Gasar Diamond League ta bana, wacce aka fara a ranar 6 ga Afrilun Shekarar 2025, tare da kungiyoyi 11, da jimillar wasanni 110, ta zo ƙarshe tare da samun zakaru.
Kungiyar Wonder Glory International Football Academy (WOGIFA) daga Agwa dake No.1 First Royal International school Rd Agwa-Kaduna, ƙarƙashin jagorancin kocinsu Godwin Ereh, ta fito a matsayin zakaru bayan taka rawar gani a gasar.
‘Yan wasan WOGIFA sun nuna bajinta tun daga zagayen farko inda suka buga wasanni goma ba tare da rasa wasa ko ɗaya ba, abin da ya sa suka zama taurarin gasar tun daga farko har ƙarshe.
A ranar 21 ga Satumban shekarar 2025 ne za a kammala gasar a hukumance, tare da karrama WOGIFA a matsayin zakarun Diamond League na shekarar 2025.
Tags
Sports Hausa