*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 4_
*_Free page_*
_______________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃.
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
____________________
.........Gaba ɗaya hankalin yaran sojojin ya raja'a akan taɗi da jin ɗumin wutar da suka kunna. Amma shi yana gefe a saman wata bishiya ko tsoron dare baya ji balle wasu halittu daka iya fakewa a bishiyar koma aljanu. Shi ɗin ɗaya ne daga cikin amintattun yaran Zak-Shadow, dan haka duk wani motsinsa na yau da kullum zuwa yanzu ya haddace shi. Yakan fahimci yaren idanu daga Zak-Shadow, ya kan fahimci na gangar jiki harna ɗabi'a. Tun lokacin daya kai masa dawar daya zubama tsuntsaye ya fahimci akwai damuwa a tare da shi, dan haka ya laɓe yana nazartar shi, sai kuma akai sa'a aka kira wayarsa a lokacin, dan haka duk wayar da yayi acikin kunnensa take, duk da ba wani surutu ya zuba ba, amma da yake yana ankare da sai ya saka ma komai alamar tambaya. Sai kuma gashi da za'ayi sallar magriba yaga Major Imran Abbas ne yaja sallar, dan haka zuciyarsa ta bashi Lieutenant Colonel na shirin barin jejin kamar yanda ya saba fitar ɓadda sawu da tunanin basa fahimta. Eh tabbas basa fahimtar, dan a duk sanda suka daina ganin gilmawarsa kawai abinda zuciyarsu ke basu yana zagayen sauran sansanin ne ko meeting da sauran jagororin sansanin wato Captains, dan yakan yi hakan akai-akai. Dan kuwa runduna guda ce a ƙarƙashinsa dake rarrabe a cikin jejin da suka kai a dadin dubu ɗaya da wani abu, kuma shine Boss gaba ɗaya da suke ƙarƙashin umarninsa, Major Imran Executive Officer, sai Captains da su na ƙasa, duk da dai suma yaran hawa-hawa ne, kamar shi yana cikin Lieutenants. Akwai Sergeants na ƙasansu, akwai kuma Soldiers (rank-and-file).
Tun asali tun fari shi dama ya shiga aikin soja ne badan kishin ƙasa ba, dan kamar an ƙirƙireshi ne saboda manufar da yake akai a yanzu, kafin ma ya shigo aikin an bashi horo na musamman ta yanda yake iya duk wani aikin munafunci da leƙen asiri cike da wayo, musamman akan Zak-Shadow a yanzu, kuma yana da tabbacin akwai ire-iren sa ma dan bashi ɗaya bane kuma suna tare da Zak-Shadow ɗin kusa sosai dama wasu manyan jami'ai irin Zak-Shadow ko na sama da shi harma dana ƙasa da shi batare da su sun sani ba. Koda yake kwanaki an taɓa kama ire-iren nasu aka kuma hukunta shi da hukunci mai girma, dan amanar gidan soja ta wuce tunanin mai tunani, su kansu a lokuta da dama suna wannan sheɗancin ne a tsorace, matuƙar tsoron gudun randa zata tashi musu. Amma maƙudan kuɗin da ake biyansu da shi na tunzurasu da assasa gurɓataccen tunaninsu da jagorancin shaiɗan. Balle shi dake a ƙarƙashin babban ZAKI, dan bafa a banza aka saka ma *_ZAK-SHADOW_* ɗin wannan sunan ba a gidan Soja, Zakin ne na gasken gaske da ya ciyo sunan tunma a asalin sunan yankan sa. Maybe shiyasa ma sunan ke da tasiri sosai a rayuwarsa da ɗabi'arsa. (ALLAH ya ƙara kare ku jami'anmu a duk inda kuke🙏. Kai mutane na ku ba MAZAJEN FAMA jinjinar ban girma mana💪😄, a haɗa musu da kirari na musamman kuma, ƙarshe a sara musu👍🏼).
Waya ya zaro daga jikinsa, ƙarama ƙirar nokia, ya dannama wata number kira. Ba'a ɗaga ba sai da ta kusa tsinkewa. Murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Good evening Sir!”.
