A Cikin Rayuwa Page 3 Complete

A Cikin Rayuwa Page 3 Complete

 _Bossladieswriters_

  *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* 

    _By Zainab Bature_

Page 3

.......Bayan sun shiga cikin bedroom ɗin Deen wanda shima babba ne, sam ɗakin baida hayaniya amman ya tsaru da tsadaddun furniture, tun daga kan yadda aka tsara ɗakin zuwa kayan dake ciki irin na turawa ne, akwai tafka tafkan glass windows a wurare daban daban na bangon ɗakin, girman windunan in mutum ya tsaya a jiki za a iya hango kusan gaba ɗaya jikinsa, a jikin windunan akwai labulaye masu kyau da inganci kalar ruwan madara, sauran kayan cikin ɗakin ma duk kalar ruwan madara ne, akwai gado king-size bed with stylish high-end bed frame with built-in headboard, sai bedside drawers a saman su haɗaɗɗun fitilu ne, akwai tebur ɗin gaban gado ɗunɗumeme, daga ƙasa wani irin lallausan carpet ne mai gwa6i yana da gashi-gashi masu ɗan tsawo shima kalar ruwan madara, can ɗan gaba da gadon akwai lounge chair daga bayanta akwai tafkekiyar window wadda kana zaune a kan kujerar wurin kana hango waje,  akwai dressing table da kujerar shi can gefe ɗaya, sai walk-in closet da ke acan cikin ɗakin, yadda aka tsara closet ɗin wurin ya yi kamar wurin sayar da kaya wato boutique, banda wurin kayan sakawa akwai wuraren ajiye takalma, daga tsakiyar closet din akwai dresser da chest of drawers a ciki su agoguna ne da sauran kayan gayun maza.


 A saman kujerar zama dake gaban gadon suka zauna, kowa ya yi shiru fuskar Deen tattare da damuwa yake kallon Fahad da ya jingina bayansa jikin kujerar ya ɗan ɗage kai yana kallon gefe guda, a hankali Deen ya kai hannunsa ya ɗaura a saman hannun Fahad ɗin dake ajiye saman cinyarsa, juyo da fuskarsa ya yi ya kalli Deen,


 "I'm sorry Yaya Fahad.." Deen ya faɗa fuskarsa tattare da damuwa, ɗan murmushi Fahad ya yi masa kawai, 


