SHA'AWA DA JARABA*
(Love and Romantic story)
💋💋💋
Mom Islam
Page 15-16
Da sauri ya janye jikinsa tare da sauka daga bed ɗin, cikin sauri ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa, kana ya sanya towel ya goge jikinsa sannan ya fito yasa kaya cikin sauri, "idan kin gama ki kulle Dady ya sauka a jirgi tun ɗazu.."
Yah Muzaffar ya faɗa yana ficewa bayan ya ɗauki key car ɗinsa, kai tsaye motarsa ya shiga, yayi mata key, driving yake yana saurarar karatun Alkur'ani mai girma, idanunsa na kallon titi, yayinda zuciyarsa da hankalinsa suka koma gida, shi yama mance da maganar dawowarsu Dady,
Cikin ikon Allah ya iso anguwar tasu, a bakin get ya danna horn mai gadi ya buɗe masa sannan ya shigar da motar ciki, jerin motocin da ya gani ne ya tabbatar masa da cewar su Dady da Abba sun iso, ƙoƙarin saita nutsuwarsa ya fara yi, kana yaci gaba da takunsa cikin izza da isa, sallama yayi daga bakin ƙofar parlon, mutanen dake zazzaune a parlor suka amsa, Dady da Momy da Diyana da Fateemah, Momy da Dady suna zaune a lallausar Sofa mai zaman mutum biyu, sai Diyana da Fateemah da suke ƙasa saman carpet a zaune, kowacce idan kaga fuskarta tana ɗauke da farinciki sakamakon dawowar Dady,
Yah Muzaffar ne ya ƙaraso cikin girmamawa yace "Sannu Dady.." Dady yai murmishi yana dubansa yace "sannu babban mutum kuma doctor"
Yah Muzaffar yai murmishi tare da gaishe da Dady yayi masa ya gajiyar tafiya, kana ya gaishe da Momy, Diyana da Fateemah suka gaishesa, har yanzu izzar tana nan, ya amsa kamar wani Basarake,
Shiru ne ya ratsa parlon Momy ta katse shirun da cewa "A kawo maka abincinka nan ne, tun ɗazu muka ci namu da Dady"
"A'a Momy, zanje part ɗin Abba inyi masa sannu da zuwa"
Dady yaji daɗin haɗin kan ƴaƴan nasu yace "aikam ya kamata"
Yah Muzaffar ya miƙe ya fice, kai tsaye part ɗin Abba ya tafi, sai da yayi sallama daga bakin ƙofa aka bashi izinin shiga kana ya ƙarisa ciki, Abba da Ummi suna zaune suma a saman lallausar Sofa, Yah Muzaffar ya fara gaishe da Abba, kana ya gaishe da Ummi, dukkansu suka amsa cikin fara'a da sakin fuska, Ummi tace "ikon Allah Doctor kaidai ba'a ganinka idan ba part ɗinku aka shiga ba?"
Ɗan murmishi yah Muzaffar yayi kana ya miƙe zai tafi, Abba yace "muje dinning muci abinci ni banci nawa ba"
Yah Muzaffar yace "Abba ga nawa can yana jiran shigowata kenan"
Abba yace "aiko dole kazo muje mu ci Abinci"
Baya iya jayayya da iyayensa, Abba ya miƙe tare da ƙarasowa inda yake ya riƙe hannunsa suka wuce dinning, Ummi ta bisu da murmishi, itakam har ga Allah rayuwar family ɗinsu yana birgeta kowa nason ɗan uwansa,
Cikin so da ƙauna suke yin breakfast ɗin, har suka kammala, yah Muzaffar ya miƙe yana cewa "Abba zan wuce sai Anjima"
Abba ya dafa kafaɗarsa cikin tausasa murya yace "Allah yayi maka albarka.."
Yah Muzaffar ya amsa da cewa "Amin ya rabbi Abba Nagode"
Kai tsaye part ɗin Dady ya dawo, ya wuce bedroom ɗinsa, har zai kwanta yaji ana kiran sallahar la'asar, yai alwalah a toilet ya fito ya wuce masallaci, bayan an idar da Sallah ya dawo bedroom ɗinsa ya kwanta, tare da ɗaukar system ɗinsa, yai ruf da ciki yana ci gaba da sarrafa system ɗin cikin hikima da ƙwarewa,
Wayarsa ce ta fara ringing, kafin ya ɗaga sai da kiran ya katse wani ya sake shigowa, ya ɗaga tare da cewa "Doctor Ashraf.." kafin Yah Muzaffar yai wata magana doctor Ashraf yace "Doctor Muzaffar na duba office ɗinka baka nan..?"
