yadda kake jin kanka a matsayin Sadauki zuwa bawa,bawan ma ƙasƙantacce?har yanzu kana jin kana da wani tasiri?"shiru ta yi tana jan numfashi a fusace,a yayin da ɗakin ya yi shiru kamar ruwa ya cinye su
"Na ba ka nan da gobe da za'a sake jin ra'ayinka!ka amsa cewa ka musulunta,ko kuma ni da kaina na raba kanka da gangar jikinka!!!
So nake ka ji cewa duk wata ji kima da iko da izza da ka nuna sun rushe, saboda a ƙarshe mace ce ta raba ranka da gangar jikinka!!
Ya rage naka ka zaɓi izza ta halaka ka,ko ka saukar da kai,ka ɗauki hakan a matsayin gargaɗi na ƙarshe"tana kai wa nan ta miƙe a fusace tana take ƙafarshi,ta yi waje, suma sauran dakarun suka bi bayan ta
Sai da ta fice daga cikin ɗakin Kazuzi ya buɗe lumsassun idanunshi yana bin hanyar da ta bi da kallo,bai taɓa jin zafin maganar da take gaya masa ba ko ya saka ta a rai ta dame shi,asalima tun daga sanda ya rasa wadda yake jin don ita yake rayuwa gaba ɗaya duniyar ta fice masa a rai,amma yana ganin zai yi maganin wannan yarinyar da take damunshi da hayaniya
Ita kuwa gimbiya Hayat gargaɗi mai ƙarfi ta yiwa kuyanginta da dakaru akan su kiyayi sanar da mahaifinta abin da ta yi,don tsanar Kazuzi ce dai babu wanda zai iya hana ta yi,kuma muddin tana numfashi sai ta ga bayanshi, shiyasa bata fatan ya amshi musulunci ma
Da yamma aka gudanar da gagarumar liyafa ta nasarar wannan gagarumin yaƙi,da addu'ar Allah ya haska zuciyar sadauki Kazuzi shima ya amshi musulunci Kamar yadda sauran dakarun Baruda da aka kama suka yi
Ita dai gimbiya Hayat bata halarci taron ba,ta aika a gayawa sarki Iyaad cewa bata jin daɗi
*DAULAR KAIZUR*
"Barka da wannan lokaci ya shugaba na!"
Ɗaga idanu sarki Mu'iz ya yi yana kallon sarauniya Amna da ta duƙar da kai ƙasa tana jiran amsa,a hankali ya furta "Barka da zuwa sarauniyar kaizur"
Sauke numfashi ta yi tana gyara zama a gabanshi,daga yadda ya ga fuskarta ya tabbatar da cewa akwai damuwa, cikin kwantar da murya ya ce"da wani abu ne sarauniya?"
Jan numfashi ta yi, lokaci guda rauninta ya bayyana, cikin rawar murya ta ce"na yi mafarki da Yariman kaizur ne ranka ya daɗe!
Haƙiƙa yarima yana cikin wani hali mai wuyar fassarawa"
Gaban sarki Mu'iz ya buga,dama ya yi tunanin hakan zata faru,a duk lokacin da wani mummunan abu zai samu yarima Sahal sai sarauniya ta ji a jikinta ko ta gani a mafarkinta,hakan kuma yana tasiri sosai a gare ta
Cikin kwantar da murya ya ce "baya cikin kowanne hali sai alkhairi da izinin Allah
Nima na yi mafarki da shi yana cikin kyakykyawan yanayi,har ma ya sanar da ni a tsammaci dawowarshi nan kusa zuwa sarautar shi in sha Allah "
Murmushi sarauniya Amna ta yi, hawaye suka cika idanunta, cikin sanyin murya ta ce"kwantar min da hankali kake yi ya shugaba na?
Hankalina ba zai iya kwanciya ba har sanda zan ga yarima na ya dawo cikin masarautar nan, ka san yadda nake ji,ina jin zafin cin amanar da aka yi min aka fitar da Yarima daga cikin masarautar nan"zuwa yanzu kuka take yi sosai
Dafa kafaɗarta Sarki Mu'iz ya yi, cikin ban baki da lallashi ya fara magana "kowacce rayuwa ta ɗan adam akwai jarrabawa,ki ƙaddara haka tamu jarrabawar take, shekaru ashirin kenan da ɓatan yarima Sahal,a tsawon waɗannan shekarun ban taɓa fitar da rai cewa zai dawo gare ni ba,
Na hukunta dukkan masu laifi,na yanke hukuncin kisa ga waɗanda na kama dumu dumu da aikata laifin,amma hakan bai bayyana min yarima ba,dole na bar wa Allah komai,damuwa da tashin hankali babu abin da za su ƙara yi sai dagula lissafi
Babu abin da nake tunawa na yi baƙin ciki irin waccan baƙar azzalumar"sarauniya Amna ta ɗago kai a sanyaye ta ce"wacce azzalumar?"
"Wadda take amsar hukunci tsawon shekaru ashirin,amma har yanzu babu abin da ya sauya zani"
Sauke numfashi sarauniya ta yi,a hankali ta ce"Ni kuma sai nake ganin kamar babu laifinta, saboda dole zata yi raunin da ba zata iya hakan ba"
Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi, ya ce"ta amsa da bakinta cewa ita ce,amma a yadda na fuskanta akwai waɗanda suka saka ta,su nake so na sani kafin na yanke hukuncin "
Gimbiya Amna ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"fatan nasara ya shugaba na, Allah ya durƙusar da maƙiyanka ya ƙasƙantar da su a gabanka "
Sarki Mu'iz ya yi murmushin bayar da ƙwarin gwiwa, sarauniya Amna ta rissina ta ce"na bar ka Lafiya ya shugaba na"daga haka ta miƙe cikin nutsuwarta ta fice daga ɗakin,bayan sarki ya sallame ta
*Ga masu sha'awar VIP group an buɗe,ku tuntuɓe ni a number ta gata nan a ƙasa*
#Nusy_bee
08125952284
