Randar Cikin Ɗaka Page 5-6 Complete by Ummu Affan

Randar Cikin Ɗaka - Abokiyar Hira Novels

RANDAR CIKIN ƊAKA...

©UMMU AFFAN

Page 5-6

"Idan kina cin ƙasa, ki kiyayi ta shuri! Wannan wanne irin wulaƙancin ne? Ban zo da Nihlah gidan nan domin ki wulaƙanta ta ba!"

 Maganar Yaya a fusace, har haɗa gumi ya ke. Wani duba Aunty Farrah naga ta jefa ma shi, irin na rainin wayon nan sai ka ce ba mijinta ba. Kafin cikin fushi ta ce,

   "Eh lallai na yarda an jiƙa an baka ka sha, daman dangin maita mene ne baza su iya ba!"

  Kuɗi ya ciro aljihunsa za su kai dubu da ɗari biyar.

  "Ba tashin hankali nazo yi da ke ba, ga kuɗin cefane nan a lallaɓa."

A yatsine ta dubi kuɗin, har ya juyo ta wani saurin cewa.

  "Muna cikin zamanmu na jin daɗi da rufin asiri tazo ta rusa komi, taya zaka ce kar na tsani wannan baƙar annobar, wai kuɗin cefane wannan ka ke ba ni. To a cikin gidan nan me zasu mana? Wallahi tunda kika rusa mini farin ciki, kema sai na rusa duk wani tanajinki sai kin yi dana sanin shugowa gonar Farrah."

Bai tanka mata ba, nima ganin ya doshi ƙofa, ban san lokacin da na fito ba har ina cin tuntuɓe.

Fita da mashin ɗin ya yi muka doshi hanyar gida, ina ta tunanin ashe nan gidan yanzu Yaya ya kamawa Aunty Farrah haya, tunda aurenmu da kwana shidda gidansa ya ƙone, ba su tsira da komi ba sai lafiyarsu domin cikinsu babu wanda ko ƙwarzane ya samu. A daidai ƙofar gidanmu ya ajiye ni tare da miƙo mini gudar ɗari biyu.

  "Ga wannan ki hau babur ki goma zuwa jimawa idan kin gama shan nonan!"

 Da sauri na dube shi, sai kuma nayi saurin ƙasa da kaina.

  "Yaya idan ka dawo kasuwa ba za kazo ka ɗauke ni ba?"

 "Ba ni da lokacin yin hakan!"

Ya ba ni amsa tare da figar mashin ɗin sa ya bar gurin. Ina tsaye har ya ɓacewa gani na, kafin na buɗe jakata na saka kuɗin jiki a sanyaye na doshi ƙofar gate ɗinmu ina ƙara jujjaya kalaman Aunty Farrah a zuciyata, tun da ba ma shiri da ita domin nasan ta tsane ni sosai har faɗa mini ta taɓa yi, ina kuma da yanzu na aure mata miji!

 Har na doshi hanyar ɓangarenmu sai kuma nayi tunanin bari na fara gaishe da su Amma surukaina da kuma Kakata Hajja. Muryata a sanyaye nayi sallama a babban parlourn bayan na shiga.

"Me ya kawo ki gidan nan?"

Ko amsa sallamata ba su yi ba, Hajja ta jeho mini tambayar a tsawa ce.

 Da sauri na zube jikina har ya fara ƙyarma sakamakon tun ina ƙaramar yarinya nake mugun tsoran Hajja, saboda sam ba ta mini da wasa ba ƙaramar tsanata tayi ba. Gaishe su nake ƙoƙarin yi Inna tayi saurin dakatar da ni.

   "Algunguma a fuska Musa a zuciya Fir'auna, ko kin yi halin naki ne? Domin wallahi na jinjinawa Mudassiru da ya kusa wata biyar da ke a cikin gida."

  Duk da a gurina wannan abin da suke ba sabon abu ba ne, ba sabo kawai nayi da hakan ba zan iya kiransa ya zama jini na, amma hakan bai gaza zubowar hawayena ba, da suna ƙarewa ruwan hawayena ya isa ace ya ƙare, amma a kullum ƙara yawaita suke, cikina har ya fara ƙogi nasan haka bai rasa nasaba da rashin karyawata saboda ɗokin zuwa gidan da tamkar ana zuba mini ruwan zafi.

   "Ba shi ne ya turo ni ba, nazo na gaida ku ne."

  "An ce miki muna nemanki ne? To matsa ki kwashi tsumman jikinki ki fitar mana jikar mayu, ni wallahi ban san me Musa ya gani da auren Banufiya ba dangin mayu kawai."

 Hajja ce mai maganar ranta a ɓace ko kallona batayi tsabar ƙiyayya, tunda muke da ita ba mu taɓa haɗa ido ba don ta ce manyan idanuwan da nake da su duk na maita ne.