"I don't know why mom is acting so inappropriately...." Ya faɗa looking worried, shiru Fahad ya yi tare da kauda idanunsa gefe, kasancewar shi mai zuciya ba tun yanzu ba abubuwan da mahaifiyarsu Deen ke yi ma danginsu ke ci masa tuwo a ƙwarya, ba don karfin zumuncin dake tsakaninsu da ƴan'uwansu ba da tuni sai ta fuskanci 6acin ransa kan abubuwan da take yi, duk irin yadda suke janye jiki da gidan gudun wulaƙancinta hakan bai sa  sun tsira ba, da alama so take kwata-kwata su daina zuwa gidan wanda hakan abu ne kuma da ba zai yuwu ba, suna ƙaunar junansu shi da sauran ƴan'uwansa, musamman Deen da Fahad akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu tun tasowar su,  mahaifin Deen ya so Fahad ya zauna gidan tare da su  saboda ganin yadda suke ƙaunar juna, saidai mahaifiyarsa firr ta ƙi amincewa ta nuna bata son ya zauna a gidan, a nan gidan Fahad ya yi karatunsa na secondary cike da ƙyara da kuma hantara daga wurin mom, idan dad baya a gidan haka zata mayar da shi kamar wani yaron gida, shine gyaran gida da su aike duk da a lokacin Deen ba wani girma ne da shi ba, yana nuna mata rashin jin daɗin hakan da take yi amman hakan bai sakawa ta bari, ya sha cewa sai ya faɗi ma Dad abubuwan da take masa amman Fahad ke hana shi ya ce masa in har ya faɗi ma dad to za su 6ata kuma zai tafi ya bar gidan, hakan yasa Deen bai ta6a sanar ma dad ɗin nasu ba, duk da a lokacin shima dad din yana ɗan fahimtar ƙuntatawar da take ma Fahad ɗin, sai dai ko ya yi mata magana sai ta nuna ita mi take yi masa kuma tun da matsayin uwa take a wurin sa ba dole ta rinƙa tsawatar masa ba kan abun da ba daidai ba, kawai dai dad na yin shiru ne don ba wani katabus zai iya yi ba kan hakan amman ya san tana takura masa, hatta iyayen Fahad a lokacin sun fahimci zaman takura yake a gidan ba kamar da suka san halin mom ɗin su Deen na rashin mutunci, saidai ko an tambaye shi  kan irin zaman da yake yi idan ya je hutu gidansu sai ya nuna masu lafiya lau yake zaune, a lokacin bai son su san halin da yake ciki ne ba don komai ba sai don ka da su raba shi da Deen sanin ba zai jure hakan ba, wani lokacin idan ta kai Fahad ɗin bango ya gaya mata magana da yake yana da zuciya har bugunsa take. Lokacin da Deen ya gama ƙaramar secondary ne ta matsa kan tana son ta maida shi London wurin ƙanwarta ya ƙarasa karatunsa a can, ba don komai ta yi hakan ba sai don ta raba shi da Fahad wanda a lokacin shi ya kammala karatunsa na Secondary, jin haka yasa dad ɗin Deen ya ce su tafi tare da Fahad sai shima ya ci gaba da karatun nasa a can, aikuwa ta hau sama ta dire kan sam hakan ba zai yuwu ba ya koma gidansu shima mahaifinsa ya nema mashi makarantar da zai ci gaba, lokacin ya so ya kafe kan ra'ayinsa amman sai ta fake da nuna mashi abun zai yi yawa a ce sun je can har su biyu sun zauna a wurin su, ya nuna mata ai ba dole sai su duka sun zauna ba sai shi Fahad ya zauna a makaranta amma ta dage kan ya san dai irin shaƙuwar da suka yi ba yadda za ai suna a ƙasa ɗaya su zauna a wuri daban-daban. Ƙarshe dai sai da ta yi nasarar yadda ta sa shi janye ra'ayin kai Fahad can. Deen ya sha kuka lokacin da za su rabu da Fahad, tare da daddynsu suka raka shi Funtua da zai koma, a can ma ganin yadda Deen ya shiga damuwa kakarsu Hajiyar Ambasada sai da ta ce ma Alhaji Ibrahim mi zai hana a tura su tare da Fahad din amman sai shima ya fake da faɗi mata irin abun da mom ɗin su Deen ta faɗa, a lokacin ta fahimci matarsa ce bata son hakan, da yake ita ba mai shiga ta yi karan tsaye cikin al'amuran ƴaƴanta ba ce, tsakaninta da matayen su sai in abu ya wuce gona da iri take shiga hakan ya sa ta ƙyale su, ƙarshe Deen yana ji yana gani aka raba shi da yayansa da yake matuƙar ƙauna a cikin zuciyarsa suka koma Abuja ba tare da shi ba. Bayan tafiyar Deen London shima Fahad mahaifinsa ya nema masa makaranta a ƙasar Malaysia ya tafi yin karatun likitanci. Duk da sun yi nesa da juna hakan bai sa sun daina zumunci ba, suna ziyartar juna duk suka samu hutu, ba kamar Deen da yake ɗan gatan Maleek ne ba ƙaramin ji yake da shi ba saboda bai da ɗa namiji, duk abun da yake so yana masa hakan yasa duk lokacin da ya nuna yana son zuwa Malaysia wurin Fahad sai ya samu lokaci ya kai shi da kansa, dama kuma akwai kamfanonin da yake yin hulɗar kasuwanci da su a can, hakan ma sai da mom ɗin Deen ta yi ƙoƙarin hana ziyartar junan da suke yi ta hanyar yi ma Maleek magana kan ya daina biye ma Deen, ta ce ko ya ce yana son zuwa wurin Fahad ya daina kai shi, sai dai bata yi nasara ba don Maleek ɗin nuna mata ya yi ai hakan ba wani abu bane kuma abun da suke yi yana da kyau ƙarfafa zumunci ne, da bata yi nasara ta bangaren sa ba sai ta koma kan wadda take da iko da ita wato matarsa ƙanwarta Safna, tsawatar mata ta yi a kan ta hana Maleek kai Deen da yake yi wurin Fahad, a lokacin Safna ta nuna mata zata yi hakan, amman da yake itama tana tsananin son Deen duk abun da yake so tana yi masa bata hana ɗin ba, ƙarshe dai dole mom ɗin ta kyale su ta ƙarata da baƙin cikin hakan.



