Kiɗa a Ruwa chapter 1 free page

Billyn Abdul ce

Typing📲

      🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧

 Bilyn Abdull ce 🤙🏻

_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

Chapter 1

        Free pages

________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt

IMZEEDVENTURE 

     Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.


Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?


Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? 


To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!


 Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.


Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃


__________________

TELEGRAM GROUP

WHATSAPP CHANNEL

TIKTOK

INSTAGRAM

_________________

        A tsari da tarihin rayuwa ƘADDARA MADUBI ce. Domin tana sakaka kallon kanka a ɗan adam kuma bawan da rayuwarsa ba ikonsa bace. UBANGIJI ya halicci duniya da halittun dake rayuwa a cikinta daban-daban, wanda suke a zahiri, da wanda ya baiwa kansa ilimin sani shi kaɗai. Sai dai a dukkan halittunsa ya tabbatar mana ƊAN ADAM mai daraja ne. Musamman idan mukai dubi da ayoyi da suka zo cikin Alkur'ani mai girma.

        Bawai hakan na nufin sauran halittunsa basu da muhimmanci ba, a'a kai dai DAN ADAM ya baka wannan darajar, ya kuma fifitaka, idan muka duba Suratul Baqarah. Yayin da ALLAH ya ce wa mala’iku zai halicci khalifa a ƙasa (wato Adam), kuma ya umurci su su yi masa sujada, abin da ya nuna fifikon mutum fiye da mala’iku (sujuda ta girmamawa ba ta ibada ba). Bai barmu a mutanen kawai ba, sai ya rabamu a jinsi guda biyu, NAMIJI da MACE. sannan ya yomu a BAƘIN FATA da FARAREN fata. Ya yomu a YANKUNA DABAN-DABAN. Ya kuma banbantamu a ADDINAI DABAN-DABAN. Ba iya nan kawai muke ba, yarukan bakunan mu ma daban-daban suke, ta yanda wani idan zai kwana magana wani bai san mi yake faɗi ba koda zaginsa yake kuwa. Ba'a nan kawai muka banbanta ba, yama wasu ARZIƘI, wasu DUKIYA, wasu ILIMI, wasu BAIWAR SARRAFA HARSHE ko yin AIKI tuƙuru daga gaɓɓansu da ƙarfin daya azurtasu da shi. Samun ɗaya daga cikin wannan bashi ke nuna maka kafi wane DARAJA ba. Dan zai iya yinka mai ARZIƘI a DUNIYA, ka tashi talaka a lahira, talauci irin na rasa ƙyawawan ayyuka da rashin samun ƙyaƙyƙyawar MAKOMA. Zai iya yinka TALAKA a DUNIYA a lahira ka tashi mai tarin arziƙi da AYYUKANKA da samun kyakkyawar makoma. Zai iya yinka mai ILIMI, a lahira ka tashi ILIMIN bai amfaneka da komai ba domin baka amfanar da kanka da shi ba bisa kyakkyawar hanyar data dace da iklasi a DUNIYA. Zai iya yinka JAHILI, amma ka tashi a ƙyaƙyƙyawar MAKOMA saboda baka cutar da kowa ba a duniya, baka kuma bi mummunar hanyar da zata RUGUZAKA ba wajen yin ayyuka saboda RIYA (Rahama ta ALLAH ce). Wannan kaɗan ne daga cikin RAHAMARSA ga bayinsa.

      A yanda DUNIYA take kamar ƙwallon wasa a ido, haka RAYUWAR kowane ƊAN ADAM take a NASARA ko FAƊUWA. Yanda kwallon ke a hannunka kusa da idanunka babba, haka girman matsalolinka da damuwarka da nasararka suke a zahirin idanunka da ZUCIYARKA. Idan ka harbata nesa da kai takan koma ƙarama, haka idan ka yarda UBANGIJI shine mai ƙaddarawa da bada sakamako sai ka dinga kallon wannan damuwar taka da matsaloli da jarabawoyi ƘARAMA kamar yanda kwallon nan dake nesa da kai take ƙarama.

     Banbancin kawai girma da ƙarantar kwallo a idanu muke ganinta ƙwaƙwalwa ta auna mana. Amma girman jarabawa da matsalolin rayuwa muna kallonsu ne a ZUKATANMU da KWAKWALWAR MU baki ɗaya.

