Kiɗa a Ruwa Page 3

sababbin Littafan Billyn Abdul

 *_Typing📲

      *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧

 *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 3

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt


IMZEEDVENTURE 

     Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.


Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?


Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? 


To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!


 Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.


IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.


Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.


https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.


Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*


Muna da account aTikTok@imzeed _venture.

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1


Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

_____________________


*_TELEGRAM GROUP_*


https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk



*_WHATSAPP CHANNEL_*


https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F


*_TIKTOK_*


https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/


*_INSTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


____________________



........Ɗagowa Imran dake zaune a study table yana duba wasu takardu yay yana kallonsa. Shi ko kallo ɗaya yay masa ya ɗauke kansa, zama yay a bakin gado ya jawo takalma daga ƙasan gadon, batare daya kalla Abbas dake cigaba da kallonsa ba har yanzu ya ce, “Zanje gida”.

        “Gida kuma? Lafiya dai ko?”.

   “Kawai zanje ne!”.

Ya faɗa a taƙaice.

Abbas yasan amsar ke nan, amma sai yay shiru yana kallonsa da nazari. Eh yasan in dai yace zai je gida akwai dalili, sannan sai ya tabbatar babu wani ƙalubale da zai bari mai girma a inda suken, amma haka kawai shi sai a yau sai yaji kamar tsoro ya tsarga masa akan tafiyar tasa, sai ya kasa cewa komai. 

        Dai-dai Zak-Shadow dake haɗa bindiga shima ya ɗan ɗago ya kalla Imran ɗin, ganin yanda ya zuba masa idanu sai ya sake tsuƙe fuska ya ɗauke kansa. Imran yayi murmushi, dan yasan ya tsani kallo. Cike da tsokana ya ce, “Anya ba kewar Madam bace ke tsikarin ka?”.

      Bai kula tsokanar da yake masa ba, kansa ya ɗan girgiza kawai yana zuwa gab da shi ya ciri ƙaramar takarda ya ɗauki pen yay gajeren rubutu. Batare da yayi magana ba kawai ya tura gabansa ya nufi barin wajen, sai kuma ya juyo yana kallonsa, cikin ɗage gira sama ya furta, “Ka rage sa ido Imran, idan nayi kewar laifi ne?”.

    Imran yayi dariya da faɗin, “A'a bakai laifi ba MAZAJEN FAMA, maza jeka ka ɗabbaƙa sunna abinka”.

       “ALLAH ya shiryeka”.

Cewar Zak-Shadow. Imran ya amsa da amin yana ɗaukar takardar ya fara dubawa.

        _“Bana son kowa yasan na fita, kamar yanda na faɗa maka 2 days ne, Kar abar ƙofar yamma a buɗe, dan haɗarinta yafi na sauran ƙofofi ka sani. Imran idonka ya zama sosai akan yaran nan da dukkan Captains ɗin kowanne sansani, sannan duk motsin da bai muku ba na sani, komai ƙanƙantarsa._

     Takardar Imran ya ajiye ya juya yana kallonsa da faɗin, “Babu damuwa in sha ALLAHU. Amma dan ALLAH ka biya ka sayo min kilishi da gyaɗa. Zan sa a kawo maka saƙo daga gida ka taho min da shi..”

      Wani kallo ya ɗago ya zuba masa, Imran daya san ma'anar kallon sai ya kwashe da dariya. “Maida wuƙar, ba ɗan aike zan maidaka ba ai ALLAH nace”.  

