Ramin Kura Page 9&10 Comple

Ramin Kura Page 9&10 Complete

 ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻

# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ

https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D    

~Na Maryam Naseer Mirrah~

𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️

   

Book One paid 

       ♡

Page 9&10


𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. 


# Be a Person

# Who Was? 

# Money in Pocket

# Power In rocket 

# Knowledge in Mind 

# Kindness in heart 

# Confidence on face 

# Responsibility in Soul

# Love Romance scene 

# A.k.a Ammey Laylerh 


   ♡♡♡♡♡♡♡♡ 


 Kai tsaye dake gidan nasu a bakin titi yake tana fitowa ta sama abin hawa tana shige wa, "Hajiya ina muka nufa?" maganar ɗan sahun ya dawo da ita hayyacinta.  "5 star Restaurant" ta bashi amsa a takaice domin acan suka shirya haɗuwan. Zuwa lokacin hadarin ya fara bada ruwa ko in ce yayyafi kaɗan². A gaban ƙayataccen  5 star Restaurant  me napep ɗin ya sauƙe ta, No na sabon inspector ɗin da aka tura mata jiya da dare a WhatsApp nata, kai tsaye ta ƙira no ɗin inda se dai ba'a ɗaga ba. don haka ta fara za gaye a wurin tana kuma ci gaba da ƙiran shi. Ta zo daf da wani table taji anyi mata gyaran murya. Saurin kallar daga inda gyarar muryan ya fito tayi, kai tsaye idanunta na sauƙa akan wani kyakkyawan matashin saurayi chocolate color. A kallon farko data masa ta san cewar shi ne wanda take nema, "Inspector Maleek?" ta faɗi tana nuna shi, wani cool murmushi ya sakar mata se dai ba sosai ya fito ba yana gyaɗa mata kansa alaman *YEAH* shi ne.  Sara masa tayi tana ɗan risinar da kanta ƙasa. Da wurin zama ya mata nuni kujerar dake pacing da shi, zaune take tana harɗe ƙafarta ɗaya kan ɗaya. Cikin harshen turanci ta gaida shi yana amsa ta tare da miƙa mata hannun a matsayin su yi musabaha. Ga tarin mamakinsa kuwa se gashi ta miƙa masa hannun tare da furta. "Ni ce  Hannah Ayuba me Kano"  Janye hannun nasa yayi don shi ƙa'idar aikin sa babu ma mata a ciki bare kuma azo batun gaisa wa ma, itama janye nata hannun tayi fuskar ta ƙawace da kyakkyawan murmushinta lokacin da yake sanar da ita sunan shi. 

"MALEEK MUSTAPHA WAZEER" Ta jima tana jin wannan sunan ko dan tsaiwa da jajircewarsa wurin aikinsa kuwa da yake yi da rai da kuma rayuwar sa. "Na sani!" ta bashi amsa daidai lokacin da da wata maid service ke jere musu, meat pie, chicken pie, se  valvet and pancakes. Da kuma energy drinks.  Energy drinks ɗin ta ɗauka tare da zubawa a glas cup tana ɗan tura masa zuwa gaban sa, Ɗan sipping nashi tayi se kuma ta dire tana kallon shi ganin be ɗauka nashin ba.  "Da duk kan alamu kai mai gaskiya ne sir, gaka a haka dai  ba yabo ba fallasa, amma kana da kyan gani ga matsayi me kyau a cikin al'umma" Se kuma ta ɗan dakata kafin ta kafe shi da fararen idanunta tare da ci gaba da cewa. 