  Jiki a sanyaye na miƙe, ganin Amma ba ta parlour (Mahaifiyar Yaya Md) na doshi ƙofarta, Inna ce ta daka mini tsawar na fice, a gigice na bar parlourn.

  Hanyar sassanmu na nufa ina share guntun hawayena, Baba da Umma ne zaune a madaidaicin tsakar gidan, gurinsu na nufa tare da zubewa ina gaishe su, babu wanda ya amsa mini a ciki sai Umma da ta ce,

   "Taron na ayya, gayyar tsiya. Ai daman Amal ta sanar da ni wai kun fito da Mudassiru zai kawo ki gida, ke ga 'yar daɗi miji. To yanzu ba wani lokaci ba ki tashi ki koma kafin jikinki ya yi tsami, bar ganin an kai ki gidan miji, wallahi wannan bazan hana na lakaɗa miki na jaki ba."

Da sauri na miƙe domin ni sai dai na ba da labarin wacece Umma ba dai a ba ni ba. 

Ina tafiya ina waiwayen ɗakin mahaifiyata Mama, wai gani nazo har cikin gida amma ba ni da ikon ganin mahaifiyata, a bakin gate ɗin gidanmu na zauna naci kukana kamar me. Kasancewar gidan babban gida ne kuma na masu kuɗi, sai dai ɓangaren iyayen Yaya shi ne yafi ko ina ƙyau a gidan, kasancewar gidan mahaifinsu ne kuma yana da rufin asiri, sai ya mawa iyayena BQ na gidan a ciki duk aka haife mu.

  Ganin zaman ba zai kaini ga komi ba sai na miƙe na gangara bakin titi domin in sami abin hawa, ina tsaye gurin naga mota ta faka a gabana, sosai ƙirjina ya buga, ƙara matsawa nayi motar ta kuma tsayawa kusa da ni. Zuba ido nayi domin ganin wanne mai kwarmin idon ne ke neman tare ni.

  "Hajiya Nihlah daman talaka na ganinku?"

Mamallakin motar yana fitowa ya furta hakan.

   "Adyaan!"

 Na furta da sauri, maganauna sun kasa sauka daga fuskarsa, yana murmushin sa da fararen haƙoransa suka bayyana ya ce,

   "Nihlatulkhair!"

Da sauri nayi ƙasa da kaina ina wasa da ɗan yatsana, ya sake furta.

   "Halan daga gida ki ke?"

   "Eh naje gida ne, yanzu zan koma gidana."

  "Allah sarki to ki shugo na rage miki hanya."

Da sauri na fara girgiza kaina.

  "A'a na gode Adyaan Allah ya bar zuminci."

 Zan fara tafiya ya yi saurin tara ta da maganarsa.

  "Nifa ɗan'uwanki ne, kar ki manta yadda muke da Yayanki Muzammil!"

   "Na sani, amma ka bari na gode."

   "To baki isa ba, sai na kai ki."

  Ina ta gaddama shima yana yi, ganin shine babba sai na bar mi shi, kawai na shiga.

Ba wanda yayi magana har muka ƙara so ƙofar gidan, ɗaga kaina nayi na kalle shi.

   "Daman kasan inda nake ashe?"

   "Haba dai Nihlah ai dole nasan inda kike, ko kin manta wane ne ni a gare ki."

  Da sauri na fara kiciniyar buɗe murfin motar. "Na gode." Na furta har na zura ƙafa ɗaya ya ce, "Ɗan dakata!"

 Juyowa nayi na dube shi, wayarsa ya miƙo mini.

  "Saka mini lambar wayarki."

  "Akan wanne dalilin, ko ka manta ni matar aure ce yanzu?"

  "Duka amsoshin zan baki?" Ya tambaya fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi, ganin ba ni da niyyar amsa mi shi ya ce,

  "Ta farko akan dalilin ki na 'yar'uwa a gare ni, na biyun kuwa ƙarshen sani ma ai tare da ni aka shafa fatiha."

  Amsar wayar nayi zuciyata na ɗillin-ɗillin na saka mishi, zan fita ya ƙara tsayar da ni, kuɗi ya ba ni ɗari biyar-biyar ina jin in ba su kai dubu goma ba sun kusa. Ƙin amsa nayi sosai ya matsa mini har sai da na amsa, godiya na mi shi tare da ficewa, jikina ya ba ni har na shiga ƙofarmu kallona yake.


Adyaan pov.

Tana shiga gidan ya sauke a jiyar zuciya tare da dafa saitin zuciyar sa, nan take idanuwansa suka kaɗa jawul, tunowa da yayi da zazzafar soyayyar da suka ƙulla shi da Nihlah.

  "Adyaan ina ji maka tsoran ka rasa Nihlah domin soyayya mai zafi irin wannan bata cika cimma gaci ba har ayi aure."

