Boss ladies writer
✨A CIKIN RAYUWA✨
Dedication
Ga duk wanda ya taɓa fuskantar zafi amma har yanzu yana murmushi.
To everyone who has loved deeply and lost painfully,
ga duk wanda ya faɗi, amma hakan bai hana sa tashi ba, this story is for you.
A cikin rayuwa, kowace ƙaddara tana da dalili, every tear carries a hidden lesson, and even in the darkest nights, there’s always a light waiting to shine again.
May this story remind you that nothing in life is wasted, duk abinda Allah Ya bari ya faru, has a meaning that only time can explain.
Zainab Bature (Zeelaluh)
Page 2
.....Lokacin da motocinsu suka ƙaraso bakin katafaren gate ɗin gidan Alhaji Ibrahim Nuraddeen dake a maitama, tun a bakin gate za ka fara sakin baki tsabar haɗuwar sa, bayan jami'an dake a bakin gate sun buɗe masu kai tsaye motocin suka kutsa ciki, al'ajabi ne ya kama ni ganin irin luxurious mansion ɗin tamkar ba a Nigeria ba, fassalta tsaruwar ginin gidan ba ƙaramin aiki bane saidai a ɗan kwatanta, gidan na da girma sosai sannan an tsara shi da shuke-shuken fulawoyi masu matuƙar kyau da tsari, ƙasan gidan kan shi ba irin wanda idanu suka saba gani ba ne, wani irin design aka yi ta yadda wani bangare na ƙasan wani irin abu mai salƙi ne tamkar in ka taka zai kada ka, wani bangaren ƙasan kuma an kawata shi da shukar korayen ciyayi gwanin burgewa, gidan ya ƙawatu matuƙa ta yadda duk wanda ya tsinci kan shi a gidan zai tabbatar da naira ta sha kashi a wurin ƙera gidan. Kai tsaye entryhall din gidan motocin suka nufa a tare suka faka, cikin escort ɗin wasu suka fito tare da nufar motocin da iyalan suke suka bubbuɗe masu ƙofofi, lokacin da Deen ya fito wani irin lumshe ido ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya furta, "Home, sweet home." Ƴar dariya duk suka yi Dad ɗin shi ya dafa kafaɗarsa ya ce ya yi missing ɗin gidan ne, buɗe kyawawan idanunsa ya yi akan Dad din nasa ya furta sosai ma,
"Ba dole ya yi missing gida ba, almost 3 years fa rabon shi da 9ja." Mom ɗinsa ce ta faɗi hakan, nufar hanyar shiga cikin gidan suka yi hannuwansa ruƙe da na Sultan da Batool, wani irin katafaren falo ne da ya gaji da haɗuwa suka shigo, falon ƙarshe ne wurin tsaruwa akwai duk wani abu da za a samu a cikin falon masu kuɗin da suka amsa sunan masu kuɗi, to uba kuɗi ɗa kuma kuɗaɗe ko ban faɗa ba an san dole gidan ya kasance aljannar duniya ne. A ɗaya daga cikin rantsattsun saitin kujerun da ke a katafaren falon suka zauna wanda akwai saitin kujeru daban-daban na gani na faɗa sun kai ukku, bayan babban falon kuma akwai wasu ƙananun faluka a wasu bangarorin cikin gidan, sannan akwai matattakalar benen hawa sama wadda ita kanta yadda ta tsaru abun tsayawa kallo ce, daga bangaren da kayan kallo da na sauti suke akwai hotunan iyalan gidan da na sauran ƴan uwansu musamman masu muhimmanci a gare su, akwai hotunan dad ɗin su da aka yi mashi wasu zaune a majalissa wasu tare da shugaban ƙasa da sauran ƴan majalissa.