   "Se dai abin  tambayar ɗaya ce anan itace me yasa har yanzun bakai aure ba?." ta faɗi tana wani rausayar da kanta gefe gwanin birgewa. Zaman sa ya gyara tare da ɗaukan glass cup ɗin dake gaban sa ya ɗanyi sipping nashi ba da yawa ba kaɗan yana sakin wani lalataccen murmushi, tare da furta. "Kema kince ba yabo ba fallasa ne ƴan mata, So kinga kenan ba macen da zata kware min har ma ta soni a hakan nan yanda nake, kuma dama  bana da ra'ayin wata macen, So dan haka nake ganin muyi haƙuri kawai mu amsawa kanmu sunan *TUZURAI* Mu maze ba wata matsala kawai nake ga....." ya yi maganar yana wani kawar da kansa gefe. Daidai nan wayar sa dake ajje saman table ɗin dake tsakiyar su tayi haske alamar ƙira ya shigo. A kusan tare ita dashi suka kai duban su kan wayar. Tarrrr idanunsu na kaiwa kan sunan  *Officer K Mashi Dikko....*   Hannu ta kai da niyar taɓa wayar se dai ya riga ta yana Saurin ɗauka domin bai son amsa wayar gabanta, se dai ba tare daya sani ba  hannun sa ya amsa wayar. Kai tsaye muryan babban ogan nasa ya dire cikin kunnuwansu su duka biyun. Ta hanyar fashewa da wata mahaukaciyar dariya yana me furta. "Ya dai ɗan ƙaramin Inspector ykk ya kuma baƙunta da aikinka?, fatan dai a wannan karon babu  masu baka tsoro Irina ba Inspector Maleek Mustapha wazeer?"   wani kalan lalataccen murmushi Maleek ɗin ya saki tare da  jan idanunsa ya lumshe, kafin kuma ya ware yana me fesar da wani zazzafan numfashi ya furta.  "Tsoro kace?, kuma wai ni ɗin? Da dukkan alamu sir Dikko yana manta cewar  tare yake da  ABDULMALEEK MUSTAPHA WAZEER ne, to ai shi kansa tsoron tsorona yake!, Ka sani bana da bukatar runduna domin  datsaka,Ni kaɗaina na zarta wadata, Domin ni kaina runduna ne, jikina kuma shi ne makamina, sanya war albarka al'umma ta kuma shi ne shigo ne, kare ƙasa ta kuma daga gurɓatattun mutane irinka shi ne aiki na dana rantsuwa a kai domin kawo ƙarshen ire irenku maci amanar ƙasa, dacin dunduniyarta...." Wani  kyakkyawan murmushi ne ya wanzu saman fuskar wanda suke wayar, yana murmushin ne kuma yana shafa haɓarsa daga inda yake zaune saman lafiyayyar kujerar office nashi, kafin cikin muryarsa me ɗauke da iko da isa ya ce."Jarumtarka tabbas na kashe ni Maleek Wazeer,  se dai ka sani you’re not going to get anything from mee. zaifi maka kyau idan akace ka zare hannunka daga wannan binceken haka nan, Idan kuma ba haka ba ka tuna kana da ahali, uwa da uba duk suna raye, kana ita wannan abar kanta dake gabanta zata iya faɗa wa a tarkon wasan..... " A bazata wani lalataccen murmushi ya  subce daga fuskar Maleek ɗin. Jin Sautin lalataccen murmushin Maleek ɗin da yafi natsa a kaff cikin duniyar sama da komai ne Maleek ɗin ya sakar masa. Ɗan zame wayar yayi tare da kallon screen na woyar sai kuma ya sake manna wayar da kunnunsa, still Sautin fitar murmushin ya kuma ji daga Maleek ɗin. 

   "Believe me K Mashi babu  wanda ya isa ya rufe wannan case ɗin until I get to the bottom of everything. I  Promise you wannan ɗin Alawari ne da na ɗaaukarma ƙasa ta da rai da ruhina. " Mr Maleek, if you think you’re goin to get something from me you’re quite mistaken..." K Mashin ya faɗi kamar a fusace. " rintse idon sa yayi kafin da ɗan ƙarfi ya daki table ɗin yana fitar da wani  huci mai zafi cikin ɓacin rai ya furta. "How dare you da zanji tsoronka?...." 

 Wata kafurar dariya K mashin ya sake saki tare da  cewa. "Da duk kan alamu wannan aikin naka da kake ji dashi tamkar rai da mutuwa, to ina bai ba ka tabbacin idan har bakai wasa ba a dare ɗaya sena gama lalata maka komai, kai harda goben ka ma idan naga dama, Shi wannan aikin naka dai da kake mutuwar ji dashi, to dashi ne zan lalata gobenka ta hanyar kirkirar maka wani laifin da baka da masaniya akansa. Ta yanda a dare daya zan mai da kai ɗan ta'addar da babu irin sa a ƙasar nigeria, Kaga kenan daga nan sai ka shiryama mutuwa, domin cigaba da wannan aikin dole kana da buƙatar izini na  Maleek, karka manta kada kai tantama dan gane da abin da nace maka zan aikata..... "  Gyara zamansa yayi tare da fesar da sassayan numfashi murya cike kamala da daraja ya fara motsa lips inshi cikin nutsuwa tsantsa ya furta.