      A karo na farko Zak-Shadow ya ɗan saki wani murmushi gefen baki yana ɗauke kansa da ɗan girgizawa. Shima Imran ɗin murmushin sa ƙara faɗaɗa yayi. Yana matuƙar son aminin nasa, kamar yanda kowa yasan shima Zak-Shadow na sonsa matuƙar so ma kuwa. Dan shi mutum ne mai ra'ayin riƙau, idan baya yinka, baya yinka kawai. Idan ya soka kuma, to da gaske son naka yake. Mutum ne tsayyaye akan ra'ayi, kuma ɗan kai tsaye, baya iya kawaici akan duk abinda bazaiyi ba kuma baya buƙata. Idan har yace maka (eh) to ‘eh’ ɗin ce koda za'a kashesa, idan kuma yace (a'a) tofa ‘a'a’ ɗin ce. Zak-Shadow yasha baƙar wahala a lokacin da suke yaran soji saboda wannan taurin kan nasa a hannun manyansu. Dan a shekararsu ta biyu da fara aiki har zaman prison na sojoji yayi na wata shida saboda wata tirjiya da yayi akan umarnin wani ogansu. An azabtar da shi matuƙar azabtarwa a lokacin, dan bayan ya fito ma mutane da yawa sunyi zaton bazai sake rayuwa mai tsaho ba, amma da yake rayuwa ta UBANGIJI ce sai gashi ya miƙe, miƙewar data zama sanadin jajircewarsa a yanzu. Dan azabar da suka bashi sai ta zama kamar sun sake busar masa da zuciya ne ta yanda bai jin shakkar tunkarar kowane irin haɗari na rayuwa, daga nan kuma nasarorinsa suka fara bayyana har zuwa matakin da yake a yau.

         Shi Dodo ne a idon wanda bai san ainahin halinsa ba, saboda a kallon fuska kai tsaye zaka kirashi mugu ne. Baida fara'a, bai san wasa ba koda da aboki ne. Duk wanda kaga yace maka yaga yana dariya lallai ya kai ai masa barka. Yana magana idan yaso, idan kuma bai so ba zaku iya kwashe awanni tare koma sama da haka bakinsa bai furta komai ba na hira sai dai kaji yana karatun Alqur'ani. Dan kuwa yana da addini sosai, hakama ilimin addinin. Tabbas da ace bai zama soja ba sai dai a kirashi malami, a yana sojan ma yana koyar da sojoji ilimin addini, kuma yana musu majalisi, sannan yana cigaba da neman nashi ilimin shi kansa. 

      Sai dai sirrin da mutane basu sani a kansa ba sai shi amininsa da mahaifiyarsa shine haƙuri. Zak-Shadow mutum ne mai haƙuri kwarai da gaske. Sannan mutum ne mai adalci da son tsayawa akan gaskiya komai ɗacinta. Yana da tausayi matuƙa musamman akan mata da yara. Zai iya saida rayuwarsa akan su. Sannan yana da kishin addini da yankinsa. Dan shi kai tsaye ma zai ce maka yana fara jin kishin yankinsa ne kafin ƙasa gaba ɗaya....

        “Ka dinga tunani kamar wani mace”.

    Buɗaɗɗiyar muryarsa ta dawo da Imran daga doguwar tafiyar tunanin da yayi. Cikin ɗan sauke numfashi yace, “Ai tunaninka nake yi”.

       “Rashin aikin yi ne yay maka yawa da har zaka zauna tunani na halan?”.

    Cewar Zak-Shadow yana ficewa a tantin. Tashi Imran yay yabi bayansa. Kamar ɗazun yaran sojin suka shiga kamewa da sake nutsuwa waje guda. Yanzu kam sunfi ɗazun yawa. Da alama wasu dama suna a cikin tantunan ne shiyyasa. Inda yake zaman yin alwala ya nufa, hakan ya tabbatar musu lokacin la'asar yayi, ruwa aka kawo masa shi da Imran, suma suka shiga haramar yin tasu musulman ciki kenan. Wanda ba musulman ba kuma suka amshi duty ɗin zagaye wajan. Koda suka idar da sallar shi da Imran sansanin suka bari gaba ɗaya, sun jima kafin can su dawo suna hirarsu.


      Wajen wani ɗan bukkan kara dake gefe suka nufa, koda ya buɗe buhun da akayi labule a bukkar wasu irin garƙama-garƙaman karnuka ne marasa ƙyawun gani, sai dai kallo ɗaya kai musu dole ne hankalinka ya tashi, dan babu tantama waɗan nan idan suka kama mutum sai kufan jinin jikinsa amma ko ƙashi bazasu bari ba, dan marabarsu da zakuna ƙalilanne. Aiko suna ganinsa suka fara zallo da haushi kamar wanda suke gaishe shi.