 Juyowa Fahad ya yi ya kalli Deen da har lokacin 6acin rai ke kwance akan fuskarsa, dafa kafaɗarsa ya yi cikin kwantar da murya ya ce, "You shouldn't worry yourself about dat, hakan na faruwa, wasu mutane suna yin abun da ake ganin ba daidai ba, su kuma a wurin su basu ganin hakan a ba daidai ba, so hakan ya daina damun ka." Ɗan yamutsa fuska Deen ya yi, "Amman ita mom ta san abun da take yi ba daidai bane tun da ba kowa take ma hakan ba. Tun ba yanzu ba Ya Fahad bana jin daɗin the way take treating duk dangin daddy, kaman sun mata wani abu?" Ya ƙare fuskarsa a yamutse, ɗan murmushi da ya fi kama da na takaici Fahad ya yi jin har yaranta sun san tana yi ma danginsu ba daidai ba, ƴar ajiyar zuciya Fahad ya sauke, 


"Zai iya yuwuwa akwai abun da ya faru da ya sa hakan ke faruwa." Fahad ya faɗa ba don yana zaton hakan bane ya dai ce ne kawai. Duk da yana yaro sosai aka aurota bai tunanin akwai abun da ya ta6a faruwa tsakaninta da danginsu da har ya haifar da hakan, dama can tun da ya taso yake jin ana ƙorafi game da halinta.


  

"Ya Club ɗin na ku, wani wasa zaku buga in ka koma?"



Da murmushi Deen ya faɗi masa ya ce, "Ko ka zama football fan ne? Da fa kana son ƙwallo sosai, ka tuna lokacin da muke yi a cikin compound kai ta fyaɗa ni da ƙasa, in kafe sai na rama ƙarshe da kuka muke gamawa ka dawo kana rarrashi na" Ya ƙarasa yana sakin faffaɗan murmushi, dariya Fahad ɗin ya yi tunowa da lokacin, gyara zama ya yi ta yadda ya ɗan zamo jikinsa ya kwanta kansa a jikin kujerar,


   

"Yanzu ma ina ɗan kallon wasu match ba sosai ba, amman duk wasan ku ina kallo." Kai Deen ya jinjina, ya yarda da abun da ya faɗa don duk suka yi wasa suka yi nasara sai ya taya shi murna ta chat ko kiran waya, koda basu yi nasara ba sai ya yaba masa tare da ƙara ƙarfafa masa gwuiwa.


   "Yanzu na fi kallon boxing sosai." Fahad ya faɗa yana ɗan shafa sajensa, 


  "Ka ce ka fi son kallon mugunta, Allah Ya sa ba kana koya bane watarana ka karya ma wani jaw." Dariya sosai Fahad ɗin ya yi, 


 

 "Wani lokaci ne dinner da ka ce?" Fahad ya tambaya yana kallonsa, faɗi masa lokacin ya yi tare da venue kafin Deen ya ce masa yana zuwa ya nufi cikin ɗakin, walk in closet dinsa ya shiga, bada jimawa ba ya fito hannunsa ɗaya jaye da suitcase kalar ruwan ƙasa da wata yar babbar jaka a ɗayan hannun masu kyaun gaske, gadon shi da ya sha gyara an shimfiɗa zanen gado mai kyau sai duvet mai laushin tsiya da aka rufe rabin gadon da shi gaba ɗayan su kalar kayan ɗakin ne suma wato ruwan madara, ɗaura akwatin ya yi saman gadon ya haye sama ya zauna, kallon Fahad ya yi ya ce masa ya zo ya gani, a nutse ya taso yana gyara rigarsa ya nufo shi, a ɗayan bangaren gadon ya zauna ta yadda sun saka akwatin tsakiya, buɗe akwatin ya yi wanda kayan sakawa ne cike a ciki, daddaɗan ƙamshi haɗi da na sabuntar kaya ne ya gauraye wurin, a tsanake yake fiddo da kayan yana nuna masa yana ajiyewa a gefe, bayan ya gama fiddo da kayan ɗayar jakar ya jawo itama ya buɗe ta, a ciki takalma ne ƴan ubansu tsadaddun gaske, akwai agoguna da turarurruka harda kayan shan iska da underwear na maza, bayan duk ya gama fiddo su ya kalli Fahad ya ce gasu nan nashi ne ya san duk za su yi masa tunda ya san size ɗin sa duk da ya ga kaman ya ɗan ƙara jiki ko ya daina motsa jiki ne, da murmushi Fahad ɗin ya ce masa yana yi, da zolaya Deen ya ce to cinye ma mommy abinci yake yi ke nan tun da ya ƙi ya yi aure, ƴar dariya Fahad ya yi kafin ya mayar da idanunsa kan kayan dake jibge a saman gadon ƙirar manyan kamfuna, ko ba a faɗa ba ya san kaya ne masu tsadar gaske, kallon Deen ya yi ya ce, "Miyasa zaka kashe kuɗi haka, kayan sun yi yawa ai." Shima yana murmushi ya bashi amsa, 