"Ita ƙaddara ta gaji haka dama ta kan iya juya fari ya koma baƙi, ko ta juya baƙi ya koma fari, haka ALLAH yake   tsara lamuransa daga wannan mataki zuwa wancan mataki, kuma komai na faruwa ne  tamkar yadda yake a rubuce a lauhul Mahfouz, babu abin da ka iya  sauya baƙar ƙaddara ta koma fara kamar tamkar yacce taka ta kasa jan zaka. Zan rura ka tamkar Wuta ta ruru bayan tumu .. "  Daga haka ya datse ƙiran yana ɗan fesar da wata zazzafar iska. Tare da dafe goshinsa da hannuwansa yana me furta. 

      ☆ 

"Wannan itace duniyar da muke rayuwa a cikin ta, wacce take ƙunshe dajin dadi da kuma tsatsanin azaba. Inda ƙalilan daga cikin ta su ne  suke jin daɗinta, inda mafi yawan cikin ta kuma sune  suke shan hawalarta. ƘIYAYYA, HASSADA da MUGUNTA  su ne ababen da suke ƙara ta'azzara komai a cikin wannan duniyar tamu. 

   Ƙarni bayan ƙarni shekaru naci gaba da shuɗewa amma babu wani Abu da yake sanjawa, saima ƙara ta'azzara da abin  yake yi, inda abin tambayar anan shi ne.  

     Shin wannan duniyar zata taɓa sanjawa kuwa?......Sabo da masu ƙarfin ikon cikin ta,  su ne a koda yaushe suke azabtar da talakawan cikinta, Inda mu kuma  muke nan burinmu NIGERIAN'MU ta gyaru dama duniyar baki ɗaya, Inda muke bada rayuwar mu ta hanyar Sadaukarwa duk wa ƙasar tamu, amma wasu daga cikin manyan mu suna lalatamana kowacce hanyar da muka ɗauko domin gyarawar. Wannan abu yana matuƙar ƙona zuciya ta da taɓa min ita sosai, amma a rai da jikina nake jin In sha ALLAHU komai se ya gyaru....." Ɗan tallafar kuncin ta tayi tare da furta.  "To amma ta yaya hakan zata faru???......" ta faɗi tana wani ɗan zazzaro idon ta waje, domin ita dai ta san da kamar wuya hakan. Se kuma ta dawo zuwa normally nata tare cewa.  "Tabbas *NIGERIA* wata ƙasace mai tarin tseko mai labarai cike da!, damfara da rashawa, inda masu ƙaramin ƙarfi suke  wahala A hannun talauci da kuma yunwa.

    To amma dai koma  meye! namu ba tsokaci da ƙorafi bane, abinda muka sani kawai mu bada rayuwarmu domin TUTARMU taci gaba da kaɗawa, da kuma kawo ƙarshen zalumci wa ƙasar mu  Nigeria baki ɗaya dama duniyar. Tabbas kai ne tauraro mai haskaka wannan tafiyar MALEEK!, Ƙasar mu dole mazaje take nema irin ka sir MALEEK WAZEER. Tsayayyen namiji mai aiki da rai da rayuwarsa mai burin zamewa *NIGERIA* uba, uban data riga da ta rasa a tin farko....." HANNAH ɗin ta furta tanajin zata yi aiki bakin rai bakin fama tare da wannan bawan ALLAH. 

      ☆" Tabbas kin yi gaskiya yarinya  irin ka DUNIYARMU take da buƙata Yaro, domin Aiki da sadaukar wa al'umma Rayuwa!, AIKI domin sanya ma zukatan bayin ALLAH nutsuwa!, Aiki da ayyuka domin sadaukar da tasu Rayuwar ma rayuwar al'umma!!!..... Dukan su a tare suka juyo ga dattijon dake zaune daga ta  bayansu.  Wani kyakkyawan murmushi mutumin ya musu su duka biyun, yana barin wurin bayan ya furta "Kun dace da juna, zan so ku amri juna!"  Wani murmushin bazata ne ya subce a kyakkyawar fuskar Maleek ɗin. Yana kare fuskar nashi da tafukan hannayensa. Se Yake ganin tamkar yanzun ne komai daya faru tsakanin sa da D. C. O. KABEER MASHI ke faruwa.... 