Kafin Deen ya zauna saida ya fara cire jacket din jikin shi Leemah da Batool suka cire mashi takalmansa, a saman kujera mai mazaunin mutum ukku suka zauna, Deen ne a tsakiya su Leemah da Sultan suka saka shi tsakiya ya ɗaura Batool a saman kafafunsa, a kujerar gefen shi mai mazaunin mutum ɗaya ƙaninsa mai bi mashi wato Omar ya zauna, daga ɗayan gefen saman kujerar dake fuskantar su mai mazaunin mutum biyu nan mom da dad ɗin su suka zauna,
Gaba ɗaya iyalan cikin farin cikin zuwan Deen ɗin suke saboda daɗewar da ya yi bai zo Nigeria ba, saidai su in sun je can su haɗu, da yake suna yawan zuwa saboda ƙanwar mom da abokin dad dake can. Maganar abinci mom ta yi masa wanda tuni an shirya mashi a dining room, ya ce mata a ƙoshe yake ya ci a cikin jirgi sai dai zuwa anjima, umarnin akawo mashi drink ta bada ta hanyar landline ɗin cikin falon, bada jimawa ba wata ƴar babbar mace ta shigo jikinta sanye da farar apron da hula irin na chef wato masu yin aikin abinci, chef Alima ke nan wadda ƴar dattijuwar bayerabiya ce, ita ce babba a cikin ƴan aikin gidan, bayan ta gaishe da su a nutse cike da taka tsan-tsan gudun masifar uwar ɗakin nata sanin bata raina abun masifa ta ɗaura luxury tray ɗin saman ƙaramin table dake a gefen kujerun, matso da taburin ta yi fuskarta ɗauke da faffaɗan murmushi ta ɗaura idonta kan Deen ta furta, "You are highly welcome sir." Da ɗan murmushi ya jinjina mata kai ya yi mata godiya, ƙokarin zuba mashi lemun ta fara, ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce ta bari ba yanzu zai sha ba in zai sha zai zuba, ɗagowa ta yi har lokacin da murmushi akan fuskarta wanda na farin cikin ganin shi ne domin suma duk suna son shi, idan ana yin ƙwallo da kungiyarsu suna cin albarkaci su zauna tare da iyalin gidan anan cikin babban falo su kalla, duk da a bangarensu na ƴan aiki akwai kayan kallon amman ta fi masu daɗi in suna kallo tare da iyalin, godiya ta yi ma shi kafin ta juya, saida ta tambayi mom ɗin cike da ladabi ko akwai wani abu da zata ƙara yi ta ɗan girgiza mata kai alamar babu sannan ta bar falon, hira suka shiga yi cike da nishaɗi,
"Ya dad da mom ɗin ka na can?" Mahaifinsa ne yake tambayar shi Maleek da Safna,
"They are all doing well, suna gaishe da ku." Ya bashi amsa cikin turancin shi na yan can, hatta hausar shi ma in ya yi zaka ji yanayin sautin kamar turanci,
"How about Basma? Da kun zo tare ai." Mom din shi ta faɗa, yanayin fuskarsa ne ya ɗan sauya ya bata amsa da basu samu hutun school ba,
"Bro amman zaka daɗe ko?" Leemah ce ta tambaya, a taƙaice ya bata amsa da ba zai daɗe ba sosai yana da wasanni da zai buga, kallon Omar ya yi ya tambaye shi ya karatunsa da yake yi a ƙasar Cyprus, amsa mashi ya yi da Alhamdulillah ya kusa komawa, kai Deen ya jinjina, maida idon shi ya yi kan Sultan ya tambaye shi miyasa basu je school ba, Leemah ce ta bashi amsa da saboda suna son su tarbe shi yasa suka ƙi zuwa. Saida Mom ta yi mashi magana kan juice da aka kawo masa sannan Leemah ta zuba mashi ya sha kaɗan, Dad ne ya yi mashi magana kan yakamata ya je ya kwanta ko ya huta gajiya, ya bashi amsa da ba wani gajiya ya yi ba sosai don ya kwanta a cikin jirgi. Suna nan zaune har aka fara kiran sallar azahar, tare da Dad da sauran ƙannansa maza suka tafi masallaci wanda yake a jikin gidan. Ko a masallacin bayan gama salla haka mutane sukai ta zuwa suna gaisawa da shi tare da yabon sa da kuma yi masa fatan alkhairi, wasu ma ba masu kallon ƙwallo bane amman saboda yadda yake burge mutane ya sa suke ta zumuɗin ganin sun gaisa da shi.