"Ina da kuɗin ne, ko da bani da su zan nema don in siya maka." Ɗan faffaɗan murmushin jin daɗin maganarsa Fahad ya yi, har da irin hakan ke ƙara masu ƙaunar juna, shima Fahad ɗin ya na yi ma Deen alkhairi duk da ya san ya fi shi kudi sosai, ko lokacin da ya fara amsar albashinsa na farko sai da ya tura ma Deen wani kaso a ciki kuma Deen ya ji daɗin hakan. Hira suka ci gaba da yi zaune saman gadon gwanin burgewa, kana kallon su ka ga zaratan maza waɗanda hutu ya zauna a jikinsu.




Leemah na barin part ɗin Deen ƙasa ta sauka ta nufi ɗakinta ta shige, ɗakin ba laifi yana da ɗan girma akwai simple modern furniture, komai na cikin ɗakin kalar ruwan toka ne, kana ganin ɗakin kasan na ɗiyar masu hannu da shuni ne don harda tv stand kalar setin kayan dakin manne da madaidaiciyar plasma suna fuskantar gadon ɗakin. Kai tsaye toilet ta nufa don ta yi wanka bayan ta rage kayan jikinta, ba da jimawa ba ta fito ƙirjinta ɗaure da tawul da ya kawo mata tsakiyar cinyoyinta da suka bayyana jajur da su ko ɗan tabo babu, ba tare da 6ata lokaci ba ta hau shirya kanta. Bayan ta gama yin shafe-shafe ta gyara gashinta da yake da tsawo ga santsi, wurin ƙatuwar wardrobe ɗinta dake a jikin bango ta nufa don ta ɗauko kayan da zata saka, saida ta yi ruwan ido wurin zabar kayan da zata saka don kaya ne ciki gasu nan birjik iri- iri, ƙarshe wani baƙin lace mai adon fulawowi peach da ratsin golden ta dauko, kana ganin leshin ba sai ma an faɗi maka zai yi kuɗi ba yadda aikin jikinsa ya saƙu sosai, bayan ta saka kayan wanda fitted gown ce da ta kama jikinta daga ƙasa ta buɗe haka hannun rigar ma dogo ne daga ƙasan shi ya ɗan bude an yi ado da bakin leshin, wuyan rigar irin mai zagayayyar kwala ne, ta matuƙar yin kyau kayan sun amshi jikinta ta fito a ƴar matashiyar budurwa, duk da bata ida zama babbar budurwa ba alamun tana da diri mai kyau ya bayyana, dama jikin momynta ta biyo duk da a fuskarta akwai ɗan yanayin daddynsu amman ta fi kama da momynsu sosai, tana da tsawo sannan bata da jiki amman kuma ba siririya bace, daga yanayin jikinta akwai alamun da ta ƙara girma ko ta yi aure zata iya ƙara jiki, gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta fuskarta ɗauke da murmushi ganin yadda rigar ta amshi jikinta, dama kayan sababbi ne bata ta6a saka su ba suna cikin kayan da aka yi masu saboda zuwan yayan su Deen, ko ƙananun kayan da suka je tarbar sa da su suma sababbi ne gal yau suka fara saka su, ɗan jujjuyawa ta yi ta kai hannu tana shafa hips ɗinta, ta ji daɗin ganin yadda suka fito, kai idonta ta yi kan ƙirjinta da suma sun fito ɗas duk da har da ƙarin bra da ta saka yasa suka cika, kallabin kayan ta shiga ɗaurawa bayan ta ɗaure gashinta da ribbom jelar ta sauka har wuce saitin kafaɗarta, tana cikin yin ɗaurin ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, ta cikin madubin ta kai idonta wurin ƙofar, har sai da gabanta ya ɗan faɗi ganin mom ɗin su ce ta shigo, 