Amsa masa da akai daga can ya sashi cigaba da magana cikin tsantseni da risinar da kai tamkar yana a gaban wancan ɗin.
“Sir! Yau ɗin nan ya fita. Dan sanda na kai masa dawar da yake zubama tsuntsaye bayan nabar wajen sai na laɓe, naji yana waya da matarsa kamar.....”
Sai kuma yay ɗan jimm alamar saurare. Kafin cikin yaƙini da son a yarda da shi ya cigaba da faɗin, “Tabbas na tabbatar baya jejin nan, dan yau ba shine yaja sallar magriba da isha'i ba. Na duba inda ake ajiye mashin ɗinsa kuma babu shi, na leƙa tantinsu oga Imran ne kawai a ciki, kuma in dai ba ana kan aiki ba baka raba su. Duk da haka na bincika dukkan sauran sansanin kuma an tabbatar min bai je ba”.
Sai kuma yayi shiru.
Zuwa can ya sake cewa, “Yes Sir!”. Daga haka ya cire wayar a kunensa yana murmurshi, yasan yau account ɗinsa sai yayi rawar girgiza kwankwaso saboda manyan kayan da zasu shigo cikinsa akan wannan albishir ɗin. Sakkowa yay a bishiyar ya koma cikin ƴan uwansa, koda abokinsa da bai san ainahin shi munafuki bane ya tambayesa daga ina yake sai ya nuna ya zagaya ne yin uzuri, dan haka babu wanda ya kula suka cigaba da hirar su......
_____________
A can ɓangaren wanda ya kira kuwa yana yanke kiran wata number ya lalubo ya danna mata kira shima. Ana ɗagawa ko gaisuwa bai tsaya yi ba ya fara magana kai tsaye.
“Congratulations Aboki, yau dai mun samu damar da muka daɗe muna fako tun a watan jiya, dan na samu tabbacin barin yaron nan jejin yanzun nan”.
Daga can aka furta, “Woow Zak-Shadow!, damar da aka daɗe ana jira kace ta samu. Lallai yau rana ce ta musamman a garemu, dan kuwa na tabbatar zamuja kaya iya kaya akan wannan albishir. Ba damuwa yanzu zan sanar da oga kuwa ai ba zancen wasa faka-faka kawai Aboki”.
Dariya yayi irin ta nasara shima, sai kuma ya ce, “Okay hakan yayi, amma abokina kadai tabbar babu matsala ko? Karfa mutanen nan su ci amanar mu. Bayan mun saida ƙasarmu sun sami biyan butarsu su zubar damu a banza batare da mun mori komai ba sai dukiya. Kasan fa halin ɗan Adam na wannan zamanin da wayo da iya cin amana, sannan mutanen nan a ankare suke komai nasu a tsare yake. Yaron nan yaron ƙasarmu ne na amana da kowa ke da hope a kan jarumtarsa, ba gidan soji da shugabanni kaɗai ba hatta al'ummar ƙasar nan ɗaukarsa suke kamar wani WALIYYIN SOJA”.
“Mtsoww!! Wato abokina wataran sai naji kana bani haushi. Wai miye damuwarka da batun wata ƙasa can, ƙasar data kasa gamsar da kai koda da albashin wahalar aikinka, su su minene ma kace duk basu suka so mu kasance a wannan hanyar ba, eh su suka so mana, tunda ai basai sunce muje mu aikata ba, sun gama tattare komai daga su sai ƴaƴansu da matansu dake ƙasashen waje. Muko an barmu da ɗumama kujera basir duk ya gama cinyemu”.
Dariya sosai wancan ya kwashe da ita, tare da faɗin, “Wlhy baka da dama, aiko bamace muna cikin masu ɗumama kujerar nan ba, dan mumafa tun farko karka manta munja kayan nan gwargwadon iko a gwamnati ta hanyar fakewa da ayyukan mu, kai dai a rufe rufau kawai. Ba lokaci faka-faka ka sanar dasu, kasan Yaron nan shegen kansa ne akwai wayo, komai a ankare yake yinsa”.
“Tabbas hakane. Ka bani 5minuts kawai, aikinka ya kammala a wannan gaɓar zakaji alert tare dana yaron shima”.
