HUKUNCIN AZUMIN WANDA BAYA SALLAH:
(1)
Wanda baya sallah ba'a karɓar aikinsa na azumi ko zakkah ko hajji, ko duk wani aiki.
Imamul bukhari yaruwaito hadisi (520) daka buraida yace: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:( Duk wanda yabar sallar la'asar hakika ya rusa aikinsa). Ma'anar ya ɓata aikinsa shine yarushe, bazai amfaneshi ba, wannan hadisi yanuna wanda baya sallah ba'a karɓar aikinsa, wanda baya sallah bazai amfana dakomai na aikinsa ba, aikinsa baza'a kaishi zuwa ga Allah ba.
Ibnul qayyeem rahimahullah yace: dangane da ma'anar wannan hadisin acikin littafinsa Assalah (65) " Abunda ya bayyana acikin hadisin, barin sallar iri biyune, barin sallah na har abada shi kwata kwata bayayi wannan yana ɓata aikinsa gaba ɗaya, da kuma barinta na wani lokaci kamar wuni guda sananne wannan yana ɓata aikinsa na iya wannan yinin, Barin sallah gaba ɗaya shike lalata aikinsa gaba ɗaya, barinta na wata rana yana ɓata aikin wannan ranar ko ranakun dabaya sallar
(2)
An tambayi shaik usaimin acikin fatawarsa (87) game da hukuncin azumin wanda baya sallah. Saiya amsa; Wanda baya sallah azuminsa ba ingantacce bane ba karɓabbe bane, domin wanda baya sallah kafirine wanda yayi ridda saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki a Suratul Tauba aya ta 11:
فَإِنْ تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ ۗ
Idan sun tuba sun tsaida sallah sun bada zakkah to sun zama 'yan'uwanku a'addini.
Da faɗin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ( Banbanci dake tsakanin musulmi dawanda bashiba shine yin sallah wanda yabar sallah hakika ya kafirta) Turmuzi ( 2621) Albani ya ingantashi acikin sahihu turmuzi.
Saboda kuma shine maganar sahabbai gaba ɗayan imma baizama ijma'insu akaiba, Abdullahi bin shaqeeq rahimahullah yana cikin tabi'ai waɗanda suka shahara yace: Sahabbai sunkace basa ganin wani aiki cikin ayyuka wanda barinsa kafircine inba sallah ba, abisa wannan idan mutum yayi azumi kuma baya sallah to azuminsa anmayar masa baza'a karɓa masaba, kuma bazai amfaneshiba ranar alkiyama, zamuce dashi yi sallah sannan kayi azumi, amma kai azumi baka sallah azuminka ba karɓabbe bane za'a mayar maka saboda kafiri ba'a karɓar duk wata ibada tasa.
(3)
An tambayi malaman lajnatul da'imah ( 10/140) tambaya kamar haka: idan mutum yakanyi kwaɗayin yin azumi kuma yana sallah da azumi amma kuma dazarar azumi yawuce shikenan yadena sallah, shin yana da azumi? Sai suka amsa: sallah rukunice daga cikin rukunan musulunci muhimmai wanda daka kalmar shahada sai ita, tana cikin farillai na tilas wajibi, duk wanda yabar sallah yana maikore wajabcinta ko kuma saboda wulakantata ko saboda kasala hakika yakafirta, amma masu azumi suna sallah acikin azumi kawai waɗannan suna yaudarar Allah ne, tir da mutanen dabasu san Allah ba sai awatan Ramadan, azuminsu bai ingantaba tare dabarin sallarsu alokacinda ba na azumi ba, sudin kafiraine kafirci babba, koda basu kore wajabcin sallar ba amafi inganci maganganun malamai.
WALLAHU A'ALAM.