    ☆ 

_"Waya baka umarnin kai harbin? Ka gaya min waya baka umarnin kai harbin?"

   K Mashin Ya faɗa a matuƙar tsawa ce. Wanda shi kuma kai tsaye ya furta masa 

 _"Ba kowa Sir"_ 

     Wani ɗan iskan kallo sir ɗin ya cillo masa cikin yanayin fusatar zuciya ya doka table ɗin dake gaban sa, tare da furta. 

  _"Me yasa kayi?....

    Folding hannuwansa yayi saman ƙirjinsa tare da furta. 

    _"Ɓacin Raine sir sabo da manyan  shugabaninmu su ne suke neman ruguza ƙasar da muke_" ya furta cikin rashin shakkun a gaban Wanda yake tsayen. 

    _"Sanin kan Kane wannan mutumin da muka kama shi ne babbar hujjarmu koh......_

  Yayi maganar yana wani wuwwula idanunsa irin na shegun nan. Shi kuma kai tsaye ya ce dashi. 

    _"Wacce hujja kuma sir?, kullum maganar kenan, munje mun shayo baƙar wuya tuƙuru wajen kame masu laifi amma daga ƙarshe manyan ƙasar  sai su fitar da su da hanyar wasu gurɓatattu daga cikin ƴan sandan mu _"

      _" Shi yasa kai kuma ka harbe shi?, Shin me yasa A  duk lokacin da muke kan aiki irin haka kaine mutum na farko da yake fara bamu  matsala?, A matsayinka na ɗan sanda sammm ko kaɗan baka iya sarrafa kanka. Ko kaɗan baka iyawa koda yaushe cikin faɗa kake, bayan kuma kai ɗin ba kowa bane face ɗan matsala da  jami'an ƙasar sa matsala MALEEK MUSTAPHA..... 

     Wani irin doka coffee table ɗin dake gabansa yayi, cikin tsananin bacin rai MALEEK MUSTAPHA WAZEER ɗin da gajiyawa da rainin yawo irin na sir ɗin nasa ya  damƙi  wuyar rigar sa tare da furta. 

     _"Sabo dani jirgin ƙasa ne duk Wanda yabi ta  hanyata markaɗeshi nake nabi ta kansa, sannan kuma  zaku iya dakatar da ruwa idan kuka tare shi, se dai idan ya tashi ɓallewa tamkar teku yake, haɗawa yake ya tafi da duk wani gurɓatacce waɗan da suka kasance marassa amfani a cikin hanyarsa_" Se kuma ya ɗan dakata tare dayin wani irin kafurin murmushi  kafin yace "Do you really want us to play this game?, I can assure you I know exactly when to throw my card. Nasan baka Sani ba, but I do know a lot of things about you, I know about your criminal records ka sani. And ina son ka sani nasan irin miyagun abubuwan da kake aikatawa wanda kake ganin babu wanda ya san kana aikatawa, shi yasa duk wata hanya da zanbi kake ƙoƙarin daƙusar dani, But se dai ka sani  If you cooperate with me, zanyi duk iyaka  ƙoƙarina wajen bankaɗo wannan sirrin Sir" 

Aikuwa nan take D. C. O. Ɗin yayi wani irin zabura da niyar hankaɗar da Inspector Maleek ɗin. Wanda shi kuma yaƙi bashi damar hakan tare da sake  finciko wuyan ogan nasa  ya matse yana haɗe shi da jikin sofar da yake jiki, yana sakin huci tare da furta. "I am not playing games with you, Now tell me sena faɗama duniya ko wanene kai nayi alƙawari a duk inda nake.....?" Shi kuwa Mr D. C. O zuwa wannan lokacin da ya gama jin  matsa, tini idanunsa sun firfito waje yana neman hanyar da zai shaƙi koda  iskar numfashinsa ne ya fitar.... 