Bayan dawowar su daga masallaci suka zauna zaman cin abinci a dining room wanda shima ya tsaru sosai da tsadaddan dining table da kujerun sa guda takwas, akwai kuma wasu set ɗin daban a can bangare ɗaya, abinciccika ne birjik a saman teburin cikin luxury warmers da sauran abubuwan zuba abinci na ƙawa, masu aiki biyu ne a tsaye suke serving na su yayin da suke cin abincin a nutse, gaba ɗaya idanun ƴan aikin na akan Deen yadda yake cin abincin shi cikin aji da jan hankali.
Bayan gama cin abincin gaba dayan su suka taru a bangaren Deen dake a saman bene, bangaren na da girma akwai babban falo da ya ji kujeru leathers sai kayan kallo da kayan sauti, akwai manya-manyan hotuna wanda yawanci duk na shi ne a wurin ƙwallo sai na ƴan gidan su, akwai hoton abokin mahaifinsa wanda yake wurin shi wato Maleek tare da iyalinsa, sam falon baida hayaniya amman kana kallon kayan ciki zaka san masu tsada ne kuma ba gama garin kaya ne ba da zaka iya samu a ko ina, daga wurin bangon da kayan kallo suke wani irin design ɗin gini aka yi na gidajen da za a iya saka abubuwa, a cikin gidajen wasu daga cikin lambobin yabo da kyaututtuka masu daraja ne da ya samu a ciki gwanin burgewa, duk da ba wai iya su kaɗai bane kyaututtakan akwai tarin wasu a gidansa na London.
Zazzaune suke a saman kujerun cikin falon suna ta hira, mom ɗinsu ta canza kaya zuwa doguwar riga navy blue da ta ƙara fiddo da haskenta fayau, Dad din su ma jallabiya ce a jikin shi, su Leemah dai kayan da suka je tarbar shi ne airport ƙananun kaya riga da wando, haka ma Omar da Sultan duk ƙananun kayan ne a jikinsu, shima Deen ya canza kaya zuwa na shan iska riga mara hannuwa da gajeran wandonta da ya kai mashi gwiwa, murɗaɗɗun hannuwansa sun bayyana,
"Bro, mom ta ce nima ina gama secondary school zan koma wurin Aunty Safnah a can zan ci gaba da karatu." Leemah ce ta faɗa tana murmushi.
"When will you be done with secondary school?"
Deen dake kishingiɗe ya tambaya,
"Yanzu ina a S.S 2 going to 3 nan da one year zan gama." Kai ya jinjina kawai.
"Ni ina ganin ba gara ki yi karatunki anan ba, in kika tafi nesa Batool ba za ta ji daɗi ba ita kaɗai ba ƴar'uwa mace."
Dad na rufe baki Mom ɗin su ta ce, "No, can zata tafi saboda Basma ta matsa tana son ta koma can itama ta samu sister, ita Batool ai autan mom ce muna tare ko yaushe ba za ta damu ba." Ta yi maganar idonta a kan Batool dake manne da jikin Deen, ta ɗage mata gira tare da tambayarta ai ba za ta damu ba tana tare da mom ko, kai Batool ta jinjina mata tana murmushi, shiru Daddynsu ya yi ya san kawai ita ke ra'ayin Leemah din ta je can, shi kuma yana tunanin hakan kamar bai kamata ba, ganin Deen na zaune a wurin su duk da yanzu yana da gidan kansa amman ai kusan a wurin su ya taso, kuma har yanzu in dai yana a London a gidan su yake zama, bayan wannan kuma shi bai son Leemah ta kasance tare da Basma su samu kusanci sosai don ya san yarinyar bata jin magana an sangartata da yawa, duk da ya san iyayenta suna ƙoƙari wurin tarbiyarta, sai dai kasancewar ita kaɗai Allah Ya basu ya sa take samun gata sosai.