      Bara mu taƙaita domin ku fahimci inda ainahin shimfiɗar tamu ta dosa kai tsaye, dan karmu shagala lokaci na gudu ba kuma mu yake jira ba. Abinda kawai nake so mai karatu ya auna anan minene ainahin RAYUWA? WANENE SHI? MAI ZAI KOMA A WATARANA? MINENE ƘARSHENSA A ƘARSHEN RAYUWA?.

     Ki yarda, ka yarda a cikin kowace RAYUWA akwai farin ciki, akwai jarabawa, akwai nasara, akwai faɗuwa, akwai ƙalubale, akwai mafari, akwai ƙarshe, akwai mina aikata mina bari a bayana?. Dukansu kuma suna ƙunshe ne a cikin wannan rayuwar taki ko taka guda ɗaya tak da ba'a hannunka take ba, yanda ba'ai shawara da kai yayin halittarka ba, sai da ka girma ma kasan wanene kai? Haka baza'ai shawara da kai wajen tabbatuwar waɗan can abubuwan na sama ba. Domin a dukkan ni'ima da rahamar da UBANGIJI ya baka babu wacce kake biyansa da KUƊI. Ibada ma idan kayi kai kakema kanka gata bazaka rageshi da komai ba, ba kuma zaka ƙareshi da komai ba. Dan haka mu tafi kai tsaye kawai a wannan labari mai suna KIƊA A RUWA! MAI MAGANIN DODO. da zaizo gareku a wannan lokacin, mu kuma hango darasin da yake mana hannunka mai sanda akai domin mu fahimta, mu ilimantu, mu nishaɗantu, mukuma wa'azantu idan hakan ta kama......

•>•>•>•>•>•>•

.....17/5/20013.....

      ......Motse-motse yake ɗan yi da surutai cikin barci, har takai wanda ke a kusa da shi yana iya jin komai. Gashi yayi sharkaf da zufa a goshinsa duk da ba yanayi ne na zafi ba. Hasalima wani ɗan karan sanyi ake zuwabawa irin mai hazo ɗin nan da iska mai kwaso ƙasa ta buɗe mutane. 

     Da mamaki wanda ke kusa da shi da littafi a hannunsa yana dubawa ya ɗan zuba masa ido, sai kuma ya kai hannu ya taɓa shi yana kiran sunansa amma ko motsi. Littafin hannun nashi ya ajiye, zuciyarsa na ƙara shiga ruɗani da tsoro. Ba wannan ne karo na farko da abokin nashi kuma amini ke shiga cikin wannan halin ba a cikin barci, wani lokacin har sai ka fara fassara al'amarin nashi kamar na mai aljanu, kuma sam ba aljanun bane ba, in dai har zai kwanta barci mai nauyi a ƴan shekarun nan da wahala ya tashi bai shiga wannan yanayin na mafarki ba, duk da bai taɓa faɗa masa irin mafarkin da yake yi ɗin ba shi ya fahimci mafarkine mai nauyi da ban tsoro....

       Sosai ya girgizashi kam yanzu, bayan ya janye bargon da yake ciki kalar army green, tare da shafa masa ruwan gorar dake gefensa a fuska. Wani nannauyan numfashi ya kawo tamakar mai dawowa daga suma, sai kuma ya ɗan furzar ya sake jan wani kaɗan kafin ya buɗe idanunsa a hankali.

      Masha ALLAH na ambata ganin wasu kyawawan idanu tamkar ba na namiji ba. Da farko abokin nashi da shima ke kallonsa ya zubama ido, sai kuma ya kauda gefe yana yunƙurawa ya tashi zaune yana jingina da jikin tantin da suke ciki. Riga ce armless data kama ginannen jikinsa kalar army green, sai wando 3-quater irin kakin sojoji. Duk da a zaune yake kallo ɗaya zai tabbatar maka da sojan ne na gaskiya kuma tsayayye, dan kuwa jikinsa irin na lafiyayyun tsayayyun jaruman sojoji ne da zasu iya tunkarar kowane harmutsi musamman na nuna ƙarfin ƙwanji.

      Abokinsa da ya zuba masa ido ya ɗan girgiza kansa, sai kuma cike da kulawa ya ce, “Da ace ina da damar matse bakin nan naka da baya son motsawa yayi magana da nayi hakan dan sanin wane irin mafarki kakeyi a shekarun nan, dake saka ka a wannan yanayin, *_Zak-Shadow_* duba fa yanda kake zufa tamkar wanda yake a filin daga, amma kuma akan mafarki, wannan al'amari na bani mamaki da tsoro”.