“Okay yayi, byeee!”. Ya faɗa yana ajiye wayar fuskarsa cike da murmushi, sai dai can ƙasan zuciyarsa wani kalar luguden daka take yi. Tabbas yasan wannan halayyar tasu mummunar halayya ce kuma abar ƙyama da duk wani ɗan ƙasa na gari bazai aikata ba koda a wanne addini yake kuwa. Sun rufe jinsu da ganinsu saboda dukiya, sun manta da basu da inda yafi ƙasar a wajensu, anan aka haifi kakaninsu, haka iyayensu, suma haka, sun kuma haifi ƴaƴansu. Amma sam basa tunanin makomar ƴaƴan nasu da ƴaƴan ƴaƴansu, su dai kawai su tara kuɗi a kirasu masu dukiya. (Lallai UBANGIJI mai rufin asiri ne, dan tabbas da wani zai san wanene ai nahin kai a take zai danneka ya maka yankan rago koda da wuƙar yankan albasar gidansa ce. Amma wata hikima ta ALLAH sai kaita warkajaminka cikin al'umma ana girmamaka batare da ansan girman na riga bane kawai. Anya waɗan nan sunma kansu adalci kuwa?, summa shugabanninsu adalci da a kullum talaka ke ƙalubalanta da gazawa batare daya san ba laifinsa bane shi kaɗai, dan da yawan tsiyatakun da irinsu da ba'a tunanin zasu iya dasu ake haɗa kai ayi ba shugabannin da kullum ake kallo da zargi kawai ba. Yanzu kamar dai shi da abokinsa, ba shugabannin komai bane na siyasa, kawai ma'aikata ne a ƙasa da suka samu dama ake kuma amfani da damar tasu ake dama ƙasar saboda suna son suma su dama da kuɗaɗe. Anya kuwa bai kamata ace su zauna suma kansu faɗa ba, su tuna zuri'arsu dake rayuwa a ƙasar, dan duk iya ƙoƙarin su na su su barta ai iyaka dai su kwashe iyalansu ba wai zuri'arsu gaba ɗaya ba ko🤔? Wani lokaci irin waɗan nan sai kaga kamar kansu ya toshe. Basa tuna dukiyar a duk ma yanda ka tara sai duniyar daka nema dan ita ta maka tsirara tikk sannan ta turaka cikin ƙasa ta rufe ruf ta barka da azabar girbar abinda ka shuka. Dan UBANGIJI baya zaluntar kowa sai bawan daya zalunci kansa......)
(Hummm kai dai ka sani zulwa, ni nayi nan🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️😏)
>•<>•<>•<>•<>•<>•<
A ɓangaren abokinsa shima dai yana yanke kiran ya isar da nasa saƙon ne inda ya dace. Dan kuwa a cikin harkar gaba da gabanta ne. Buƙatar ganinsa da ogan nasu ya bashi ya sakashi shiga canja kayan jikinsa. Sauri-sauri ya kammala ya fice dan yana buƙatar ficewa karma matarsa ta ganshi. Aiko bata ganshi ɗin ba sai tashin motarsa taji. Cikin takaici taja tsaki, dan ita tunanin ta da manufarta daban ce kamar dai yanda kukasan mu mafi akasarin mata muke, kullum zargin baya wuce namiji na yawon banza ko huɗɗa da matan banza a waje kai tsaye idan yana fitar dare, sai dai abinda bamu sani ba wasu mazan ba hakan bane, wasu ɓarnar tasu ma tafi ta neman matan, ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara tsare mana mazajenmu.
(😄👍🏼 Wannan jinjinar taku ce MAZANMU nagartattu, MAZAN ƘWARI kenan kuma MAZAN FAMA a wajenmu, ALLAH ya ƙara baku kariya da tarin ladar ƙoƙarin sauke hakkokinmu da kukeyi. ALLAH yasa mu da ku duk mu shiga aljanna. Ƴammata da zawarawa ALLAH ya baku mazaje na gari mazan fama a gidajen ku kuma. Kai a bama MAZA jinjina tare damu ma MATAN ƘWARAI RABIN ADDINI😘😘😀👍🏼❤️❤️💃)...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa) (VIp 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*