Idonta akan Leemah dake ci gaba da yin ɗaurin kallabinta ta nufo cikin ɗakin, gefenta ta tsaya tana bin ta da kallo mai cike da mamaki, sai da ta kammala yin ɗaurin sannan ta juyo ta kalli mom ɗin na su da murmushin ƙarfin hali kan fuskarta ta furta, "Mom na yi kyau ko?" Bata amsa mata ba da alamun mamaki ta ce, "To wannan ɗin na minene?" Ta yi maganar tana nuna ta daga ƙasa har sama, ɗan tura bakinta da ya sha dark peach din jambaki ta yi da yanayin shagwa6a ta ce kwalliya ce kawai ta yi, wata uwar harara ta wurga mata da alamun 6acin rai ta ce, "Ke nan wanccan mutumin ki kai ma kwalliyan?" Bata rai Leemah ta yi, "Mom ni fa kawai na yi kwalliyana ne, kuma ai ba yau na fara yi ba ko." 


Bin ta da kallo mom ta yi sheƙeƙe, fuska a yamutse ta ce, "Eh ba yau kika saba yin kwalliya ba, amman ba irin wadda kika saba yi ɗin ba ce ai kika yi. Wato dai zargin da nike yi a kan ki Leemah ya zama gaskiya ko! Idan ba akwai wani abu tsakanin ki da wanccan yaron ba uban miye to na yin kwalliya haka? Ko yayanki da ya ɗau tsawon lokaci bai zo ba sai yau baki yi irin wannan kwalliyar ba don tarbar sa, soyayya kike da Fahad ko!" Ta tambaya cikin kwatsa tsawa, tura baki Leemah ta yi rai 6ace ta ce, "Wai mom sau nawa zan ce maki ni ba soyayya muke yi da shi ba, kuma in ma soyayyar muke yi ai ba haramun bane tun da akwai aure a tsakanin mu..." Uwar tsawa ta daka mata ta ce, "Kar ma ki fara wannan tunanin wllh! In ma soyayya kuke yi to tun wuri ki datse ta idan ba haka ba zan datse ta da kai na, matuƙar ina numfashi ba zan bari hakan ya faru ba wllh, ai zaren bai yi daidai da kalar yadin ba, bai kai matsayin da zai iya auren ki ba!" Ta ƙarasa tana ɗan jujjuya kanta ta ƙanƙance idanunta, cikin ƙuna-ƙuni Leemah ta ce, "In haka ne, to ai kema mom ke da daddy zaren bai yi daidai da kalan yadin ba ko kuma ya aure ki, kuma ai ya Fahad bai da wani aibu yana da kyau kuma yana da aiki mai kyau sannan danginsu masu arziƙi ne, ke kuma ai dangin ku ba masu kuɗi bane amman a hakan suka amince dad ya aure ki, sai ke kuma zaki ce ba za ki amince ma wani nasu ya auri ɗiyar ki ba." Tana maganar tana ɗan ja da baya, da alama ta kashe bakin mom ɗin nasu, tsananin al'ajabin abun da Leemah ta faɗa ne bayyane akan fuskarta, 


Cikin murya mai kaushi ta furta, "Leemah ni kike faɗi ma wannan maganar!" Ta faɗa tare da nuna kanta da yatsa,


 "To ai gaskiya na faɗa ko mom, ba ta inda na fi ƙarfin ya Fahad, in ma don kina ganin daddynmu mai kuɗi ne shima ai daddynsa yana da kuɗi, ko da don kina tunanin dad ya fi abbansu kuɗi ne kin manta da cewa dad ɗin namu ƙanin mahaifinsu ne?" Wani kallon takaici mom take bin ta da shi ta yamutsa baki, Leemah na kikkafta idanu ta ƙara cewa, "In dai ina son shi shima yana sona sai mun auri jun...." Da sauri ta goce ma marin da mom ta kawo mata, tana huci ta furta, "To don ubanki, ko shi ɗanɗan ƙaruna ne baza ki aure shi ba don ba ɗan shaye-shaye na haifa ma ke ba! Sannan ko wadda take iko da ubanki bata isa ta sa ya aure ki ba balle shi uban naki! Gara ki dawo cikin hayyacin ki tun wuri." Tana ƙarasa maganar ta juya ta nufi barin ɗakin, ta san Leemah ba kunya ta ishe ta ba, in ta biye mata haka zatai ta saka ta hargowa tana ƙara ƙunsa mata bacin rai, 