"Bro Deen, pls gobe ka kaimu school friends dina na ta son su gan ka da na faɗa masu zaka zo, wasu ma sun ce sai sun zo nan gidan sun gan ka ku gaisa." Shiru ya yi idonsa akan Leemah da ta yi maganar yana ɗan murmushi, magiya ta shiga yi masa akan ya kai su, Sultan ma ya ce shima abokansa na son shi sosai kuma suna ta son ganin shi, haɗuwa suka yi suna roƙon shi akan ya kai su makarantar, Leemah har da duƙawa ƙasa a gaban sa, su Dad sai dariya suke masu, amsa masu ya yi da zai duba ko da ba goben ba zai kai su, sallamar da suka ji an yi ce ta saka su kai idanunsu gaba ɗaya kan ƙofar shigowa, wani matashin mutum ne ya shigo, a yanayin halitta dogo ne kusan zasu iya yin kai ɗaya da Deen, baida jiki yanayin shi irin na ƴan gayun fulani da hutu ya zauna masu, amman kuma duk da rashin jikin shi sam baida sirantaka, jikinsa na da ɗan cika ta yadda riga da wandon jeans din da yake sanye da su sun kar6e shi sosai, yanayin hasken fatarsa da kuma sumar kansa sun fallasa kasancewar shi bafullatani, duk da bai kai hasken su Deen ba amman kuma shima ba baƙi bane, saidai ya fi wasu daga cikin ƴan gidan su Deen ɗin haske kamar Omar da Sultan hasken mutumin ya fi nasu, ba kamar Deen da Leemah ba da suka fi kowa fari a gidan don sak kalar fatar mahaifiyarsu suka ɗauko, itama Batool tana da haske tafi su Omar da Sultan amman kuma ba ta kai hasken Deen da Leemah ba,
Leemah da bata kai ga miƙewa daga durƙuson da ta yi a gaban Deen, tana ganin mutumin da ya shigo ta yi saurin miƙewa, nufar shi ta yi muryarta da alamun mamaki ta furta, "Ya Fahad!" Bin ta da wani mugun kallo mom ɗin su ta yi ganin yadda take rawar jikin ganinsa, ba tun yanzu ba tana jin haushin yadda Leemah ke rawar ƙafa duk in ta ga Fahad, kwanaki can baya har tsare ta ta ta6a yi kan ta faɗi mata ko akwai wani abu a tsakaninsu, Leemah ɗin ta ce mata ita ba wani abu kuma miye don tana nuna murna in ta ganshi ba ɗan'uwanta bane, kuma matsayin yayanta tun da ɗan yayan mahaifinta ne, a lokacin kashe ma mom ɗin nasu baki ta yi da amsar da ta bata dama kuma Leemah tsagera ce.
Deen na ganin wanda ya shigo shima ya yi saurin miƙewa yana sakar masa murmushi ya nufe shi, dad dake zaune sai murmushi yake ganin Fahad ɗin, tsaye Leemah ta yi a gaban shi tana sakar mashi murmushi ta ce, "Sannu da zuwa yaya Fahad, ashe zaka zo?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, Deen na ƙarasowa ya nufe shi tare da ɗan rungumo shi yana yi mashi sannu da zuwa, bayan ya ɗago Fahad ɗin ya amsa mashi tare da yi masa an zo lafiya, kamo hannunsa ya yi yana faɗin su shiga ciki, gaba ɗaya falon ya karaɗe da kamshin turaren jikinsa mai daɗin ƙamshi da sanyaya zuciya yayin da suke ƙarasa shigowa ciki, a saman kujera ɗaya suka zauna, dad dake kallon shi fuskar shi ɗauke da murmushin ganin ɗan yayansa, da ido kawai mom din su ta bi su saidai a cikin ranta sam bata jin daɗin yadda su Deen ke rawar jiki akan Fahad din,
"Daddy ina wuni." Fahad din ya gaishe da shi a nutse, da faffaɗan murmushi ya amsa. "Lafiya lau son, ya hanya? Ya ka baro duk mutanen Funtua?" Amsa masa ya yi da Alhamdulillah duk suna lafiya suna gaishe da su, maida idon shi ya yi kan mom din su Deen itama ya gaishe da ita.