Daga haka yayi  wani irin wurgi da D. C. O ɗin tare da  ficewa  a office ɗin kowa na bashi hanya.......   

  Shi ne dalilin, wannan shi ne dalilin masa transfer daga Kaduna zuwa Kano, shi ne silar faruwar komai. "Kana lafiya Sir Maleek?..." maganar Hannah ɗin ya dawo dashi daga cikin duniyar tunanin daya ɗan Lula. 

Ita se a yanzu nema take ƙarema shigarsa kallo. Sanye yake cikin wasu tsadaddun luzary    Ride vizzon sky blue, ƙirar companyn Christian Dior, inda daga ƙasar rigar kuma 

  irin hadarin Dubai ɗin nan ce kaɗan. Sai lallausan farin wando trouser kansa sanye cikin hular luxary supereme se sun glasess ɗin da ya  toshe idonsa dashi. Inda yayi wani irin zama, Zama ne na wanda suka Isa. Suke kuma ji da kansu Wanda hakan da yayi ne ya shagaltar da Hannah  a kallonsa. ♡ Ba tare da cewar su kansu sun san da cewar tsarin Ƙaddararsu ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar ɗan uwansa, da wannan tsarin na  ƙaddararsu ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wannensu. 

   ☆  

A natse a kuma wani irin hankali ta ƙarasa zare navy blue turkian abayar dake jikinta tana  jefar da ita  saman maroon Chiara Andreatti sofar dake babban bedroom ɗin nata, Kai tsaye ta na nufar gaban mirrorn ɗakin.

   Kyakkawar fuskarta da ta ɗanyi  ja ta kalla ta cikin mirrorn, Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da zare fararen undies ɗin dake jikinta tana watsarsu saman bed nata. Kai tsaye shower ta sa karma kan ta, tare ɗan  lumshe ido saboda damuwar da take a cikin ta. 

    Gashin kanta gaba ɗaya ta tattare tana yin baya dashi tana bama ruwan dake dukan jiki da kuma fuskar ta damar dakar ko ina. Yana yin yanda ruwan ke dukan jiki da kuma kanta kawai ya Isa bayyana maka cewar lallai ba'a cikin tunani da kuma  hayyacinta  take ba. Domin duk yanda taso da kawar wannan tunani da maganar ta gaza yin hakan. Ahankali ta kai hannunta tana kashe showern, tare da ɗaukar wata kakkaurar bathrobe ɗin dake gefen ta  tana  sanya wa  jikinta, ba tare data  tsaya tsane gashin kanta dake malalar da ruwa ba ta  nufi ƙofar fita cikin bathroom ɗin. A natse ta kai fararen santala santalan hannayenta kan handle na ƙofar tana  buɗewa, yayin da take jin ƙirjinta na amsawa aduk   wani taku daya da  zata yi, na tsantsanr azabtuwar da ranta keyi akan yayan nata ɗaya tilo tallll data gama mallaka a duniyar. har zuwa lokacin kuwa zuciyarta zafi take yi mata, yayin da take jin wani irin ɗacin dake   daɗa mamaye maƙoshinsa dangane da wannan bahagon lamarin, Fararen idanunta  da suke a lumshe ta ware saboda bata jin zata  iya jurewa gizon da amsa kuwwan da maganganunsu ke mata, wanda suke  dawo mata tamkar dai yanzun abin yake faruwa. Don haka a yanayin da take ciki bata da  buƙatar komai domin brain nata na  gab  da juyewa, wanda hakan kuma yayi kusan sanadiyyar hautsinewar tunanin ta. Yayinda da har yanzun kalaman Ihsan ɗin ke mata yawo a tsaƙar kanta da kuma tunaninta. Barin ma kalmar. "Ni fa da ace wannan bazaraten matashin saurayin ze aure ni ko na rana ɗaya ne, wllh zan yarda, ke ko da ace ma na dare ɗaya ne wllh zan iya bashi kaina kyauta ma in yana so". Wani kalan runtse idanunta tayi  zuciyar ta na mata  tamkar zata bar gangar jikinta, tamkar kuma zata tarwatsa mata  ƙwaƙwalwar kai  da zuciyar ta. Wani 