  "In har Allah Ya ƙaddara shi mijina ne sai na aure shi, ba wanda zai iya hana hakan." Ta faɗa cikin tura baki, lokacin mom ta kama ƙofa zata fita ta tsinkayi muryar Leemah, juyowa tayi cikin sakin shu'umin murmushi ta furta, "We shall seee..." Daga haka ta fuce tare da rufe ƙofar da ƙarfi ta bada sauti.


 Bakin gado ta nufa ta zauna dabas fuskarta a jagule kamar zata sa kuka, sam bata ji komai ba da mom ta kira Fahad da ɗan shaye-shaye, ba tun yau ba tana jin hakan saidai ita bata ta6a ganinsa ba yana shan wani abu da ya danganci haka, takaicinta ita ba ma soyayyar suke da shi ba, kawai dai tana jin wani abu a ranta game da shi wanda ta san son shi take amman shi bai ma san halin da take ciki ba. Gaba ɗaya mom ta lalata yanayin farin cikin da take aciki, ji take kamar ma ta cire kayan ta fasa fita, sai dai son ta yi hakan ya rinjaya a cikin zuciyarta. Ta ɗan ɗauki lokaci zaune tana ta ƙunci kafin daga bisani ta miƙe ta koma gaban madubin ta ɗan ƙara gyara fuskarta bayan ta gama ta ciro takalma flat kalar peach ta zura kafafunta ta nufi hanyar fita.



Kiran dad da ya shigo wayar Deen ya sanar da su cewa lokacin sallar la'asar ya yi su fito su tafi masallaci ya tashe su daga hirar da suke yi. Bayan sun dawo suna shigowa falo Deen ya ce ma Fahad su je dining room ya ci abinci, suna zuwa tsakiyar falon Leemah dake zaune tana jiran dawowar su ta nufo su, ganinta ya sa su tsayawa ta ƙaraso gaban su da ɗan murmushi ta yi masu sannu da dawowa, fuskar kowannan su da murmushi suka amsa mata. 


"Leemah, an zama ƴan mata." Deen ya faɗa da murmushi, hannuwanta ta sa ta rufe fuska alamar kunya, buɗe fuskar ta yi suka haɗa ido da Fahad dake ɗan yin murmushi,


   "Ya Fahad mu je ka ci abinci gashi can na kai maka dining, tun da ka zo baka ci komai ba." Ta faɗa tana ɗan rausayar da kai. 


"Good, dat's why i love u Leemah, kina da hankali da sanin yakamata." Deen ya faɗa, 


  

 "Amman ɗazun dad cewa ya yi wai wani lokacin nike da hankalin." Ta tura baki, da alama bata ji daɗin maganar ba, kuma ba don komai ba sai don an faɗi hakan a gaban Fahad, satar kallon shi ta yi suka haɗa ido. 


"Suna maki wasa ne ai." 


Fahad ne ya faɗa idonsa a kanta, ɗan murmushi ta yi ko ba komai ta ji daɗi da ya ɗauka wasa suke, Deen dake ta kallon su yana ɗan murmushi don ya so ya fahimci wani abu, ya ce ma Fahad su je Leemah ta yi serving na shi zai je part ɗinsa ya ɗauko wayansa ya san yana

 da tarin saƙonni, kuma yana son yin magana da manager ɗinsa, nufar dining room suka yi suna tafiya a jere shi da ita yayin da Deen ya nufi upstairs jikinsa sanye da farar jallabiyar da ya saka da za su je masallaci ya yi kaman balarabe...

*Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268*

Post a Comment

We welcome your thoughts! Please keep comments respectful, relevant, and free from hate speech, spam, or false information. Offensive or promotional content will be removed, and repeat offenders may be banned. By commenting, you agree to follow our Community Guidelines.

Previous Post Next Post