"Yauwa, an zo lafiya." Ta amsa babu yabo babu fallasa, ba tare da ya maida idonsa a kanta ba a taƙaice ya amsa mata da lafiya lau, kallon Deen ya yi suka sakar ma juna murmushi,
"Our football star, sai ga ka a ƙasarmu." Fahad din ya faɗa, ƴar dariya Deen ya yi ya ce, "I thought zan ganka cikin wanda suka zo welcoming ɗina a airport." Hannu ya kai ya ɗan shafi gashin fuskarsa da ke a kwance ya sha gyara tare da ɗan gyara zamansa ya ce mashi aiki ne ya ruƙe shi ya yi ƙoƙarin ya taho da wuri,
"Daga wurin aikin ma ka taho ke nan?" Dad ya tambaya, Fahad ya ɗaga kai ya bashi amsa da eh,
"To ya aikin? Ana dai ƙoƙari yadda ya kamata ko?" Kai ya jinjina ma Dad alamar eh, addu'ar Allah ya taimaka ya yi masa suka amsa da Amin har da Deen, Leemah ce ta shigo hannunta ruƙe da madaidaicin tray a saman shi glass jug ne ɗauke da ruwan lemu da cup, kallon mamaki mom ta bita da shi don ba wanda ya lura da lokacin da ta fice daga falon, ɗan tebur ɗin dake a gefen kujera ta dauko ta ɗaura tray ɗin, da kanta ta tsiyaya masa lemun ta miƙa mashi tana murmushi ta ce gashi ta san yana buƙatar shi tun da ya yo tafiya mai nisa, jin abun da ta ce ya sa shi kallonta suka haɗa ido ya sakar mata murmushi kumatunsa duk suka ɗan lotsa alamar yana da dimples, amsar cup ɗin lemun ya yi tare da yi mata godiya.
"Daɗi na da Leemah wani lokacin akwai hankali." Da sauri ta kalli daddynsu da ya yi maganar, ɗan tura baki ta yi, "Daddyyy, you mean wani lokacin bani da hankali ke nan?" Ta tambaya ta ɗan ɗaure fuska tare da tura baki,
"Haka ne mana." Kafin Dad ɗin nasu ya bata amsa Omar ya faɗi hakan, kallo mai kaman harara ta wurga masa dama ita ke bi mashi ba su cika jituwa ba, a faɗace ta ce, "To an ji ɗin." Gaba ɗaya Omar ɗin ya bata haushi don sai ta ji an muzanta ta a gaban Fahad, kallon dad din su ta yi ganin yana ƴar dariya ta ƙara ƙulewa kaman zata yi kuka ta ce, "Dad, you are the one who caused it and yet you are laughing." Maganar tata duk ta basu dariya, yana kallonta ya ce to shi mi ya yi ai ba a ji ya ce bata da hankali ba Omar ne ya faɗi hakan, tura baki ta yi tana ƙyaƙkyafta idanu, ta nufi jikin hannun kujerar gefen da Fahad yake ta zauna, ganin ya ruƙe lemun bai fara sha ba ya sa ta ce mashi ya sha mana, ya kai cup ɗin bakin shi ya fara kur6a a hankali, mom dai bakinta ya mutu sai bin Leemah take da ido ganin yadda take nema ta wuce gona da iri, sai ka ce ita kaɗai yake ɗan'uwanta da za ta yi ta faman rawan jiki haka,
"Amman dai ya Fahad kwana zaka yi ko?" Shiru ya ɗan yi ya dakata da shan lemun, kallonta ya yi bayan ya kawar da idonsa ya ce mata yau zai koma saboda aiki gobe, a shagwa6e ta ce, "To ba sai ka ɗauki excuse ba, yaushe rabon da ka zo nan gidan ka kwana." Ɗan murmushi kawai ya yi, Deen ya ce, "Pls ka bari sai gobe, dama akwai welcome dinner da aka shirya saboda ni sai mu je har da kai..." Tun kafin ya rufe baki mom ta tari numfashinsa, "To in bada shirin kwanan ya zo ba miyasa zaku matsa masa ne sai ya kwana? Ba ku ji ya ce daga wurin aiki ya taho nan ba, na san kayan jikin shi ne kawai ya taho da su, in ya tsaya ina zai samu wanda zai canza?" Duk kallonta suka yi irin na mamakin jin abun da ta ce, Fahad dai idonsa na ƙasa, a hankali ya ɗan yamutsa fuska jin maganarta, ba yau ne ta fara masa irin wannan kora da halin ba, shi ya sa bai son zuwa gidan ko da ya shigo Abuja bai wuce ya zo su gaisa ba, koda kwana zai yi in ya zo gidan daddy ya ce masa ya tsaya ya kwana wani lokacin sai ya ce mashi a ranar zai koma ko kuma ya ce sun zo wani taro ne an kama masu wurin da za su kwana, kusan in har ya zo gidan ya kwana to Deen na nan ne,
