Ina jin kunyar shiga mutane saboda manyan nonuwana

ji kunyar shiga mutane saboda manyan nonuwana'

“Nakan riƙa tafiya kafaɗa ta a ɗage don in nuna cewa ina da manyan nonuwa. Amma yanzu idan na tuna haka, kunya kan kama ni.”

A shekarar 2010, wata farfesa a ƙasar Argentina ta yanke shawarar yin aikin rage girman nonuwanta. Yanzu da take da shekaru 52, ta ce wannan aiki ya ba ta wani irin ‘yanci da ba ta taɓa ji ba a baya.

Duk da cewa a wasu sassan duniya ana ganin manyan nonuwa a matsayin abin jan hankali, a zahiri suna iya zama barazana ga lafiyar mata da ingancin rayuwarsu. Sau da yawa suna janyo ciwon baya, ciwon wuya, ciwon kai, karkatar jiki, rashin jin daɗi, matsalar bacci, har ma da damuwa ta tunani.

Bisa sabon rahoto daga ƙungiyar masu aikin kwaskwarimar jiki, an yi wa mata 652,676 aikin rage nono a shekarar 2024. Brazil ce ke kan gaba da 115,647, sai Amurka da 67,478, Faransa 38,780, Jamus 32,068, Turkiyya 25,334, da Indiya 22,400.

A Argentina kuwa, ana ɗaukar masu manyan nonuwa a matsayin masu albarka.

“Mutane da dama, musamman mata, kan ce min na yi babbar sa’a,” in ji Raquel.

“Amma gaskiya na sha wahala tun ina budurwa, har zuwa lokacin da na zama uwa.”

Ta ce ta daɗe tana fama da ciwon baya saboda yadda take ƙoƙarin ɓoye jikinta da tafiya a lanƙwashe.

ji kunyar shiga mutane saboda manyan nonuwana'


Raquel na son yin yoga da motsa jiki, amma girman nonuwanta ya hana ta jin daɗin hakan.

Dakta Nora Nugent, shugabar ƙungiyar masu kwaskwarimar jiki a Birtaniya, ta ce yawancin matan da ke zuwa wajenta suna korafi kan wahalar motsa jiki.

“Manyan nonuwa na da nauyi sosai. Suna iya jawo ciwon baya da na wuya, kuma su hana mace sakewa yayin motsa jiki,” in ji ta.

“Haka kuma yana da wahala a samu rigar mama mai dacewa.”

Raquel ta ce tana saka rigar mama biyu ko uku lokaci guda domin samun tallafi. Kuma rigunan mama masu dacewa da manyan nonuwa na da tsada sosai a ƙasarta.

A yayin aikin da aka yi mata, likitoci sun cire kilogram 2.5 daga nonuwanta.

“Bayan aikin, na tuna lokacin da na tsuguna don ɗaukar abu. Na ji wani irin sauƙi da natsuwa a jikina. Na ji kamar an sauke mini nauyi.”

Muhimmancin Rigar Mama Mai Dacewa

Farfesa Joanna Wakefield-Scurr ta fara bincike kan lafiyar nono ne bayan da aka ba ta shawarar ta nemi rigar mama mai kyau domin rage radadin da take ji.

Ta gano cewa mutane da yawa ba su fahimci muhimmancin rigar mama ba.

“Mutane suna kallon rigar mama a matsayin kayan ado ne kawai, ba kayan lafiya ba. Wannan abin takaici ne,” in ji ta.

A shekarar 2005, ta kafa ƙungiyar bincike kan lafiyar nono a Jami’ar Portsmouth. Tawagarta ta gano cewa saka rigar mama da ba ta dace ba na iya janyo zafi, lalacewar fata, matsalar numfashi, da sauyin bugun zuciya.

“Idan nono yana yawan motsi yayin tafiya ko gudu, hakan na shafar numfashi da yadda jiki ke aiki gaba ɗaya,” in ji ta.

Bincikensu ya nuna cewa nono na motsi ta hanyoyi takwas daban-daban yayin motsa jiki. Sun kuma gano cewa tafiya a hankali da samun rigar mama mai kyau na rage zafi fiye da yadda mutane ke zato.

A yanzu, tawagar na aiki da manyan ‘yan wasa mata, ciki har da tawagar Ingila, domin samar musu da kayan da suka dace da lafiyarsu.

Fahimtar Jama’a da Rayuwa Mai Inganci

Raquel ta ce bayan aikin, ta fuskanci rashin fahimta daga wasu mutane.

“Wasu suna kallon aikin a matsayin na kwalliya, ba na lafiya ba,” in ji ta.

“Wata ma ta taɓa ce min, ‘Ya kamata ki je ki rage ciki ma.’”

Duk da haka, ba ta yi nadama ba.

“Yanzu ina cikin farin ciki. Bayan na daina al’ada, ban san yadda zan yi rayuwa da manyan nonuwa ba. Ba zan iya ɗaukar wancan nauyi ba kuma.”

Dakta Nugent ta ce ƙaruwa da ake samu na mata masu neman rage nono na nuna cewa mutane sun fara ba lafiyarsu muhimmanci.

“A yanzu mutane da yawa suna son su rayu cikin ƙoshin lafiya, ba mata kaɗai ba,” in ji ta.

Source: BBC

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post