Alh Nura Gwaska ya ba Makarantun Islamiyya gudunmawar ₦900, 000

2027 Elections

Biyo bayan irin gagarumar gudummawa da Gidauniyar Alhaji Isma'il Nura Gwaska ke badawa wajen Cigaban ilimi dama cigaban marayu da marasa karfi a karamar hukumar Igabi dake Jihar Kaduna yana haifar da ɗa Mai ido duba da irin halin da ake ciki yanzu.

Shugaban Gidauniyar, Alh. Nura Ismail Gwaska kuma ɗan takarar kujerar Malisar tarayya na Igabi, ya halarci Muhadarar Bude Masallacin Ansarur-rahman dake Daura Road, Hayin Danmani Rigasa Kaduna.

A jawabinsa, yayiwa babban bako na musamman Sheikh Muhammad Bn Uthman fatan Allah yamaidashi gida lfy, Kuma yajin jinawa sarkin Hayin Danmani Alh. Abba Abdullahi bisa kokari dayake wurin cigaban Unguwar Danmani ta kowacce siga.

Ya ƙara da cewa, "Duk abinda aka ce na cigaban al'umma ne to in sha Allah za'a same mu a kan gaba"

"Duk abinda aka harka ce da addini in sha Allah idan aka ƙwanƙwasa kofa da yardar Allah zamuyi don haka ba tare da ɓata lokaci ba tunda wannan masallaci na neman gudunmawa na maida ta Masallacin Juma'a Mun bada namu gudunmawar na ₦500, 000"

Haka zalika Alh Nura Gwaska ya ziyaarci Makarantar Anas Bn Malik Da Makarantar Markaz Darus-Salam in a nan ma ya ba ko wacce makaranta gudunmawar #200, 000 tare da ba Ɗalibai masu hazaƙa kyaututtuka.

Alhaji Nura Isma'il Gwaska ya kasance mutum ne mai kishin addini, tausayi da kyautata ma marayu da marasa ƙarfi.

Post a Comment

Previous Post Next Post