"Mom kaya ai ba problem bane, akwai clothing stores available da za a siya nan take ma a saka." Leemah ta faɗa tana watsa hannuwa, hannu Deen ya kai ya shafi sumarsa yana kallon Fahad da har lokacin kansa yake sadde ƙasa, ya ce masa ya ma kira wurin aikin ya ɗauki excuse anan zai kwana dama shima zai je Funtua ko goben sai su tafi tare, wani kallo mom din shi ta yi masa ba ta dai ce komai a.
"Bro Deen yanzu sai mu je a siya kayan da zai saka na dinner ɗin ko?" A ɗokance Leemah ta faɗa, kai Deen ya girgiza ya ce mata ba sai sun je sun siyo ba akwai kaya da ya siyo mashi daga can, daɗi ne ya kamata ta shiga sakin murmushi.
"Fahad, ya Hajiya fa? Wllh ina ta so in je don na kwana biyu ban leƙa ta ba sai dai ta waya, amman kwanan nan zan yi ƙoƙari in sha Allahu in samu in je dai." Tun kafin Fahad ya ce wani abu mom ta yi karaf ta ce, "To ai rashin zuwan ba laifin ka bane, kowa ya san yanayin aikin ka, ɗan siyasa dama ina ya ga wani isasshen lokacin da zai rinƙa yin tafiya a duk lokacin da ya so, kuma itama Hajiyar ba ta so a rinƙa ganinta ba ko yaushe, tun da ai har nuna kana son ta dawo nan ka yi amman ta ƙi amincewa, don haka ka ga sai dai ta rinƙa yin haƙuri sai lokacin da ta ganka kawai." Ta ƙarashe maganar tare da maida bayanta ta jingina da jikin kujera, yadda ta yi maganar ko a jikinta saima ta ɗauki waya tana latsawa, Fahad da Deen kuwa gaba ɗaya wutar su ce ta ɗauke jin kalamanta, shi ma dad ɗin shiru ya yi bai ce komai ba, wani abu ne ya tokare wuyan Fahad jin yadda Daddyn ya yi shiru, duk da dama bai yi zaton zai ce mata wani abu ba, saboda ba yau ta fara danƙara magana irin haka ba ba tare da ya tsawatar mata ba, ƙiri-ƙiri take nuna bata son danginsa su ra6e su, ta fi son ya rinƙa hidimta ma danginta kawai. Kowa na danginsu ya san bata son suna ra6ar shi sai ka ce ba ƴan'uwansa ba, abun takaicin ma hatta mahaifiyarsa bata ƙyale ba, ji dai yanzu maganar da ta faɗa, a cikin ran Fahad ayyanawa yake da a ce mahaifiyarsa ce ta yi maganar nan tabbas sai ta gane kuskurenta a wurin abbansu, amman shi duk irin abubuwan wulaƙanci da cin kashin da take ma danginsa ya zuba mata ido, yadda take cin karenta babu babbaka ba tare da ya iya yin wani katabus ba akai abun na basu mamaki, ko don tana da kyau ne ya sa ya ƙyale ta take abun da ta ga dama? Amma in haka ne, ai itama mahaifiyar su Fahad tana da kyau don bafullatana ce kuma jinin sarauta amman hakan bai sa abbansu ya bata damar da zata wulaƙanta na shi ba, dama kuma mahaifiyarsu Hajiya Amina mutuniyar kirki ce bata da halin wulaƙanta mutane. In ba don alaƙar aure ta haɗa Hajiya Jameela da nasu ba wllh bata kai matsayin da za ta taka wani daga cikin ahalin su ba ba tare da ta gane kuskurenta ba, matar da ahalinta duk talakawa ne kawai kyawun sura da Allah ya yi masu ne ya rufa masu asiri suke auran masu kuɗi, dama kuma iyayensu mukwaɗaita ne mugun son abun duniya gare su, hakan ya sa suka maida ƴaƴannasu jari.