  brown towel ta ɗauka tana ɗaure kanta dashi, jin sanyin ruwan na neman ratsata, farar fatar jikin  nan kuwa se famar ƙyalli ta keyi, tana bayyanar da tsananin hutu da kuma jin ɗadi da tsadaddiyar kular da ta ke samu ta hanyar amfani da skin products masu tsananin kyau da tsada. Kai tsaye gaban madubin dakinta ta nufa tana zama kan stool tare da kunna hand dryer tafara busar da gashin kanta dake ɗigar da ruwa. Daga nan kuma ta shige cikin clothes nata tana shirya kanta cikin wata rantsatstsiyar doguwar malaysian mara nauyi ash color, domin komai nashi da yafi so ta jima da haddarsu, shi yasa kusan komanta kalan nashi ne, kai tsaye nufi hanyar fita ta ƙofar baya, zuwa ɗan Balcony nata. Tana  zira Burberry slippers 

wannan shegen ƙamshin turaren nata na Versace bright crystal ya gama mamaye inda take tsayen. 

Babu motsin komai a wurin sai ƙamshin flower's ɗin dake ratsa ko ina na passes ɗin, kasancewar wurin zagaye yake da tarin shukoki na flower's color daban daban, Hakan seya bama yanayin dadɗan yanayi na musamman, tare da cakuɗuwa da iskar wajen da kuma ƙamshinta yana sanja iskar wajen.  Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauƙe ta ƙauna da kewan face nashi da tayi. loƙacin da taji jiniyar car's nashi sun  karaɗe gaba ɗaya ilahirin gidan. Da shegun  jiga jigan manyan motocin suke yi. Wata  mahaukaciyar Black car ɗin da tafi kowacce kyau da tsaruwa a cikin su wani soldier yay hanzarin buɗe masa  luxurious  car ɗin sanfurin ƙirar Rolls *R* Rayce. Sauran  bodyguards ɗin dake tsaitsaye gaban manyan motocin  da suka kasance launinsu bakake tikk su kuma suna sanƙamewa. Daidai lokacin da yake fitowa tsaye kan diga digansa, jikinsa na ingarman namiji na sake bayyanuwa, wani irin sake zanƙamewa suka yi tare da sara masa cikin ladab da kuma girmamawa, Shi kuwa cikin takun jan hankali da mazan taka ya fara tafiya kan sawayensa. taku yake yi irin na cikakkun  jarumai ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa ka san cewar shi ɗin cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma. Daga inda take tsaye bayan jin tsaiwar motocin nashi zuciyan ta taƙi ci gaba da bata haɗin kai da kuma  kwarin gwiwan kin kallonsa. Sosai ta ƙura masa kyawawan idanunta daga yanayin yadda yake takunsa da cikakken ƙarfi na hasali zaka san cewar ehhhh lallai shi ɗin matashi  ne mai ji da lafiya, cikakken namiji ne wanda a kallah zai iya kai 33 year's haka  a duniya,  hair'nsa yana kwance  ya sha gyara irin na Manyan soldier's ɗin nan masu ji da gayu da kuma samartaka. Yana tafe yana shafan woyansa me ƙirar  Samsung galaxy A16. Ahankali ya ɗago fararen idanuwansa yana  kallar  agogon _Patek Philippe_ ɗin  dake ɗaure a tsintsiyar hannun sa, Haka cikin tafasar jini yaci gaba da takunsa  yana sake nufo ganinta  kai tsaye. Wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙara mannewa da jikin Railer ɗin  tana jin shin a wanne mataki ne ma ya kamata ace ta  sanya shi?  Tabbas tana jinsa sosai har cikin zuciya da ruhinta, se dai dan me ƙaddara zata mata?, me yasa zata bari tana jin yayan nata haka don me don me don meeee?...... 

    "Lafiyanki kuwa Nufaisa Inata ta magana shiru baki jini ba tun ɗazun?" Haka taji sauƙarn muryan mahaifiyanta dake tsaye daga bayanta tun ɗazun tana ta mata magana shiru. Hakan ya sanya a  ɗan  tsorace ta juyo don batay tunanin wanzuwar Ammeyn nata a wurin ba. Ijiyan zuciyan hakan ta sauƙe tana juyowa gaba ɗayanta. "Ina kallon Woje ne Ammey !!!" Ta furta tana son kawar da abin da ke damun. Daidai kuma da loƙacin da yake bayyana a wurin, wanda  kai tsaye mayen ƙamshinsa ne ya fara sanar mata da wanzuwar nashi  wanda baya taɓa ɓuya koda kuwa a cikin dubu yake.