  Kalaman abokinsa kuma Yaya a gurin Nihlah Muzammil ya tuna, a lokacin har faɗa sai da suka yi saboda wannan maganar da ya faɗa yayi sati kuwa yana zuwa gurin shi amma baya kula shi sai daga baya. Numfashi ya sauke tare da tada motar ya tafi gida zuciyarsa na zafi, ganinta ya ƙara fama mishi mikin da baya tunanin warkewarshi har abada.

 Gida ne wanda ba sai an faɗa ba kasan na masu da shi ne, ya doka hurn. Mai gadin na leƙowa yaga ɗan lelen Hajiya ne yayi saurin wangale ni shi faffaɗan gate ɗin. Sai sannu da zuwa yake mi shi, amma hannu kawai ya iya ɗaga mi shi ya gangara ciki, shi kan shi mai gadin a ransa ya aiyana yau ɗan lelen Hajiya ba lafiya, kasancewar duka ma'aikatan gidan sun san halin Adyaan na son mutane da fara'a duk da tarin dukiyar iyayensa da tashi kowa na shi ne talaka da mai kuɗi yana girmama kowa.

  A sanyaye ya fito daga motar ya doshi hanyar cikin babban parlourn gidan, Hajiya zaune ita ɗaya cikin shigar alfarma, shugowarshi ta faɗaɗa fara'arta.

   "Oyoyo mutanen wancen gari."

Dole shima ya ƙirƙiri dariyar tilas tare da zaunawa daidai ƙafafuwan Hajiyar yana gaisheta.

  Amsawa tayi cike da kewar tilon ɗan nata kafin ta ce,

  "Da wata a ƙasa, anyi yamma da kare. Adyaan me ke damunka, domin idan kana farinciki na sani haka ma akasin hakan."

  Bai da munafurci mahaifiyarsa tamkar aminiyarsa haka take a gurin shi, komi nashi ta sani kamar yadda bata ɓoye mishi komi, hakan ya samo asali daga shaƙuwar da ke tsakanin. Kuma ta rasa iyayenta duka, haka Adyaan na da shekaru goma mahaifinsa ya rasu, hakan yasa komi ta samu ɗanta na farin ciki ko baƙin ciki Shi kaɗai ta haifa hakan ya sa bata iya ɓoye mishi komi shi ne danginta gabaɗaya.

   "Hajiya yau na haɗu da Nihlah, har na rage mata hanya."

  Zuba mishi ido tayi ganin yadda ake maganar ina hawaye kuma yana dariya, tsabar tsantsar damuwar da ya shiga da ganinta. Ajiyar zuciya ta saki ta ce,

  "Adyaan daman har yanzu ba ka cire ta a ranka ba? Amma alƙawari ka mini ka daina tunaninta?"

  Murmushi ya yi, "Eh tabbas anyi haka, Hajiya ai ba tunaninta nayi ba a zahiri ne muka haɗu, ni ne ma na sauke ta har gidanta."

  "Baka tsoran mijinta ya ganka?"

   "Ai Yayan abokina ne, ba zai kawo komi ba, shima nasan ya manta da baya abotarmu da ƙaninsa kawai zai kalla."

  Hajiya ta ƙurawa Adyaan ido hankalinta a tashe, hatta tafiyar nan da yayi ta sa shi saboda ya rage tunanin Nihlah, sai ga shi yana dawowa garin da ita ya fara ci karo, da ƙyar ta saka shi ya yi wanka sannan yazo suka ci abinci, sai nasiha take sake mi shi gami da muhimman cin haƙuri da yarda da ƙaddara mai ƙyau ce ko akasin hakan.


Nihlah pov.

Jingina nayi da garo (Bango) a zauren wani irin kuka da ban yi tunanin zuwan shi a yanzu ba ya kubce mini. A hankali na gangare ƙasa ina ci ga ba da kukan.

' _Adyaan sun raba mu, Umma tayi sanadiyya tarwatsa zuciyoyinmu, tayi fata-fata da muradanmu_' Na furta a cikin zuciyata. Kafin na miƙe ina furta astagafurullah, tunowa da nayi ni matar wani ce.

  Ina shiga parlourn muka haɗa idanuwa da Amal ta miƙe tana doka dariya tamkar mahaukaciya sabuwar kamu......

08104335144

Masu buƙatar littafin za suyi magana ta lambar da ke sama ko a tura kuɗi kai tsaye 500 ta 8104335144 Opay wallet Fatima Rabiu Sunusi sai a tura shaidar  biya ta 08104335144 na gode.

#Nihlatulkhair

#YahMd

#YahMz

#Adyaan

#Amal

#Farrah

#UmmuAffan

#RandarCikinƊakaa

Post a Comment

Previous Post Next Post