Deen ya lura da yanayin fuskar Fahad akwai alamun 6acin rai dama kuma ya san shi da zuciya, kamo hannunsa ya yi ya ce mashi su je ɗaki zai nuna mashi abu, hakan ma mom ɗin sai da ta tanka, ta ɗaga murya tana faɗin su da ya bari anan ba don shi suka zo part ɗin nasa ba ko su basu da muhimmanci ne, Dad ne ya ce mata ta ƙyale su ta san kamar abokai suke da juna za su buƙaci ke6ewa su tattauna tun da sun daɗe ba su haɗu ba, Deen bai tsaya saurarar ta ba ya ja Fahad ɗin suka shige cikin bedroom, dogon tsoki ta ja tare da miƙewa ta nufi hanyar barin falon tana tafiya cike da isa, duk suka bita da ido, su kan su yaranta sun fahimci tana nuna bambanci tsakanin danginta da na daddynsu in suka zo ko suka haɗu da su, ko Funtua sai a daɗe bata je ba sai in wata hidima ta kama itama sau da yawa sai daddyn ya matsa mata sannan ta je, akwai part ɗin su da suke sauka a gidan Hajiyar Ambasada, haka za tai ta wulaƙanci tana yi ma mutane kallon rashin arziki, ko zaman da suke yi a gidan Hajiyar ba so take ba saida tai ta yi ma daddyn mitar ya gina masu gidansu daban kamar yadda yayansa wato mahaifin Fahad shima yake da gidansa daban, da ya tambaye ta miye illar zaman su gida ɗaya da Hajiya, sai ta fake da cewa unguwar da gidan yake ta yi ƙauye da yawa ba kamar unguwar da gidansu Fahad yake ba a bakin babban titi ba hayaniya da cunkoso, kawai ta faɗa masa hakan ne amman saboda bata son yadda danginsu da mutane suke zuwa in suka je ne, wani lokacin bata samun damar yi masu wulaƙanci saboda Hajiya na taka mata burki, shi ya sa take son ya gina masu gida daban su rinƙa sauka yadda zata ji daɗin taka duk wanda ta ke so. Duk suka je sai ta yi ta mashi mitar ya gina masu gida, sai dai ya amsa mata da zai gina masu, har dai daga baya sai da ta yi nasarar saka shi ya fara yi masu ginin katafaren gida amman har yanzu ba a kammala ba.
Batool na ganin mom ɗinsu ta fita ta miƙe ta bi bayanta, Sultan da Omar ma duk suka miƙe suka fita, miƙewa shima dad ya yi zai tafi, ganin Leemah ta yi zaune bata da niyyar tashi ya ce mata ta tashi su je, tana yamutsa fuska ta ce mashi tana son su yi hira da ya Fahad ne, ce mata ya yi ta bari zuwa anjima in sun gama tattaunawa tun da anan zai kwana sai su yi hiran, fuskarta a yamutse ta tashi ta bi bayan shi suka fita.
Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268