    A mamaki na sai naga ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “Good Afternoon my Boys”.

       Wani haushin suka ƙara yi a tare kamar masu amsa masa. Imran yay dariya da faɗin, “Kama yaran nan naka training mai wahalar gaske. Idan suna wani abun sai ka rantse mutane ne”.

     Ƙaramin Murmushi Zak-Shadow yayi da ɗan taɓe baki. Idan yayi murmushi ƙyau yake masa, maybe shiyyasa baya son yi. Sun jima a wajen karnukan sannan suka fito, lokacin duhun magriba yayi. Yanzu kam sojoji ne sosai a camp ɗin, gaba ɗaya sun fito daga tantunansu, ashe a ɗazun wasu basa wajen shiyyasa, wasu kuma na barci, dan maimakon barcin dare su na rana sukeyi saboda tsaro. Tunda Imran da Zak-Shadow suka fito gaba ɗaya wajen yay tsitt kamar an musu tsawa, kowa ya nutsu. Kallo ya bisu da shi kaf ɗinsu, a ƙalla sun kai su ɗari, dan wasu basa a cikin sansanin a yanzu suna kan aiki a cikin jejin tako wace kusurwa. Wanda ke nan tare da shi bazasu wuce ɗari ba. Wucesu yay ya zauna kan dutsin da yake zaman yin alwala akoda yaushe, ai da sauri wani ya kawo masa ruwa dan in dai kaga ya zauna a wajen alwala zai yi. Daga nan kowa ne ya fara ƙoƙarin yin alwalar, sai wanda ba musulmai ba suka sake amsar dutyn zama garkuwa a yanzu ma kamar dai ɗazun. Sanin yau zai bar jejin kuma baya son su fahimta sai ya ce yanzu ma Imran ya jasu salla. Hakan baisa sun zargi wani abu ba suma, dan yana yin hakan a kowane lokaci, ba oga Imran ba har a cikinsu yaran masu addinin kan jasu salla, duk da dai duk wanda ke a ƙarƙashin Zak-Shadow duk iskancinka da sakacinka ga ibada wlhy sai ya saita maka haukan kanka. Dan in har kana cikin tawagarsa bakai ba wasa da salla, ba kai ba shaye-shaye koda na sigari ne kawai, bakai ba zama da jahilci dole ka cigaba da neman ilimin addini, shiyyasa ma ya saka musu ranakun karatu, bashi kuma kaɗai bane malamin harda wasu a cikin yaran masu ilimi na koyarwa suma, sai dai in ana kan matsannacin yaƙi ne. Hakan yasa Alhamdullah hatta wanda ba musulmai ba a cikinsu zaka gansu a nutse. Dan in ma kace zaka bijire kayi jikinka ne zai gaya maka a hannunsa..

     Bayan sunyi sallar magriba Imran yay musu nasiha kamar yanda suka saba, har zuwa lokacin isha'i. Bayan an idar kowa ya miƙe suka kasu group-group dan kowa da abokansa da kuma abokan maganarsa suka kunna wuta suna hira, wasu na cin abinci. A lokacin ne Zak-Shadow ya sulale ya bar jejin, barin da da yasan sakamakon da zai so da shi da bazai yi ba. Dan kuwa tabbas wannan barin shine mafarin wata babbar ƙaddara da alkalami ya jima da rubutata a cikin rayuwarsa tun yana cikin Ummiensa.........✍🏼


   *_Wace ƙaddara ce wannan? Mizai faru? Mike shirin faruwa ne da Zak-Shadow 😭. Ya labarin mace mai ciki kuma? Wace rawa zata taka mana a wannan labarin?. Amsar ku na cikin labarin KIƊA A RUWA MAI MAGANIN DODO. Kada ku bari a baku labari. Dan ni kaina Bilyn ku labarin nan tsumani yake yi💃💃💃._*



_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._


*_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa)_*

*_+227 98 94 12 81_*

      *_My NITA_*


        _Shaidar biya👇_


*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*



*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*


*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*


*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*



*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*



*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

 @BilynAbdull


*_WHATSAPP (500)_*


*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*



*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*



*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*



*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*


*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment

Previous Post Next Post