       Wani ɗan kallon fishaa yay masa slowly da idanunsa ya kuma janye, batare da yayi maganar da yake so yayi ɗin ba ya miƙe abinsa. Nace oh oh! Wato fa da gaske a sojojin ma akwai SOJA, akwai kuma SOJI. Kai daka kalla wannan kasan yaci sunansa na Zak-Shadow, har hamar ya dace a ƙara masa da ILIYA ƊAN MAI KARFI. Dan kuwa mazan faman ne fa a mazansu da kayar da su ƙasa sai an haɗa da babban shirin haɗin gwiwa. Cikin yanayinsa na rashin gaggawa da hayaniya ya saka tausasan slippers baƙaƙe dake a gaban gadon daya tashi, batare daya sake kallon abokin nashi da yay tagumi yana binsa da idanu ba ya nufi ƙofar tantin da suke ciki, sai da ya ɗan ranƙwafa sannan ya fice. 

    Babbar magana, jeji ne iya jeji da babu alamar wani gari ko motsin halittu na mutane a kusa. Idan ka cire ɗan sansanin da suka kafa nasu na sojojin mai Tanti biyar kacal. Uku manya ne sosai da zai iya cin sojoji da yawa. Guda biyun sune ƙananu madaidaita. Guda ukun manya da ɗanyan ƙaramin suna a kusa da juna ne, ɗayan da Zak-Shadow ya fito a ciki yana gefe guda ne a ware ƙarƙashin wata ƙyaƙyƙyawar bishiya ƙatuwar gaske. Sosai garin yayi hazo na yanayin sanyi har baka iya hango abinda ke ɗan nesa da kai da ƙyau koda bishiyoyi ne, a gurin yashine shimfiɗe mai ƙyau da ɗaukar idanun mai kallo, ga tsafta, dan gabansu kaɗan akwai ruwa kwance dake rayuwa a wajen, dan haka ya zama matattara dabbobin jeji dake zuwa shan ruwa, wani lokaci kuma harda masu haɗari amma suka zo suka kafa sansani a wajen saboda ƙarfin hali irin na soja.

      (Sojojinmu ALLAH ya ƙara muku lafiya da nisan kwana a duk inda kuke🙏). 

     Babu yawan sojoji a waje, dan basufi a ƙirga ba dake ɗan kai-kawo da bindigu a hannu sai wasu a zaune, da alama ƴan jiran kota kwana ne.

        Fitowar Zak-Shadow ya saka wanda ke jikin tantin daya fito nutsuwa da sauri, tare da ƙamewa yayi salute nashi cike da girmamawa yana sake risinar da kai ƙasa, dan da gaske Zak-Shadow zakine a wajen na sama da shi ma ba naƙasan kawai ba. Idanunsa kyawawa masha ALLAH ya zubama sojan na sakanni, sai kuma ya maida ga sauran da ƙamshinsa ya fargar da su, suma duk sun nutsu, wasu a cikinsu jikinsu har tsuma yake yi. Jin shakkar Zak-Shadow a jinin duk wani matashin soji daya sanshi yake, badan ya kasance azzalumi ba, sai dan kasancewarsa tsayayyen mutum da baya ɗaukar shirme akan aikinsa da gaskiyarsa, kana take doka ko gaskiya ya ɓallaka ya ɗora gaɓa-gaɓa wannan abu ne mai sauƙi a wajensa. 

     Sai da ya gama ƙare musu kallo tsaff batare da yace uffan ba yay wucewarsa cikin takun bajinta na ma'abota ƙarfin jiki. Numfashi suka shiga saki a hankali, dan tunda ya fito kowa ya riƙe nashi a maƙoshi gudun shiga tarko. Sai kuma suka shiga ɗan kallon juna suna gulma da idanu, dan buɗe baki dai ayi magana tamkar taro match ɗin da babu yawan ƴan wasa ne..........✍🏼


     _(🤣To bana kuma wa muka kwaso ne? Nima fa masu karatun wannan Zak-Shadow ya fara razana ni🤭, kota yaya labarin ma zai rubutu oho🥱😆. Kudai kuyi addu'a kawai kar ku ji ana karya Bilyn ku gaɓa-gaɓa ana ɗorani🤥.)_


   

________________👇


_Zaku samu wannan Littafi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._


*_NIGER🇳🇪- (500 CFA)_(VIP 1000 CFA)*

*_+227 98 94 12 81_*

      *_My NITA_*


        _Shaidar biya👇_


*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*



*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*


*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*


*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*



*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*



*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

 @BilynAbdull


*_WHATSAPP (500)_*


*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*



*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*


*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment

Previous Post Next Post