"Na dawo gida Abba ne ya dawo daga US, kuma na kammala aiyuka na"
Doctor Ashraf yace "wata yarinya ce tazo nemanka wai mahaifiyarta ce ta aikota"
Yah Muzaffar yace "manta da ita koma wacece.."
Ya ajiye waya kana yaci gaba da aikinsa.
Zaune suke a saman royal bed ɗinsu, kowacce da abinda take saƙawa, Fateemah tace "anya ba zamu koma gidan Granny da zama ba kuwa?"
Diyana ta zaro idanu waje kafin tace "wlhi Dady da Abba bazasu yarda ba, Hmm an gaya miki yah Muzaffar zai amince ne?"
Fateemah tace "gaskiya tsananinsa yayi yawa, idan da shine yah Jawad wlhi da mun huta"
Nan dai sukai ta tufka da warwara suna sharawar komawa gidan Granny sai dai suna ganin abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa,
Cikin Nutsuwa Resh ta shiga wanka ta fito, kana ta mayar da kayan da ta cire ɗazu sannan ta saka zumbulelen hijabinta ta fito bayan ta ɗauki bag ɗinta, daga nan gidan anty Zubaida ta wuce, mai mashin ya sauketa a bakin get, tayi nocking mai gadi ya buɗe mata ta gaishesa kana ta shige ciki, a parlor ta tarar da anty Zubaida tana zaune hannunta na riƙe da cikinta sai cije lips takeyi, Resh ta ƙarasa da sauri ta riƙeta cikin raunatacciyar murya tace "anty Zubaida lafiya, meke faruwa cikinne?"
Ta gyaɗa mata kai tana ci gaba da juyi, Resh ta ɗauki wayar anty Zubaida ta shiga WhatsApp ko zata samesa online, cikin sa'a ta samu yana online tayi masa voice da cewa "anty Zubaida babu lafiya"
Shima voice ɗin ya fara yi mata, cikin kiɗimewa yace "Subhanallah kin tafi hospital ne?"
Resh tace "yanzu na shigo wlhi na sameta a cikin wanan halin"
Yace "su wuce hospital sannan zai yi magana da Ammi da Abbey akan Resh ɗin ta dawo nan gidan da zama har zuwa lokacin da Anty Zubaida zata samu lafiya"
Ita kanta Resh ɗin taji daɗin maganar da yayi, sai dai bata nunar masa ba ta katse kiran, taimakawa anty Zubaida tayi suka fito compound ta fara ƙwalawa driver kira, ya taho da sauri, Resh tace "ka buɗe mana mota hospital zamu tafi"
Da gudu driver yaje ya buɗe mota, ta riƙe anty Zubaida ta shiga sannan itama ta shiga driver yayiwa motar key suka wuce.
Suna isa hospital, bayan Resh tayi musu bayanin da anty Zubaida tayi mata aka turasu scanning, daga nan suka fito jiran sakamako, bayan sakamakon ya fito aka haɗa mata magunguna suka dawo gida, anty Zubaida ta wuce bedroom ɗinta resh CE kawai a parlor tana kallo bayan ta kammala aiyukanta, ta kunna datar wayarta ta hau online, first abinda ta fara dubawa shine group ɗinsu na Classic Lady's, saƙonni ta gani rubutu dan haka ta fara bin ko wanne tana mayar da amsa, ƙawayenta na ganinta online kowa ya fara turo Emojis na farinciki, itama ta tura musu, wata daga ciki tace "wai ya labarin makaranta ne, nifa rabona da zuwa tun kafin insan daɗin dake a cikin cin gindi"
Resh tayi reply da emoji na zare ido, tayi typing tace "a uzubillahi" kedai bakya jin kunya a rayuwarki...?
Wai da kunji Resh CE take salati😂
Cigaban nakuɗi ne complete document 1500 account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank shaidar biya ta wannan number 08141799224