  Murmushi Ammeyn ta sakar masa tana ajje Plate na abincin dake hannun ta saman ɗan glas table ɗin dake wurin, tare da furta "Yau kuma da wuri haka Aliyu?" ta furta daidai lokacin da yake kaiwa zaune saman cushion ɗin dake gefe da inda take  lafe luff tamkar wata ƴar mage. "Lolly Barka da dawowa" ta faɗi  tana sauƙar da kanta ƙasa daga kallon sa, dan jin yadda gabanta ke dukan tara tara don ta san kwanan zancen. Zuwa lokacin kuma Ammey tabar wurin. "Shi waccan ɗin wayene?, kana miye alaƙar dake tsakanin ki da shi har yake da damar kusanci irin haka dake?" Rasss haka taji gabanta ya sake faɗuwa tana nemar ma diriricewa. "Tell mee" ɗin daya sake faɗa ne ya sanya ta saurin ɗagowa tana kallarsa. Se kuma tayi saurin meda shi inda ta ɗaukosa don ganin yadda ya kafe ta da fararen idanunsa. Ganin duk yacce take ne da kuma ƙin masa maganar da tayi ne ya sanya shi miƙewa tsaye tare da furta. "Idan kuma kin shirya ajje aikin ne kuma kina iya turo shi gida, bawai iya tare mutum a woje ba" yana kaiwa nan yay ficewansa daga wurin... 

   Wani kalan nooding kanta tayi tare da  sake lafewa a cikin cushion ɗin tana janye idanunta daga kansa..........

  Tare da furta (Yaya AA Matsala)..... 

☆ Kai tsaye daga nan ɓangarensa ya nufa, yana shiga ya zare kayan jikinsa. A ƙugunsa ya ɗaura towel ɗin yana  faɗa wa  toilet ya sakarma kansa ruwa yana rufe idanuwansa ahankali gudun kada ruwan su shiga mai. Yana fitowa kai tsaye ƙananun kaya  marasa nauyi ya sanya  yana kwanciyar sa kafin lokacin sallar zuhr yayi. 

   ☆ AFTER ISHA'I 

Ahankali  yake saƙƙowa  daga saman benensa hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa, yana tafiyar nan  nasahi tamkar wani King. Inda yake sanye cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na trouser, yayinda fuskar nan ke sakaye cikin sun glasses ya sanya hular jacket ɗin dake saman  kayan jikinsa, kasancewar ruwan da aka ɗanyi kafin bayan sallar isha'i sannan ya sanya face mask. gentle yaci gaba da saƙƙowa zuwa downstairs, jikin sa na fidda wani irin fitinannen ƙamshin perfumes nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa. Babu kowa a parlourn don haka a ƙasaitance ya kai zaune zama irin na sarauta saman Royal caution ɗin dake jere a parlourn,  system nashi ya janyo yana fara aikinsa. cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin A/cn  na ratsa ko ina na parlourn. Mahaifinsa da tin farkon shigowarsa parlourn yake kallon sa ne yaja wani ɓoyaygen numfashi. A ransa yana ayyana abubuwa da yawa akansa. 

   Domin shi Captain AA ba  cikakken mutum ne kamar kowa ba, duba da murɗaɗɗen mutun ne shi wanda baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ma ina ya dosa kwata kwata. Idanunsa yaja yana lumshe wa a cikin zuciyar yana me furta.  _Wuta ta ruru bayan tumu, tabbas babu wanda ya isa yama ɗan doya rumfa ubansa be noma ba_ 

   Kafin kuma wani shegen murmushi ya subce masa aransa yake hasko wutar bal balalin masifar da zata kunnooooo...... 


Hhhhhhhhhh Ni kuwa AMMEY LAYLERH  nace to ai shikenan🤗 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️


_Domin ni ban san asalin wannan karin Maganar na mahaifin Captain AA ba..... _


08104493215


*BY AMMEY LAYLERH ✍️ *

Post a Comment

Previous Post Next Post